Haka dai, mu yi mu'amalarmu mafi kyawu, tare da taimakonta. Domin ita ce tushen abun, saboda kulawarta ga soyayyarmu. Mu gujewa duk wani damuwa.
A zo wani lokaci, na kan kira number nata,amma ba a dauka, sai mun hadu a WhatsApp,na tabbayeta meyasa (dayake ni gani nake kamar taki dauka ne), ta ce wlhy ba komai, lokacin wayar baya hannunta ne kuma ta zo ta gani ba credit a layinta. Nan dai na aminta,to wanan abun dai ya ci gaba.Tun ina uzuri na zo na kasa.Kuma maganar kenan cewa:Ba ta nan ne,ta zo ta gani bata da credit.To kuma gashi har rantse min take,hakan ya sa dai na rasa me dalili.Anan sai na fara tunanin ko dai yanzu ta samu wani ne,wanda ya fini.Shiyasa bata daukar kirana.In na tuna da cewa kuma in mu hadu a WhatsApp muna soyayyarmu ba chanji,sai wanan tunanin ya kau min.Wani lokaci na ce,ko dai Ummah ce ta hanata.Nan ma dai in na tuna cewa,bata boye min abu,sai wanna tunanin ya kau.Haka dai sai na ji cewa,tunda Khaleesat zai yi wuya ta dada shekara daya bata yi aureba,kuma ni zan kai shekara akalla uku,to ya kamata nasan wana mataki zan dauka.Anan sai mu zauna da wani abokina.Na dauki cewa na sama kaina a raina zan iya samunta,kuma zan iya rasata.Hakan shi ne zan samu saukin kewa ko da a ce ta yi aure ta barni.To haka ayi na hakura,na barma Allah lamarin.To dama ina da matsalar in na kirata ban cika samuntaba.Sai nan na yanke cewa mu dinga chatt kawai,haka dai na daina kiranta sai dai mu yi chat,to amma hakan duk bai kawo wani chanji ta bangaren soyayyarmu ba.
To wani lokaci,na zo naga na daina ganinta online,to ban san meyasaba.Kuma gashi na riga da na sanya cewa ba zan kara kiran number nataba,lokacin an kai wata biyu,ba ta hawa WhatsApp,har wata rana na gwada kiran number nata sai naji a kashe.To bayan haka dai sai wata rana ina online WhatsApp naga sallama nata.
Mu fara chatt,anan sai na ce,yau kam ya kamata na daure na matsa mata don jin me dalilin da yasa bata daukar kirana,domin ni ban yarda ba komaiba.Anan sai na dauko maganar na ke cewa:Watannin baya,akwai wani yanayi da mu shiga da baki daukar kirana,kuma na yi-na yi kinqi fadamin ko meyasa,ko laifi na miki.Anna sai take cewa:"Wlhy ba laifin da ka min,in da ka min laifi wlhy ka fi karfe na boyema,zan fito na fadama".To anan sai na ce to meyasa,nan sai ta ce ba komai.Anan sai nake cewa:Ni in ma misali yanzu kin ce baki yi da ni,wlhy ki fadamin zan dauki wanan jarabawar,domin dama duniyar kanta ma juyi-juyi take.Nan dai ta gani bata min reply ba,anan sai na fahimci kamar maganar ya mata ciwo ne.
Anan tun da mu yi haka,wlhy duk wanan rashin daukar kiran dake damuna ya wuce,azo itama take kirana.Kamar yanda muke soyayyarmu a farko.Azo ba samu damuwa.To anan dai na sha gwadata don fahimtar son da take min,na fahimci tana so na sosai har yanzu.
Na zo,na tafi school,na kirata nake ce mata zan tafi school,take cewa Allah sarki,sai take cewa Allah ya taimaka,take cewa:"Zan baka amana,wallahi kuma ban da kallon yayan mutane".Sai na yi dariya na ce,da ban yiba sai yanzu,ina dake wa zan tsaya kuma kallo.Ta yi dariya ta ce,uhmm wasa nake ma na yarda dakai My.Haka dai ina school,ina kiranta in na samu dama.Muna gaisawa,wani lokaci mu yi hira sosai.Wata rana na kirata,muna hira sai take cewa:"Na ji labari wai zaka yi aure".Na ce mene, aure?,uhmm ni wanan labarin ne ma na ji a kanki,wai zaki yi aure nan kusa,sai ranta take ya baci,wanda tun da nake da ita ban taba ganin bacin ranta kamar na ranarba.Nan na bata hakuri,na ce wasa nake miki fa.Da kyar ta wuce.
Akwai wani mu'utamar da ayi a garinmu,Ramin-Kura na yini daya watanin baya,a wannan lokacin ban samu shigaba.Sai dai na samu na je an rufe da ni,wannan lokacin ta zo,to ni banma saniba,dayake kafin program din mun yi waya ta ce bata zoba.Mu shiga kawai na nufa wurin zama zan je na zauna,sai naga tana kallona,tana murmushi.Nan dai nima namata.To a zo a tashi wayana ba credit,balle na kirata mu hadu mu gaisa.A nan dai a zo zata tafi na ganta cikin mutane sai ta kallen,na kalleta ta yi dariya,sai su kama hanya har sun fara tafiya sai ta jawo abokiyar tafiyarta ta tsaya,anan sai na nuna mata da hannu su tafi kawai.
Bayan an tashi,sai na hau WhatsApp,nake bata hakuri kan rashin haduwarmu,dayake tsarina ban haduwa da ita cikin mutane da yawa, cikin taro.Ta ce ba komai.Yau she zaka zo to,sai na ce zan zo,amma ban san ranaba.Dayake ni yanzu ma wlhy duk lokacin da na yi nufin kawo miki ziyara sai na ji ya warware,kamar wani wanda ama tsafi,sai ta yi dariya ta ce,ai kamar wasa ka dade rabonka da saminaka.Nan na ce,ina shigowa kwanakin baya.Lokacin in na Kira number naki baki dauka.
Nan har naga ta sanya wani hoto da su yi gun mu'utamar,sai na ce ina so wannan hoton,anan sai ta turomin duk hotunan da su yi.Na ce,amma kin sha kyau My,sai ta ce,uhmm na gode.Sai na ke cewa,Amma zan so amin wanka ni kadai,da zan gani.Sai ta ce,uhmm.Karka damu ai kafi karfin haka.Yau she zaka zo,nama alkawarin zanma.Anan sai na ce a satin nan in sha Allah.
Cikin satin sai a zo na bar gida,mu tafi zaria ABUTH za a yiwa kanina aiki,hakan yasa bamu haduba a satin.To na zo na kirata sai take fadimin bata da waya yanzu,wlhy wayarta ta fada ruwa.Sai na ce Allah ya kyauta.
To mun sati daya a asibitin,na yi zaton zamu dawo,bamu dawoba.Sai ana gobe muzaharar ashura,sai a kiran da wata number,sai na dauka,sai na ji ita ce,ta ce min in kira.Na kira mu gaisa,sai nake cewa Wana number fah,sai ta ce ai wayar kawarta ce ta ara.Wata yar kusa da su.Anan sai take ce min:"My zaka shigo muzahara ko,ina son ka zo".Sai na ce:Wlhy bana gida muna asibiti tare da kanina an masa aiki,ta ce, Allah sarki Allah ya bashi lafiya.Haka dai duk da bata da waya takan yawan min flashing a kai akai muna gaisawa ta layin kawarta.Har na zo mu dawo.
To na dawo,ban dadeba kwana na biyu,na sake komawa zaria.Na yi kwana 5,na dawo.To da na dawo.Sai mu kara waya da ita,mu yi hiranmu,karshe take cewa yau she zaka zo ne.Na ce karki damu zan zo.
Na zo,wani yake cewa ai Khaleesat ma ta kusa aure,anan na ji wani iri,amma na daure.Sai nake ce masa ba damuwa,aiko zan mata kokari sosai ko da bani na auretaba,domin zamnmu da ita ta rike amana.Kuma har yanzu bata taba cewa,ko nuna bata yi daniba.Zan dauki wanna a matsayin kaddara,dama ba komai ake nema a samuba.Nema dole ne,samu na gun Allah.
Bayan kwanaki kadan,na zo ciwon kai watara rana,ya kamani lokacin na wuni a daki,na sha magani yayi mun sauki.Sai na samu na fito da dare,can ya kara dawo mun cikin dare.Lokacin na kai kwana biyu,ban jin dadi kullum sai na sai magani a chamest,to karshe ya zo,naji wuya na ya fara min ciwo,hadiya na ban wahala ko yawo na hadiye zafi.Ciwon kai ya bari,haka dai n haveata shan maganin ciwon wuya din.Har wata rana muna zaune haka,sai nake baiwa wata mamana labari,wallahi kwankin nan ban jin dadi, shekaran jiya ma har tunanin zan mutu na fara yi,ga ciwon wuya yanzu da kyar nake hadiya zafi.Sai take cewa na je wurin wani wanzami ya dubamin,in na tsarawa ne ayi,in kuma magani zai baka ya baka.
Anan akwai wata sister na sai take cewa:"Ai ciwon wuya zafin,ai kaima sai an tsarama",sai na ce tsarawa kuma,shi ya ake yi.Sai ta ce:"Ai aska da wani karfe ake cusawa can makogaro sai a tsaga",sai nake cewa:Da zafi?,ta ce:"Eh".Nan nake cewa tab,ni kam nawa ba za a tsaraba in sha Allah,anan har muke hira,nake cewa:Ciwon wuya fa yana kashe mutum,sai wannan maman nawa ta ce, sosai ma kuwa in ya zo a ajali.
Nan dai bayan kwanaki kadan na ji sauki,a zo har na warke,kamar ban yi ba.
To ina zaune,sai na daga waya na kira Khaleesaty don mu gaisa,don na yi kwana biyu ban da lafiya,ban samu na kirataba.Da na Kirata na sameta,mu fara gaisawa sai na ji muryarta,ya canza.Maganarma bai fita sosai,sai nake cewa:Lafiya kuwa,sai ta ce:"Wallahi ciwon wuya nake yi, maganama dakyar nake yi",sai na ce,tab lallai kina shan wuya sannu.Ai ciwon wuya da wahala.Nima kwanaki na yi na warke,amma nawa na ciki ne,sai nan take cewa:"Ai nima haka ne na ciki ne,wlhy da kyar nake magana",na ce Allah sarki Allah ya baki lafiya.Nan sai na ji tana wucewa tana ta gaida mutane,sai nake cewa:Ke magana na baki wahala ne amma sai gaisuwa kk,ta ce:"Ai bari kawai na dole ne.Nan sai na ce,sai anjima ki gaidamin da Umma.Ta ce toh.
Allah ka idda rahmarka, ga ruhin Khaleesaty, mai halin girma.
Zan ci gaba...