A duk sanda naga wasu masoya,nakan raina irin soyayyar da suke,in na tuna da irin soyayyar da Khaleesaty take min,mai cike da amana.Abokanai da yawa duk wanda ya ga irin salon da muke bi,ko da labari ya ji,sai mun birgesa.
Akwai wata rana,na shiga daki don in kwanta,a wanna lokacin bayan na shiga daki,sai na daga waya don kiran Khaleesaty,na Kira number nata.Mu yi hira,to dama na saba mata da bata labari na nishadi,wani lokaci na dauko kissa na bata na Annabawa ko A'imma,kuma a tsarin bata labari duk lokacin da zan bata labari ina dauke wanda zamu dauki wani darasi ne.Daga karshe na nema ta fadimin wana darasi ta dauka.Ahaka mu tafi duk lokacin da zan bata wani labari sai na tabbayeta darasin da ta dauka ciki.
Akwai wani labari kissa da na taba bata,na wani Areefy,a kissar an ce,ya kasance shi mai tsoron Allah ne mai kula da dokokin Allah,mutanen gari da suka fahimci hakan,sai su nema su bata masa alakar dake tsakaninsa da Allah,akwai wata shaidaniya ta shahara a karuwanci,haka su turata don ta je ta rinjaye wanan Areefy din,to da ta je sai ta yi dubara ta san in ta je haka nan kawai ba zata samu muradintaba.Sai ta hada makirci ta je da gudu tana ihu,tana zuwa kofar gidansa se ta buga tana ihu,sai wanan Areefy ya ce waye,sai ta ce ka taimaken zasu xubda min da mutumcina.Anan saboda tausayi ya sa ya bude mata,tana shigowa ya rufe,anan kawai sai ta fara cire dan kwalinta,tana kokarin cire riga.Annan sai wanan Areefy ya fita daga hankalinsa,har sha'awarta ya fara debansa,har ya kai da ya kama hannunta ya fara wasa da ita.An wanan yanayin kawai hankalinsa ya dawo jikinsa sai yayi wuf ya kufce hannunsa,nan ya fara tunanin girman sabon da yayima Allah,an ce a wanna dakin akwai wutan gwarwashi a kasko,se ya nufa kan wutan nan,ya sanya wanna hannun da ya kama hannunta,ya saka cikin wannan gwarwashin,saboda tsoron abun da ya aikata,a ce a wanna lokacin wanan karuwar ta fita da gudu ta je ta baiwa wadanda su ka turota labari,ga shi can ya kona hannunsa.
A wanna labarin,bayan da nagama baiwa Khaleesaty,sai nake tambayarta wana darasi ta dauka.Ta ce ta dauki cewa duk lokacin da zaka sabawa Allah to ka tuna girman azabarsa,saboda ganin wutan lahira ya fi na lahira,ya sa ya sanya hannunsa ciki wuta don kara samun tsoron Allah.
Haka dai mu ci gaba,tana da son labari,nima ina kokari wurin na bata wacce zamu dau darasi,wani lokaci na bata na nishadi.Ni kuma yawanci ban cika tambayartaba,amma a duk san da muke hira tana kokari wurin sanar da ni,sirrukanta.
Akwai sanda na kai mata ziyara,muna hira haka,anan sai take ban labari,cikin labarin take ce min ta kai kusan shekara tara tana kaduna.Bayan rasuwar mahaifinsu shi ne ta dawo nan.Anan tausayinta ya kama ni,abun da ya fara fado min shi ne,maraicin mace ba karamin maraicin ba ne.Anan na tuna da cewa nima mahaifinmu ya rasu,amma banma sanshiba.Ita ko ta sanshi ga ta mace.Na ji tausayinta sosai.Anan har nake bata labari nake cewa Allah sarki, Allah ya kara muku hakuri,lallai akwai zafi sosai rashin uba.Gashi kin ma sanshi(dayake bai wuce shekara huduba da rasuwa),lokacin da mu yi maganar.Anan nake ce mata nima mahaifinmu ya rasu amma tun ban wuce shekara 3 ba,domin rarrafe nake lokacin.Anan sai take cewa,Allah sarki, Allah ya musu rahmah,har take ban shawara take cewa ita mace ce,ba zata wani dadeba.Ni ne zan iya dadewa,na dage na yi karatu.
A nan ta ban labarin yayansu Saifullahi,take cewa:Yana kokari damu sosai,shi ne ke kula da duk sha'aninsu.Take cewa yanzu ma yana school yana karatunsa,sanan kuma yana kula da namu.Nan sai nake cewa Allah sarki,Allah ya kara masa gwarin gwiwa.Muma haka ne,lokacin da Abbanmu ya rasu,tun muna rarrafe har zuwa yau Babban Yayanmu yake kula damu,bayan rasuwar mahaifinmu yayunmu sun yi aure fiye da mutum biyar,kuma duk shi ne jigo.Ya dauke mu kamar yayansa,na ce mu dai maraici,sai dai mu ce mun rasa uba,mun rasa shakar wanan numfashin dake tsakanin da da mahaifi,amma komai in muna bukata in dai mai amfani ne,bamu rasawa.Sai take cewa,Allah ya saka musu da alkhairi.
Wata rana,dayake ta riga da tasan yan gidanmu,domin ta sansu a hoto,nima duk ta ban labarin yan gidansu,to wata rana,na kirata sai take cewa dazu Abban yaya su bar wurin program(dayake in dai zan mata magana kanshi,Abba yaya nake cewa),har farkon fada, take dariya haka,sai nake cewa eh mana,to bakiji an ce babban wa ubaba,in ji masu hikma,to shiyasa ya zama Abba yaya.To itama dai a haka ta zo take kiransa.Shi ne dai take fadi min,to ta kiran lokacin ta zata na zo ne,sai na ce ai ban samu zuwaba,ni sanyi ma ya hanani,kar na yi mura.Nan take cewa ai ko an sha sanyi,domin ita yanzu murama ya kamta.
Soyayyarmu a haka ta ci gaba,ba damuwa ko kadan,wlhy sai shakuwa,da girmama juna.
Har a zo wani lokaci,da ta rasa waya,bamu samun yin waya.Anan sai na sa wani abokina akan ya amso min number Ummansu,to ya samo min,to lokaci-lokaci na kan kira Umma mu gaisa,in mun gaisa na ce a baiwa Khaleesaty, Umma ta bata.Mu yi firanmu.Haka dai na yi ta yi,to wata rana sai na kira Umma,bayan mun gaisa.Sai na ce Khalisah na kusa,sai Umma take cewa waye,sai na ce Jamilu ne,Umma ta ce daga ina,na ce Ramin-Kura.Anan sai Umma take cewa:"Yauwa yayanta ya ce in fa dagaske kake ka turo",to anan dai ban cema Umma komaiba,se to, bayan haka ta baiwa Khaleesaty wayar,mu gaisa sai nake cewa ya naji muryanki ta canza,sai take cewa wlhy zazzabi take.Na ce Allah sarki,Allah ya kara lafiya.Bari na barki ki kwanta ki huta.
To bayan mun gama waya,sai naji zuciyata sai bugawa take,na kasa samun natsuwa,na je gida na saka abinci,na yi cokali daya na ji bazan iya ci ba,na koma daki na shiga na rufe.To abun da ya kawo rashin samun natsuwa na,shi ne,ji nake kamar za a rabamu ne.Domin ni yanzu bazan iya fadima Babban yayanmu,maganarba saboda mun gama secondary 2018,mun zana wata paper "Nbais" ta zo ta fita,mun ga ba sunanmu ba ne.Hakan ya sa kusan kullum fada yake mana,kan cewa kamar laifinmu ne,na yi tunanin yanzu in na taresa da maganar bacin 2019 na apply din school, admission kawai nake jira.Zai ce ban son karatu ne,kuma shi yana son mu yi karatun.Haka dai na rasa yadda zan yi.Na yi tunanin na tura wata Mamanmu ta je ta same Mamansu su Khalisah,akan cewa dagaske nake,amma yanzu bazan yi aureba saboda karatu,sai nan da shekara 3-4.Nan ma dai naga duk ba shi ba ne.Lokacin na wuni ina tunanin yanda zan yi don kar wanna abun yayi sanadin rabuwarmu da Khaleesaty.
To,haka dia na kwanta cikin tunani,to na kwanta na yi mafarkin ai Khaleesaty ta zo garinmu.Lokacin muna karatu tare da babban yaya,azo a fadimin ga Khaleesaty can tana kiranka.Nan sai na ce ma Babban yaya bari na je,da naje mu yi Hira mu dade sosai.Dare yayi,daga nan na ce mu je na kaiki gidanmu,na kaita.Ni kuma na dawo daki na kwanta.
Wannan mafarkin,bayan na tashi,sai na ji na dan samu,natsuwa a raina.Anan sai na sanya cewa:Aure kaddara ne,zan barma Allah lamarin,in Allah yayi zan aureta sai ta kai shekarun da zan yi.Haka nan dai na kai kusan kwana uku ina tunanin yanda zan yi na samu kwanciyar hankali,har na fara tunanin zan fadama Umma,to abun da zai faru shi ne,ko na fadi mata Abba yaya,ba zai amince ba,domin karatu yake son na yi,har na fara tunanin yin wata addu'a don samun rinjayen ra'ayi,shi ma dai haka ban yiba.Na dai barma Allah lamarin.
Lokacin mu dade bamu yi waya ba,domin bata da wayar,Umma ce dama nake Kira ta bata,gashi kuma ta taren da maganar nan,bayanda zan yi.Ni kuma ina jin kunyarta sosai,ba zan iya tsayawa mu yi magana sosoiba.Mun kai wata biyu,bamu ko waya,wata rana dai muna chat da abikina,sai yake ce min yau sun gaisa da Khaleesaty,har sun yi magana kaina.Anan yake cewa ama tana sonka fa dan uwa,nan sai na basa labarin abun dake faruwa.To ya dai tausayamin,nan dai ya ce na kwantar da hankalina,zai sameta ya ji ta wurinta wana mataki ta dauka.To haka dai a tafi ahaka,ina zaune wata rana sai naga kira,ina dauka sai na ji ita ce,mu yi hira sosai.Sai na ke cewa wanan number din fa,sai ta ce wlhy makota ta shiga ta ara waya ta saka number na,ta kiran.A lokacin ban tuntubeta kan wancan maganarba,haka nan ita,har mu gama mu yi sallama.
To nan dai sai,wata rana wannan abokin nawa,ya min magana,ya ce ya sameta sun yi magana.Yake cewa:"Ta ce masa,ai yayansu shi baima saniba,Umma ce kawai ta fada,ta ce kar ka sake kiran Umma,in ba hakaba komai kan iya faruwa".Anan sai na ce to,zan ma share number din.
To anan sai naji dadi,ta zo ta yo waya,lokacin na cike Kaduna state University,na bata labari,take cewa su ma shekara mai xuwa zasu zana.Har take cewa ai tana da yaya yana karatu a can,akwai wanda ta sani suna karatu a can,anan har nake ce mata kema ai zaki zo ki same mu ko.Ta ce uhmm.Eh.
Mu dai ci gaba da soyayyarmu,to har azo maulud na garinmu 2019,a wanna lokacin mun dade bamu haduba,na kirata,dayake an yi muzahara,ban gantaba.Sai na dare kuma,na kirata na ce:"Ban ganki ba a muzahara,ta ce:eh ban samu zuwaba",na ce zaki zo na dare ne,ta ce tana son zuwa amma bata da kudi,gashima yanzu ana ta shiga muta,kamar na yi fuffuke na zo.Sai na ce,karki damu,ki zo,sai take cewa,to,sai nake cewa nawa ne kudin ta ce ba zai wuce 200 ba.Anan na ce ta zo to.
Ta zo,suna shigowa ta kiran ta ce,ga su a Ramin-Kura,na ce sannunku da zuwa.Nan dai ta kace wayar,to can anjima ta kiran,take cewa ni fa banganka ba My,kana ina.Sai na ce zaki ganni,ai wurin da jama'a ba dole ki ganniba.Anan na ce anjima zan kiraki.Ta ce toh.
To mu je gida,bayan da zamu dawo.Sai na kirata na ce,mu hadu a fudiya,sai take cewa ai ita ta manta fudiya,domin ta dade rabonta da ita,nan sai na ce to ki nema sister yar Ramin Kura ta kaiki,nan muna waya dai ina ji tana neman sister yar Ramin Kura,nan sai ta ce babu anan.Nan sai na kira wata sister na,na ce kije ki nema ina ne,yan smainaka suke.Ki ce wacece Khalisah,ki rakata fudiya,ta ce to,bayan haka dai na kirata na ce gashi nan nasa wata ta zo ta nuna miki.Anan na kira sister na, ta ce,bata gantaba.Daga karshe dai Ukasha ya ce,mu tafi kawai mu zo da ita,to mu tafi a hanya sai nagansu tare da sister na,anna ban musu maganaba.Sai na ce ma Ukasha sun wuce ma,mu bi bayansu kawai.Suna zuwa ta kiran ta ce gasu a fudiyan,na ce to gani nan.Bayan da muje,sai nake tsokananta nake cewa,duk kin wahalar damu,fudiyan ne baki saniba.Sai ta yi dariya tace,lallaima ko ka wahalar daniba.Nan su gaisa da Ukasha,mu ci gaba da hirarmu.Mu tashi dayake,hanya ne,mu koma can ta ciki,anan dai sai nake tsokananta da cewa,da zan ga wani hoto da na nuna miki,to ama yayi nisa zai ban wahala.Sai nake cewa na sama miki Kawa ce,sai naga ta dan bata rai haka.Sai na yi dariya na ce,zaki iya kishi da yar shekara 4-5,sai ta yi dariya ta ce tab,da na yi aure da wuri ai da na haifeta.Take cewa,ni fa a wurina kishiya abokiyar zama ce,in na rigaki zuwa ki na dauke ki kanwa,in kuma kin rigan na dauki abokiyar zama.Nan dai mu ci gaba da hiranmu.A karshe sai take cewa,wayana ba chaji da na nunama hoton wani saurayina(ta rama kenan),anan sai na ce,mene,tab.Sai ta yi dariya ta ce,wasa nakema wlhy a wayata ma bamu hoton wani.
Anan sai naji,mallam ya hau munbari,sai take cemin ya kamata ta koma.Suna tare da Mama ne,ta san zan fitoma ba zata barniba.Sai na ce hakane,gaskiya Umma na sonki sosai,tana kulawa dake.Nan dai na ce ta gaishemin da Umma.Mu dawo wurin program,anan sai su hadu da wani abokina.Mu tsaya sai su gaisa,daga karshe dai take cemin,to sai na zo,gobe gai da umma.Sai na ce dagaske kk,ta yi dariya ta ce,to kasa ma na fasa.Nan dai nake cewa ya kamata mu koma,domin ni din nan ina son jin lecture din Fasihul lisan,sai take cewa ai ya iya jawabi,ta san shi,makocinsu ne a Kaduna.Yayanta ne,sai na ce Allah sarki.Nan mu koma dai wurin program din.
To washe gari.Na kirata na ce,ki shiga whatsapp ki sauke jawabin Fasihul lisan,domin jiya kin hanamu sauraro,sai ta yi dariya ta ce,ka hanani dai.
To haka dai,mu ci gaba da soyayyarmu duk da wancan damuwar,bata canza minba.Nima haka dai,abun sai gaba yake.
Kai Khaleesaty tana da halin girma,rayuwarmu ta ita ta koyar dani abubuwa da yawa,akwai wani lecture na Mallama Fatima,shirin alwilaya,na Mafificiyar mata,a wanna lokacin na tura mata,bayan na sauke na saurara.Da yake duk ana magana ce akan kyawawan dabi'un sayyada Zhra,da zamantakewarsu da imam Ali.Na tura mata,dayake sau daya duk abun da nasan zai amfaneta na kan yi kokari wurin tura mata.Akwai lokacin da na sauke addu'oi na A'imma,su jaushil kabeer,sageer,tawassul,kumail,ziyaratul nabi, addu'oi yaumiyya,nadba,da sauransu.Duk sauti a lokacin ita na fara tura mata.Na ce ta sauke.Har nake cewa in baki da data na turo miki da kudi ki saya ki sauke.Sai ta ce Aa zata sauke gobe.Gobe na tambayeta ta ce ta sauke,ta yi godiya.Dayake in ta min godiya,na kan rama,ma'ana ta koyamin,sai na ce ki godema Allah da ya bani ikon turo miki.
Zan ci gaba...