"Mun sanya wa tutar Faransa wuta ne don martani na kai hari ga Musulunci da Musulmai da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi" Cewar Sheikh Sidi Munir Sokoto


Yau 17 ga Rabi’ul Auwal 1442AH wanda yayi daidai da 3 ga Nuwamba 2020, Mabiya shaikh Zakzaky ya fito kan titin Babban Birnin Tarayya don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).


Jerin gwanon da aka gudanar yau da yamma ya sami halartar da yawan mutane kuma ya kasance mai ban sha'awa da nasara.


Masu zanga-zangar sun Kona tutar Faransa don nuna cikakken goyon baya da biyayya ga Annabi mai daraja, kuma sun kara da yin Allah wadai da ayyukan Emmanuel Macron bisa batanci ga Manzon Allah.


A yayin sanya wa tutar Faransa wuta Sidi Munir Sokoto ya bayyana cewa “mun banka wa tutar Faransa wuta a wani martani da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi wa Musulunci da Musulmi tun bayan munanan laifukan buga zane-zanen Manzon Allah da mujallar Charlie Hebdo ta yi. Don haka muke yabawa yakin da ake yi a halin yanzu a tsakanin Musulmai da duk masu kaunar zaman lafiya da mutuntaka…”


A kasa wasu hotunan taron ne 






Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post