Bismillahi Rahamanir Rahim.
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Aliy Muhammad.
Godiya da jinjina su tabbata ga Allah SWT mamallakin dukkan duniya da abinda ke cikinta, Wasila da Fadila su tabbata ga Wanda aka aiko yazama Rahama ga dukkan hallita, Shugaban mu, Masoyin mu, Abul Kasim Mustapha Muhammad Dan Abdullahi Shugaban farko da karshe da dukkan nin iyalan gidansa tsarkaka.
Maudu'i: -Muhammad Mahmoud Turi, A Tsakanin 'Yan Uwa da Al'ummar Gari.
Gabatarwa: Sheikh Muhammad Mahmoud Turi, bawan Allah ne wanda bayani akansa ko kuma fadin waye shi yana bukatar binkice mai tarin yawa. Sheikh Turi mutum ne bawan Allah wanda akalla 'yan uwa dama sauran Al'ummar gari sun shaidesa akan saukin kai ga hakuri wanda har saboda hakurinsa wani Dan uwa yake cemini ai shi Sheikh Turi bai masan menene fishi ba, idan kuwa kaga yayi fishi to tabbas akan Allamma Sayyid Zakzaky (H), ne. Yana farin ciki da farin cikin sa haka ma yana bakin ciki da bakin cikinsa. Sheikh Turi mutum ne da yake yafiya tun kafin anemi yafiyasa, mutum ne ma'abocin kunya da gaskiya mutum ne mai taka tsan-tsan acikin dukkan al'amuran sa, jarumi mai karfin zuciya da imani Wanda yakai ga ana cemasa ya sunkwiyar da kansa ayayin harin da azzalumar gwamnati Najeriya takai a Zaria ana harbi kuma ya tabbatar da cewa zasu iy harbinsa amma ya ce ina "Mace bata haifi Dan da zai durkusawa ba matukar akan kare jagoransa ne". Sheikh Turi mutum ne wanda bai san menene tsoro ba saboda baya shakkar fadar gaskiya agaban kowaye. Idan magana ce akan Iliminsa, Sallamawar sa, Makarumil Akhlaq, Kwarjinin sa, Haibarsa, Tsabtarsa, Imanin sa, Tausayinsa, Hankalin sa, Sadaukarwar sa, Zumuncin sa, Ibadar sa, Takawarsa, Rikon Amanar sa, ko Tsantsenin abin duniya to gaskiya bansan ta inda zan fara ba saboda hankalina da tunanina bazasu iya hango girman wadannan bangarori na rayuwarsa ba. Sheikh Turi ta kowanne janibi Kamil ne ba Nakis ba wannan shine Sheikh Turi atakaice a matsayina na Wanda bansan shi sosai ba.
Sheikh Muhammad Mahmoud Turi A Tsakanin 'Yan Uwa: Mu'amalar Sheikh Turi da Yan uwa takasu kusan kashi hudu.
1. Yana mu'amala da yan uwa amatsayinsu na yan uwa a addini wato hatta dashi kansa amatsayin mu na almajiran Sheikh Zakzaky (H) gaba daya kenan.
2. Yana mu'amala da yan uwa amatsayin sa na wakilin sayyid Zakzaky (H).
3. Sannan yana mu'amala da yan uwa amatsayi na kannai agunsa kokuma amatsayin uba ga ya'yansa.
4. Sannan Sheikh Turi yakanyi mu'amala amatsayin aboki ga sauran yan uwa wanda bambancin shekaru, wakilci na Sayyid Zakzaky (H) duk hakan baya hanashi yayi wasa da dariya da yan uwa.
Sheikh Turi yana mu'amala da yan uwa batare da ya nuna bambanci tsakanin wani Dan uwa da wani ba kokuma tsakani wata yar uwa da wata ba wato indai kai Dan uwa ne to dai-dai kake da kowa awajen sa. Haka nema yasa wannan Dan uwa sai yaga kamar yafi kowa kusa da Sheikh wancan ma sai yaga ai shi ne yafi kusa da kowa awajen Sheikh saboda iya mu'amala da sanin yakamata. Sannan Sheikh Turi yana matukar kula da Yan uwa in dai kuna haduwa dashi ko awajen karatu ko wajen Sallah to matukar yayi Kwana biyu baigan kaba to insha Allah sai yasa an tambaya lafiya ko ba lafiya ba. Idan kuma muka koma bangaren Yan uwa mata Sheikh Turi yana matukar tausaya musu ta kowanne bangare kuma yana la'akari da rauninsu wajen saka lokacin yin (program) taro saboda saukaka musu yadda bazasu takuraba. Sannan duk wacce takawo kara azaman takewar aure to insha Allah sai ya tabbatar da ya nemo mata hakkinta. Haka zalika Sheikh Turi ya samar da wani bangare na harkokin aiki musamman bangaren gini kama daga sayan fili har zuwa kammala rufi dakomai na gida Wanda hakan ya tabbatar da cewa dayawa daga cikin Yan uwa maza sun samu aikin yi ta wannan hanyar. Idan kuma muka dawo ta bangaren mu'amalar sa da iyalan shahidai sanin kowa ne cewa Sheikh Turi yasha fada a tarurruka daban-daban cewa 'Bamu da aikin da yawuce tallafawa da kuma kula da ya'yan shahidai' hakan tasa yakan ware lokaci na musamman yakai musu ziyara har gida sannan ya tambayi matsalar su sannan yayi kokarin ganin an share musu hawayen su. Haka ne yasa ya'yan Shahidai suke tsantsar kaunar sa tare da jindadin yadda yake karfafa musu gwiwa wajen jajircewa akan abinda yashafi gwagwarmaya. Sheikh Muhammad Mahmoud Turi yana mu' amala da yan uwa dai-dai gwargwadon yanda kazo masa misali; idan kazo masa amtsayin almajiri to amatsayin Malaminsa zaiyi mu'amala da kai, idan amatsayin neman shawara kazo masa dashi to shawarar zaibaka amatsayin aboki ko Dan uwa ko kani, haka idan amatsayin makocinsa kazo, kokuma kazo masa amatsayin dansa haka ko tawanne irin janibine yasan yadda zaiyi mu'amala dakai batare da yanuna maka bambancin shekaru, girma kokuma karatuba saboda iya mu'amalar sa.
Sheikh Muhammad Mahmoud Turi A Tsakanin Al'ummar gari: Mu'amala ko muce dangantakar Sheikh Turi da Al'ummar Gari, dangantaka ce ta addini wajen gaskiya, rikon amana, sanin yakamata da girmama mutane da sauran su. Misali awajen rikon amana Sheikh Muhammad Mahmoud Turi yakai matsayin da akwai lokacin da mahaifin sa yabashi ajiyar wasu kudade masu yawan gaske amatsayin ajiya. Wannan kudade sun dade sosai awajensa hartakai ga shi mahaifin nasa ya manta dasu sai shi Sheikh ne ya tunasar dashi cewa ya taba bashi ajiyar kudi, mahaifin nasa yace shi yamanta da wannan kudi. A nan take Sheikh Turi yabashi labarin lokacin daya bashi da rana har da ma watan da shekarar sannan yamaida masa kudin sa Kamar yadda yabashi. Acikin littafin Shekaru sittin 60 Masu Albarka na Sheikh Zakzaky (H), shafi na 103. Nakaranta wajen da Sheikh Turi yake bada amsa akan wata tambaya da aka yimasa acikin amsar ya zo daidai wajen da yake bada labarin zuwansu Hajji shi da Sayyid Zakzaky (H), saboda gaskiya da amana ta Sheikh Turi shine Wanda Sayyid Zakzaky (H) ya amincewa amtsayin me asusun ajiyar kudaden da sukeyi Wanda suke sayan abinci da abin sha har zuwa lokacin da suka kammala aikin Hajjin.
Ta bangaren girmama mutane kuwa akwai lokacin da wani makocinsa Dan Izala yake cewa da dukkan al'umma irin Mallam Turi ne to da baza aji wata hayaniya tsakanin Dan Darika da Dan Izala ko da Dan Shi'a ba. Saboda shi mai fadar wannan maganar yaga mu'amalar da baitaba ganin wani mai irinta ba saboda yana cewa akwai lokacin da ya gaiyyaci Sheikh Turi daurin auren yarsa to babban abinda yabaiwa wannan makoci nasa mamaki shine Sheikh Turi yama rigashi zuwa muhallin daurin auren. Sannan Sheikh takai matsayinda agidan sa ake taruwa wajen warware matsalolin dasuka shafi unguwar dayake zaune batare dayanuna musu bambancin Mazhaba ba. Sheikh Turi baitaba gazawa dai-dai da rana daya ba wajen amsa gaiyyatar da makotansa suke aiko masa wajen daurin aure, radin suna kokuma janaza. Bayan waki'a ane aka fahimci cewa duk likkafanin da ake dinkawa mamatan unguwar Sheikh ne yake siya yabaiwa limamin massallacin dayaji inda akayi rasuwa sai aje akarba adinka badan waki'a ba bazamu San wannan ba saboda yace kar afadawa kowa. Haka duk lokacin da ya gaiyyaci makotansa, suna farin ciki dakuma amsa gaiyyatar da yayi musu. Nasamu labari ayayin binkicen danake cewa akawai lokacin da wasu 'yan izala Wanda suke makota da gidan mahaifin sa acan Kaduna, su wadannan 'yan izala suke cewa ''yan shi'a batattune tabbas amma banda wannan bawan Allah dake cikin su wato Sheikh Turi. Wanda wannan yana nuna iya mu'amalar sa ce tasa har ake masa irin wannan shaida. Bangaren sanin yakamata Sheikh Muhammad Mahmoud Turi abin bada misali ne saboda sau tari yakan shiryawa lokaci zuwa lokaci yakaiwa abokan karatun sa ziyara na cikin harka islamiyya da nawajen ta. Misali akwai lokacin da yakai wa wani Mallami babban Dan izala a Kaduna ziyara ta zumunci. Bayan yadawo gida sai shima wannan Mallami yaga yakamata shima ya ramawa Sheikh wannan zumunci. A lokacin da yazo Kano sunyi mu'amala sosai har takai ga bayan Sheikh ya jagorance su sunyi Sallah Azhur sai shi Sheikh ya umarci wanna abokin nasa da ya jagorance su suyi Sallah Asr. Sheikh yace ai yanzu kaine bakon mu kuma kana kan hanyarka ne ta sada zumunci mu kuma muna neman tabarukin dake tare dakai. Hakan Tasha faruwa ba sau daya ba basau biyu ba yakan saryantar da limanci ga ma'abota ziyara koda kuwa wahabiyawa ne saboda baya la'akari da bambancin Mazhaba mutanen gari yana mu'amala dasu dai-dai da dai-dai.
Sheikh Turi makotansa sun tabbatar da cewa duban marar lafiya aikinsa ne sannan yakan dauki nauyin marasa lafiya batare da yaduba bambancin Mazhaba ba. Mafi kankantar kyautar sa binkice yanuna baya kasa da dubu goma musamman ga Al'ummar gari. Haka bangaren tsaro (security), na unguwar dayake zaune shine Wanda yasamar dashi wanda wani Dan uwa yatabbatar Mana dacewa akwai lokacin da Sheikh ya ce shi ba iya Markaz yakeso a baiwa tsaroba wato gaba daya unguwar yakeso abaiwa tsaro da kariya kuma hakan akeyi. Ta bangaren taimako ya baiyyan bayan waki'a cewa akwai baiwar Allah data muslinta kafin waki'a tazo ta tabbatar dacewa shine yake daukan nauyin karatun ta. Sannan akwai gidan da Sheikh Turi yake musu albashi kusan duk wata yakan basu dubu goma ko shabiyar wadan da ba yan uwa bane saboda hali na rayuwa dasuke ciki. Yanayin ka'idojin da aka sanyawa wannan gasa bazai bari mufadi adadin ya'yan da Sheikh Turi ne ya yanka musu ragunan suna ba, misali kwara daya shine yaron da akeyiwa lakabi da Dan Mallam Turi, sannan bazamu iya kawo adadin yan uwa da Sheikh yabaiwa shawara su koma karatu ba, sannan Sheikh yasha amsa gaiyyatar Mauludi na yara kanana yakan basu gudunmowar kudi sannan yaje ya amsa gaiyyatar kamar yadda yake fada cewa "idan su yarane wadanda suka gaiyyaceni to ai shi wanda akeyima Mauludin ba yaro bane".
Kammalawa, atakaice dai Sheikh Turi mutum ne Wanda babu Wanda zaiyi mu'amala dashi ta tsawon wuni daya batare da yaga addini ataredashi ba. Yana mu'amala ne mu'amala ta addini da kowa. Duk wani abu da kaga Sheikh Turi yana aikatawa to lallai addini ne wato yakasance mutum ne da baya aikata aiki sai yasan hukuncin Allah acikinsa. Gaba daya rayuwarsa addini ce tsantsa Kuma abar koyi agaremu. Muna adduar Allah Swt ya gaggauta baiyyanar sa Bihakki Sahibul Asr Ajfr.
Madogarar binkice/reference
1. Mallam isah Shuaibu wakilin yan uwa na garin Kaugama, jihar Jigawa.
2. Alhaji sani mai magani kano
3. Mallam ado matasa Kano
4. Littafin Shekaru sittin 60 Masu Albarka na sayyid Zakzaky (H)
5. Mallam Yusuf hamza sudani kano
Rubutawa: Abdullahi Garba Kaugama
Phone number: 08138784549,08131532930
Email: abdulkaugama001@gmail.com
Address: Gerawa oil Mills, tokawara industrial area. KANO STATE.