Ni wallahi abin nan yana bani haushi kuma yana bani mamaki, wai yanzu dama acikin duniya akwai wata halitta da tafi dayarta, inba wacce tafi dayar tsoron Allah da kyawawan dabi'u ba.
Amma abin takaici, more especially ga mata, wai sai kaji tana fadar ai ita tafi karfin wane, jifa sana'arsa ko kuma jifa abin hawansa, ji fa shigarsa ai nafi karfinsa, ni sai mai kudi, mai mota, mai babban gida da duk wani abu daya shafi jin dadin duniya.
Ta manta da cewa, duk wannan dukiyar da take hange take hankoron ta riska , aikin banza ne wallahi idan babu kyawawan dabi'u da addini, saboda bazaku taba zama lafiya ba, kullum cikin facing sabuwan matsala kike, ga dukiyar amma babu damar cinta saboda tashin hankali
Kudi, katon gida ko abin hawa mai tsada bafa shine mutum ba,tabbas zuciya nasan jin dadi, amma abinda ya kamata mu lura shine, duk tarin dukiyarka duk girman gidanka da tsadar motarka, wallahi zaya zama tarihi wata rana.
Wai amma 'yan matan yanzu, mun daina kula da dabi'u da addinin wanda muke so, mun koma kula da yanayin dukiyarsa, bama hanga yacce rayuwarmu data 'ya'yanmu zata kasance, idan ya zamana babu wannan mai dukiyar,
Wallahi wallahi banga anfanin zama da mutumen dakeda dukiya baida dabi'u masu kyau da addini ba, saboda addini shine jagaba wurin horonmu akan zaman lafiya, domin duk talaucinka idan kana da kyan hali kuma kana ruko da addininka, to gidanka sai a zauna lafiya, amma gidan mai kudin da ya rasa wa'yannan ba a zauna ba.
Bance kar kice sai mai kudi ba, amma nidai a nawa ra'ayin wallahi indai kana da rufin asiri wanda zaka iya rike gidanka, iya hakanma ya isa ba sai ka zama shegen mai kudi ba, (abinda yan mata muke fada), wai har tambaya zakaji anayi, waye wance ta aura? sai kaji ance ai wane ne, kawai sai kaji taja tsaki mtssss amma ta bani kunya, wannan matalaucin ta aura,nayi tunanin wani shegen mai kudi ne, aini wallahi saimai kudi.
Hmm ta manta wanda yayi mai kudi shi yayi mai rufin asiri yayi talaka,
Nidai indai kana da hanyar neman halas dinka, kuma kanada gidan da zaka ajeni basai mai kyau ba, sannan ka cika duk sharuddan da aure ke bukata kafin ayi sa, wallahi babu ruwana da rashin motarka ko a kafa zan bika muje duk inda zamu.
Allah yasa mu dace
_ Zarah A Zamsarf