Me Yasa Da Yawa Daga Cikin 'Yan Mata Suke Rabuwa Da Samarinsu, Bayan Sun Ci Gaba Da Karatu A Makarantar Gaba Da Sakandari?.. Fita Na Huɗu (4)


 MEYASA DAYAWA DAGA CIKIN'YAN MATA SUKE RABUWA DA SAMARINSU BAYAN SUN CIGABA DA KARATU (HIGH INSTITUTION)??


PART FOUR (4)


Bismihi ta'ala


Nasani majority na wannan laifin ana dora shine akan mata, amma idan zamuyiwa kanmu adalci, to laifin na kowa da kowa ne, duba da yanayi na yadda ake tafiyar da soyayyah a yanzu.


Wani lokaci, na daya daga cikin abinda ke haifar da wannan matsalar, shine : idan har ta tafi makaranta ko shi ya tafi makaranta( high institution), to lallai dole zasu sanja yadda suke ma'amala a tsakanin su ba kamar da ba, abinda nake nufi shine, idan ada sanda tana gida kuna waya kullum, saboda babu abinda takeyi a gidan daga aekin gida sai islamiyya, idan tana zuwa kenan, to daga lokacin data fara zuwa school dole zata dan zama busy, saboda yanayin karatun secondary dana high School ba daya bane, dole zaka rika kiranta kaji Batayi picking up ba, saboda maybe lokacin da zaka kira suna lecture ne ko kuma tana wani abunda ya shafi school din.


Dole sai munyi hakuri mun dauki wannan acikin zaman takewarmu, saboda kana saurayinta ba hakan yake nuna batada wani time sai naka ba, A'a dole zaka rika kira Batayi picking up ba, saboda tanada ayyukan da zatayi ba lokacinka kadai gareta ba. Amma fa bawai ina nufin batada Time dinka kwata kwata ba, Aa sanda duk ta san zakuyi magana to duk time dinta ya zama naka, hadama hankalinta da dukkan nutsuwarta.

Amma wani lokaci sai kaga wasu mazan da sun kira bata daga ba sai yayi fushi, idanma akai rashin sa'a Sai kaga sun dauki lokaci baya mata magana, wai saboda ya kira Batayi picking up ba. To ita kullum wayarta na hannunta ne, idan bata aikin gida sai akace bata saka wayar charge, ko idan ta saka zama zatayi tayi gadinta saboda karka kira bata daga ba kayi fushi wani lokaci ma wayar na hannunta amma zataki dagawa saboda tadan ja maka aji, kuma bawai don bata sonka bane. Dole sai mun Lura da wannan ba kowane lokaci yake zaman da gangan taki dagawa ba.


To idan kuma tana school ne shima dai matsalar duk dayane, zakaga kamar ta kyaleka kota shareka ta daina kulaka, kuma Alhali karatu ne ya dauki hankalinta, idan ta samu time zata kiraka ko kai ka kirata. Amma dole zakuga kamar kunyi baya baya da junanku musamman idan tana karatu shima yanayi ne, saboda akwai CA akwai exams akwai assignments, kai ko babu ko daya dole karatu zaya dauki hankalinku.


Idan da rashin rabo sai kaga kamar ta manta dakaine saboda taje high institution, alhali ba haka bane, ko kuma ita ta rika ganin kamar ka manta da itane saboda kaje can kana ganin yan mata, alhali duka ba haka bane kawai ku duka duk kun zama busy ne saboda wani sabon mataki da kuka taka na rayuwa ...........


Allah ya bamu ikon fahimtar abokan rayuwarmu


Insha Allah zan cigaba


_✍️ zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post