Me Yasa Da Yawa Daga Cikin 'Yan Mata Suke Rabuwa Da Samarinsu, Bayan Sun Ci Gaba Da Karatu A Makarantar Gaba Da Sakandari?.. Fita Na Uku (3)


Bismihi ta'ala 


Sauda dama, wannan matsalar tana faruwa ne da sa hannun kowa acikin samari da 'yan matan, wani lokaci ma har iyaye suna shigowa ciki, har yanzu ina magana ne akan : barin saurayi saboda abin duniya, abinda yasa nace har iyaye zasu shigo, saboda wata ba tada irin wannan halin, na son abin duniya (kwadayin zama abinda Allah bai kaika ba), amma sai ayi sa'a iyayenta sunada shi, musamman mahaifiya mace anfi samun irin wannan daga gare su, amma fa ba hakan yake nuna babu maza masu irin halin ba, aa suma iyaye maza ana samun masu son abin duniya, kuma idan aka samu mahaifi ne keda wannan halin to matsalar tafi girma, tunda shine keda iko da komai a gidan, tun daga matar gidan har duk yaran gidan.


Sunsan tana sonshi, sun shafe tsawon lokaci a tare, kai ko yini dayama suka kare a tare ai indai halayyansa sunyi, an kuma yi binkice akansa kamar yadda addini ya tanada ai ba damuwa akan hakan, amma da zarar iyayen sunga mai kudi, saisu rufe ido suce shi zasu ba, dama maganar sai anyiwa mai kudi bincike ma bata taso ba,saboda shi ai alhaji wane ne, dan gidan wane, mai gida wuri kaza da shaguna a wuri kaza, don haka shi dukiyarsa ta isa ta bayyana waye shi, basai anyi bincike akansa ba, sun manta cewa 'yarsu bashine zabinta ba, amma saboda wanda takeso din bayada tarin dukiya da mota sai kawai a nuna masa fin karfi da isa.


A lokaci guda kuma, iyaye na taka rawa sosai a wannan fage, taharyar hurewa yaransu kunne akan karta kula kowa saimai kudi( amma fa wasu iyayen ne ke haka, don ba duka aka taru aka zama daya b), to idan wanda take tare dashi da farko baida kudi, sai kaga tana kokarin barinsa ta samo mai kudin, tunda dama a gida ake tarbiyya, kuma ita an nuna mata ba'a son talaka, shikenan idan kwalwarta da zuciyarta suka amince da hakan saidai kaji ana cewa ai an saka bikinta da alhaji wane.


Samari da dama sun rabu da 'yan matan su saboda hakan, wasuma wacce zasu aura tunda har maganar iyaye ta shiga tsakani, Amma a haka da anga mai kudi za'ayi duk yadda za'ayi a lalata wannan maganar a tada sabuwa.


Wani lokaci ma akwai iyayen da sune suke dagewa sai diyarsu taje high School, saboda ta hadu da samari masu kudi, wallahi akwai wayanda da dama iyayensu na turasu makarantar ne don su hadu da yaran masu kudi, bawai karatun shine hadafinsu ba, kuma tana barin gidan zasuyi kokarin korar wanda ta bari anan din.


Amma fa suma 'yan matan sunayin haka a kashin kansu ba tare da sa hannun kowa ba, saboda ita burinta kenan ace mijinta shine alhaji wane............


Zan cigaba insha Allah


✍️_ zarah A zamsarf
 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post