Bismihi ta'ala
Naji ra'ayoyin mutane da dama akan wannan issue din, kuma kusan dai idan ka duba, zakaga abu biyu ne zuwa uku aketa mai_maitawa, ta wasu sigogin na daban.
A ra'ayina kamar yadda wasu suka fada, na daya daga cikin abinda ke haifar da wannan matsalar, son mutum saboda wani abu na duniya, abinda yasa nace na duniya shine: zakaga tana tare da saurayi, amma ko yanayin rikonsa da addininsa bai dameta ba, saboda ai ba sallahrsa ko zikirinsa zaya rika bata ba, amma abinda duniya kamar irinsu kudi, Kaga wannan zaya bata ne ko kuma ya siya mata wani abu na kudin. Amma shima wlh indai yanada su kuma baya bata, to wallahi zasu rabu ne, saboda zakaji tana fadar yanadasu amma ba a ci.
Idan har tana son saurayinta, saboda abin duniyarsa to daga ranar data kyalla ido ta hango wanda ya fishi to lallai zata barshi ne, koda kuwa duk dukiyarsa ita yake bawa, data samu wanda yafishi tarin dukiya zata barshi, saboda dama can dukiyarsa take so ba shiba.
Ana samun irin hakan dayawa alokacin data cigaba da karatu, saboda a high institution kowama zaka hadu dashi, mai kudi, Dan masu kudi, mai sarauta, ko dan masu sarauta, mai rufin asiri da kuma talaka, duk zaka samu acan, to dataje ta hadu da wanda ya fika shikenan burinta ya cika.
Idanko har tsakani da Allah take sonsa to tabbas babu abinda zaya rabasu saidai ko kaddarar ubangiji, ita kuma yana kaddarawa bawa abinda yaso ne, amma magana ta gaskiya a yanzu soyayyar tsakani da Allah tayi karanci wallahi, bance ba'a samu ba, amma tabbas ba kamar a baya ba, yanzu son duniya ya lalata komi..........
Allah ka hanamu barin masu sonmu tsakani da Allah saboda abin duniya
Zan cigaba insha Allah
_ ✍️ zarah A Zamsarf