Me Yasa Da Yawa Daga Cikin 'Yan Mata Suke Rabuwa Da Samarinsu, Bayan Sun Ci Gaba Da Karatu A Makarantar Gaba Da Sakandari?.. Fita Na Ɗaya (1)


 

A lokutan baya ba'a cika samun irin wannan matsalar ba, amma a yanzu abin kullum yawa yake karawa, a wurin wasu hakan cigaba ne, amma ni a wurina wannan cigaban na mai hakar rijiya ne muka samu. 


A ganina da kuma ra'ayina akan hakan, dalilan dake haifar da wannan matsalar suna da yawa, amma ta wani fuska kuma za'a iya cewa dalili daya ne, wanda kuma bayada kishiya, shine RASHIN GINA SOYAYYAR TUN FARKO KAMAR YADDA ALLAH YACE ( rashin yinta tsakani da Allah).


A ganina da kuma ra'ayina, na daya daga cikin dalilan dake haifar da wannan matsalar, fara soyayyah a lokacin da su kansu masoyan basusan meye ya dace dasu ba, ma'ana basu san waye ya kamata su zaba a matsayin abokin rayuwarsu ba, wasu lokutan kawai suna bin 'yan abi yarima asha kida, taga wance kawarta tanada saurayi itama bari tayi, ko yaga wane abokinsa yanada budurwa shima bari yayi, amma bawai don sunsan meye amfanin hakan da tasirinsa a garesu ba.


Sau dayawa irin wannan soyayyar, na daya daga cikin dalilan dake haifar da wannan matsalar, saboda suna tare ne da junansu kawai saboda shiga tsara, ma'ana saboda suma su shiga yayi ace tanada saurayi shima ace yanada budurwa shine kawai.


Kai da kanka idan kayi duba da yanayin dabi'unsu da kuma halayyarsu zakaga basu dace da juna ba, bawai ina nufin tafi karfinsa ba, ko yafi karfinta ba, a'a ina nufin akwai hadin da kana ganinsa zaka ga ya dace, saboda ya cika sharudda da daman gaske, akwai kuma wanda kana ganinsa kasan akwai matsala idan har suka cigaba da zama tare, maybe saboda banbance_banbancen dabi'u da halaye, wanda kasancewarsu a tare zaya zamana dole daya ya cutar da daya, ko kuma wani dalili ma akasin hakan.


To daga lokacin da daya daga cikinsu ya fara kokarin neman wanda ya dace dashi, sai kaji ana cewa an yaudari juna, ba kowane rabuwar saurayi da budurwa bane yake zaman yaudara, akwai wadda dalilai ne suke haifar da hakan, kuma hakan shiya dace din. A lokacin da suke secondary School misali, zakaga a dai_dai lokacin da za'ayi masu aure to tabbas wasu sun dace da junansu, amma fa a stage na secondary, to kuma data matsa daga nan, ko ya matsa daga nan zakaga banbanci miraran da rashin dacewarsu, wanda su dakansu dama sauran al'umma da zasuyi adalci to tabbas sunsan yanzu basu dace da juna ba...........


Zan cigaba insha Allah


✍️_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post