@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA KOWANNE MAI KARATU AKE TAMBAYARSA MAS'ALAR ADDINI BA
Shi ilimi wata taska ce taskakkiya wacce ta taskace abubuwan amfani na duniya da lahira, kuma take cike da sanin abubuwan da za cutar da mutum a duniya da lahira, sannan babu mai sanin abinda ke cikinta sai mai ilimi da wanda ke yin tambaya.
Wani abin hatsarin da ke cikin tambaya kuwa shine tambayar ma'abota karatu ba masu ilimi ba. Duk wanda ya kaucewa masu ilimi ya tambayi masu karatu zai fada cikin kwazazzabon da zaiyi sanadin halakarsa.
Yazo cikin Alqur'ani inda Allah ke cewa,
الآيات النحل الأنبياء
" فَسْئَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ ."
" KU TAMBAYI MA'ABOTA SANI (Ilimi) IDAN KU BAKU SANI BA ."
Su wadannan ma'abota sani sune Al-A'immatul-Hudah Al-Ma'asumeena (A. S) wadanda Annabi (S. A. W. W) yabar mana su da Alqur'ani a matsayin jagorori ababan koyi gare mu.
Duk wanda ya sake su a bayan Annabi (S. A. W. W) ya riqi wasu koma bayansu za kuga sune halakakkun da suka zama sila na lalacewar koyarwar Manzon Allah (S. A. W. W) a bayansa.
A wannan zamani kuma masu riqo da A'immatul-Hudah sune wadannan Ahluz-Zikr da aka ambace su cikin Qur'ani.
Yazo cikin Al-Kisaal na Ibn Mugeerata da isnadinsa, daga Sakuuniyyi, daga Ja'afar daga bayansa (A. S) yace,
1- ل، الخصال ابْنُ الْمُغِيرَةِ بِإِسْنَادِهِ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنْ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ:
" الْعِلْمُ خَزَائِنُ وَ الْمَفَاتِيحُ السُّؤَالُ فَاسْأَلُوا يَرْحَمُكُمُ اللَّهُ فَإِنَّهُ يُؤْجَرُ فِي الْعِلْمِ أَرْبَعَةٌ السَّائِلُ وَ الْمُتَكَلِّمُ[1] وَ الْمُسْتَمِعُ وَ الْمُحِبُّ ."
" SHI ILIMI TASKA CE, MABUDIN KUMA SHINE (yin) TAMBAYA, KUYI TAMBAYA SAI ALLAH YAYI MUKU RAHMA. DOMIN SHI MUTANE HUDU (4) SUNA SAMUN LADA CIKIN ILIMI.
MAI (yin) TAMBAYA,
DA MAI YIN MAGANA (malami mai amsa tambayar),
DA MAI SAURARO,
DA MAI SO (yaji anyi tambaya da kuma amsar tambayar.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 197
A wata riwaya kuma wacce ta inganta cikin SAHIFATUL-RIDHA (A. S), DAGA RIDHA DAGA IYAYENSA (A. S) YACE, MANZON ALLAH (S. A. W. W) YACE,
3- صح، صحيفة الرضا عليه السلام عَنِ الرِّضَا عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص
" الْعِلْمُ[4] خَزَائِنُ وَ مِفْتَاحُهُ[5] السُّؤَالُ فَاسْأَلُوا يَرْحَمُكُمُ اللَّهُ فَإِنَّهُ يُؤْجَرُ فِيهِ أَرْبَعَةٌ السَّائِلُ وَ الْمُعَلِّمُ وَ الْمُسْتَمِعُ وَ الْمُحِبُّ لَهُمْ[6]."
" SHI ILIMI TASKA CE, KUMA MABUDINSA SHINE (yin) TAMBAYA. KUYI TAMBAYA SAI ALLAH YAYI MUKU RAHMA. DOMIN SHI MUTANE HUDU (4) NA SAMUN LADA CIKINSA.
-MAI TAMBAYA,
-DA MALAMI,
-DA MAI SAURARE,
-DA KUMA MAI SONSU. "
Cikin wata riwaya kuma da isnadinsa zuwa kan Musa Bn Ja'afar, daga iyayensa (A. S) yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace,
" KU TAMBAYI MALUMA, KUMA KUYI MU'AMALA DA MASU HIKIMA, KUMA KU ZAUNA TARE DA FAQIRAI. "
.
5 نَوَادِرُ الرَّاوَنْدِيِّ، بِإِسْنَادِهِ عَنْ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص سَائِلُوا الْعُلَمَاءَ وَ خَالِطُوا الْحُكَمَاءَ وَ جَالِسُوا الْفُقَرَاءَ."
Hikimar da ke cikin wannan hadisi shine, matuqar za ka tambayi maluma (masu aiki da ilimi) kuma kana mu'amala da masu hikima za ka amfana daga gare su.
Shi kuma zama cikin faqirai na qara tausayi da kawar da girman kai ko jiji-da-kai .
Riwayar da za mu kawo ta qarshe cikin wannan rubutu namu ita ce riwayar Zurarata da Muhammad Bn Muslim da Buraidin Al-Ijliyyu, suka ce, Abu Abdallah (A.S) yace,
" ABIN SANI KAWAI MUTANE NA HALAKA NE DOMIN SU BA SA YIN TAMBAYA ."
6 -رَوَى زُرَارَةُ وَ مُحَمَّدُ بْنُ مُسْلِمٍ وَ بُرَيْدٌ الْعِجْلِيُّ قَالُوا قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع إِنَّمَا يَهْلِكُ النَّاسُ لِأَنَّهُمْ لَا يَسْأَلُونَ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 198
Ma'anar hadisin shine, in da ace mutane za su riqa yin tambaya (a muhallinsa) kan abinda basu sani ba , to, da za su ilimantu, kuma da ba za su taba halaka ba. Amma rashin yin tambaya ko kuma yinta a gurin da bai dace ba (GHAIRA AHLIHI), yakan yi sanadin halaka.
Allah yasa mu dace.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
2nd November, 2020/ 16th Rabi'ul-Awwal, 1442.