✍ Zainabal-Akeelah Ali
Bismihi Ta'ala
Zuwan musulunci ya toshe duk hanyar da wasu za su yi amfani dasu don cimma manufofinsu ta hanyar daga musu darajarsu da kuma takaita mu'amalolinsu ta hanyar sanya musu hijabi, wanda shi wannan hijabin katanga ne daga munanan abubuwa ga mata ta kowane janibi na rayuwarsu. Sannan musulunci ya bai wa mata hakkoki dadama kamar; hakkin neman ilimi zuwa makurar da za su iya, hakkin mallakar abu da kuma sarrafa abunda suka mallaka bisa ka'ida, hakkin gado (su gada kuma a gaje su), hakkin zabar abinda suke so da sauran hakkoki.
Musulunci bai tsaya nan ba, sai da ya yi duba zuwa ga yanayin halittar mata sannan ya ba su aiki daidai da halittarsu saboda tsantsar adalci irin na addinin musulunci bai ce tunda ya daidaita mace da namiji a Dan Adamtaka, to dole ya zama aikinsu iri daya da na maza ba, ya duba bambanci na halitta, na jiki da halaye da ke tsakanin mace da namiji sai ya ba su ayyuka mabambanta kamar yadda Allah (S) ya fada cikin littafinsa mai tsarki "Wa ma khalakaz zakara wal unsa, Inna sa'ayakum la shatta". Mafi muhimmanci ayyukan mata a cikin gida suke inda suke taka rawa a matsayinsu na 'ya'ya, matan aure da kuma Uwaye.
A dukkan wadannan rawar da suke takawa, musulunci ya dora musu wani nauyi da za su sauke wanda sauke wannan nauyin shi ne mafi muhimmancin aikin mata, dadin dadawa mata sune ginshikin gyaruwar al'umma domin da gyaruwarsu ne al'umma take gyaruwa!
Sai kuma wani aikin da ke bi mishi na al'umma; mata suna da damar shiga cikin al'ummah su bada gudummuwa wurin cigabantar da al'ummah ta hanyar koyarwa, kula da lafiya da sauransu.
Zamu cigaba Insha Alla