MATA SILAR CHANJI: Musulunci Shine Ya Bai Wa Mata Matsayi Da 'Yanci Na Mutumtaka.. Fita Na Daya (1)


 


✍ Zainabal-Akeelah Ali



Bismihi Ta'ala

Allah ya halicci halittunsa a doron kasa a jinsi biyu (mace da namiji) wannan ka'ida ce da Allah (S) ya so ya wanzar da halittu ta hanyar ta kuma wannan ka'idar ba ta canza ba a halittar dan Adam. An halicci mace ne daga abun da aka halicci namiji, kuma daidai suke a halitta, babu fifiko a tsakanin su sai na tsoron Allah. 


 Kafin zuwan musulunci, mata sun tsinci kansu a mawuyacin hali. A wasu al'ummun an musguna musu an tauye musu hakkokinsu an maida su wani abu da ke tsakanin mutum da dabba, wato su mata ba a dauke su mutane ba. Hakan yasa suka fuskanci nau'uka na zalunci da tauye hakkoki kamar killace su a gida tamkar fursunoni, an maida su ababen mallakar maza wanda har ta kai ga ana gadonsu, wadannan abubuwan a bayyane suke a al'ummu kamar tsohuwar daular Indiya, Jahiliyyar Larabawa da sauransu. Wani nau'in zaluncin da kuma mata suka fuskanta an maida su hoto da ake amfani da su don cimma wata manufa, anan ana ba su wasu mukamai na zahiri misali; Sarauniya ta wani gari a zahiri amma a badini ba ita ba ce wasu ne ke amfana da kasantuwarta Sarauniyar. Wannan amfanuwar da ake mata ta kaima hqr aka maida su ababen bauta, kamar; yadda ya faru a Misra da Indiya. 



 Zuwan musulunci shine ya bai wa mata matsayi da 'yanci na mutumtaka wanda yayi daidai da na namiji (ya daidaita su a dan adamtaka) ba tare da nuna fifiko kamar yanda a zamanin Jahiliyya aka yi ba, an kwato musu hakkokinsu da aka tauye musu sun zama cikakkun mutane masu 'yanci.



Zamu cigaba Insha Allah......

Help to share🙏

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post