@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MARHABAN BIKA YAA KHAIRUL-BARIYYAH
Maganar Annabi (S. A. W. W) ce cewa duk wanda ya Jahilci abu zai yi adawa dashi. Amma kuma wani lokaci mafi yawa mutane na bin son zuciyarsu ce wajen qiyayyarsu ga wani abu wanda bai zo daidai da son ransu ba.
Jahilci ko son zuciya yasa wasu magabata suka cika littafai da rubuce-rubucen qarya don mumuna kalmar SHI'AH da mabiyanta. Sun qirqiro cewa wai Shi'ah ta samo asali ne daga wani mai suna Abdullahi Bn Saba'a Al-yahudiy, kuma wannan zantuka ya tasirantu sosai cikin zuciyar maqiya zuriyar Manzon Allah (S. A. W. W).
Cikin rubutunsu da zantukansu suke cewa babu SHI'AH lokacin Manzon Allah (A. A. W. W), wai bayan wafatinsa ne Ibn Saba'ah ya qirqirota.
Saboda haka yanzu za mu shiga cikin Tafsirin Imam Suyudi mai suna (DURRUL-MANSUR) don ganin abinda ya kawo qarqashin Tafsirin aya ta 7 cikin Suratul-Bayyinat.
RIWAYAR ABU HURAIRA
أخرج ابن أبي حاتم عن أبي هريرة قال: أتعجبون من منزلة الملائكة من الله؟ والذي نفسي بيده لمنزلة العبد المؤمن عند الله يوم القيامة أعظم من منزلة ملك واقرأوا إن شئتم
{إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية}.
Ibn Abiy Hateem ya fitar daga Abu-Hurairata yace, " Kuna mamaki ne game da matsayin Mala'iku a wajen Allah ? Na rantse da wanda raina ke hannunsa, matsayin Bawa mumini a wajen Allah ranar alqiyama yafi girma daga Matsayin Mala'iku . Idan ka so ka karanta,
" LALLE WADANDA SU KAYI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA, WADANNAN NE MAFI ALKHAIRIN AL'UMMAH. "
RIWAYAR A'ISHA
وأخرج ابن مردويه عن عائشة قالت: «قلت يا رسول الله: من أكرم الخلق على الله؟ قال: يا عائشة أما تقرئين {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية}».
Ibn Mardawihi ya fitar daga A'isha tace, " Nace, yaa Ma'aikin Allah ! Waye mafificin halitta a wajen Allah ?" Yace,
" Yaa A'ishatu ! Amma ba kya karanta, " LALLE WADANDA SU KAYI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA WADANNAN NE MAFI ALKHAIRIN HALITTA ? "
RIWAYAR JABIR BN ABDULLAH
وأخرج ابن عساكر عن جابر بن عبد الله قال: «كنا عند النبي صلى الله عليه وسلم فأقبل عليّ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: والذي نفسي بيده إن هذا وشيعته لهم الفائزون يوم القيامة، ونزلت {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية}»
فكان أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم إذا أقبل عليّ قالوا: جاء خير البرية.
Ibn Asakiri ya fitar daga Jabir Bn Abdullah yace,
" Mun kasance wajen Annabi (S. A. W. W) sai Aliyu ya fuskanto (yazo), sai Annabi (S. A. W. W) yace,
" NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA, LALLE WANNAN (ALi) DA 'YAN SHI'ARSA SUNE MASU RABAUTA RANAR ALQIYAMA.
Sai aka saukar,
" LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA, WADANNAN SUNE MAFI ALKHAIRIN HALITTA ."
Sahabban Annabi (S. A. W. W) sun kasance idan Aliyu ya fuskanto sai suce, " MAFI ALKHAIRIN HALITTA YA ZO !"
RIWAYAR ABI SA'ED
وأخرج ابن عدي وابن عساكر عن أبي سعيد مرفوعاً: عليّ خير البرية.
Ibn Adeey da Ibn Asaakiri sun fitar daga Abu Sa'eed (Marfuu'an) yace,
" ALIYU NE MAFI ALKHAIRIN HALITTA ."
RIWAYAR IBN ABBAS
وأخرج ابن عدي عن ابن عباس قال: «لما نزلت {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية} قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لعلي: هو أنت وشيعتك يوم القيامة راضين مرضيين».
Ibn Adeey ya fitar daga Ibn Abbas yace, yayin da aka saukar,
" LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA, WADANNAN NE MAFI ALKHAIRIN HALITTA ."
Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Aliyu,
" KAINE DA 'YAN SHI'ARKA RANAR ALQIYAMA KUKE YARDADDU ABABAN YARJEWA ."
RIWAYAR IBN ABIY 'DALIB
وأخرج ابن مردويه عن عليّ قال: قال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ألم تسمع قول الله: {إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات أولئك هم خير البرية} أنت وشيعتك وموعدي وموعدكم الحوض إذا جئت الأمم للحساب تدعون غرّاً محجلين».
Ibn Mardawihi ya fitar daga Aliyu yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace gare ni,
" ASHE BA KAJI FADIN ALLAH BA, " LALLE WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA, WADANNAN NE MAFI ALKHAIRIN HALITTA ."
" ALQAWARINA DA ALQAWARINKU SHINE TAFKI, IDAN AL'UMMU SUKA ZO DON YIN HISABI ZA A KIRA SU (ne) MASU JAJAYEN SOFANE A GURABUN SUJADAH ."
Duk wannan bayanan
mun ciro muku ne daga Durrul-Mansur na Imam Suyudi.
QALUU-BALEE
Duk wanda ya karanta wannan rubutu sai yaji abin baiyi masa dadi ba saboda bai zo daidai da abinda yake son ji ba, to, ya koma cikin littafin da muka ambata ya qara gani da idanunsa.
Idan ya qara jin rashin jin dadi cikin zuciyarsa sai ya kawo nassosin da suka soke wadannan riwayoyi, idan kuwa ba shi dashi kasu kada ya bude bakinsa don za aji warinsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08126385470)
3rd November, 2020/ 17th Rabi'ul-Awwal, 1442.