Malam Salihu Alkali Ya Kubuta Daga Hannun Masu Garukawa Da Mutane !!!


 

A ranar Talata 03/11/2020 ne Alkali Malam Salihu Muhammad na kotun Addinin Musulunci (Shari'a Court) ta garin Dan Sadau karamar hukumar mulkin Maru dake jihar Zamfara ya samu ku6uta daga hannun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan ya share sama da wata 2 a hannunsu saboda rashin biyan kudin fansa da aka yi a tsawon wannan lokaci.


Shi dai Malam Salihu an yi garkuwa da shi ne a hanyarsa ta dawowa karatu daga jamhuriyar Nijar tare da takwaran aikinsa Alkali Malam Shafi'i Ibrahim na garin jangebe ta karamar hukumar mulkin Mafara duk a jihar Zamfara, kuma 6arayin sun nemi a basu Naira Milayan Goma ne ga kowane mutum daya cikin wadannan Alkalai da suka sace a matsayin kudin fansa.


Wata majiya ta shaida muna cewa, tun a wancan lokacin gwamnatin jihar Zamfara ta shiga cikin lamarin don ganin ta ceto wadannan alkalai, amma daga karshe dai shi Malam Salihu rahotanni sun tabbatar da cewa iyalanshi ne suka hada Naira Miliyan daya suka amsoshi bayan doguwar muhawara ta ciniki da suka yi da 6arayin da suka saceshi.


Sulaiman Isma'il Rimi daya daga cikin Almajiran Malam Salihu, shine ya fara wallafa wannan labari na ku6utar da Malam Salihu yayi daga hannun wadannan 6arayi a shafinsa na Facebook, bayan iyalinshi sun biya Kudin fansa. in ji shi


Har ya zuwa hada wannan rahoto, bamu samu bayani akan Malam Shafi'i Ibrahim (dayan alkalin da aka sacesu tare da Malam Salihu) ba.


® Sharief Munauwar Mukhtar

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post