Ku Yi Koyi Da Imam Ali (A.S) Wajen Ciyarwa !!!



 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


TSINANNE NE WANDA AKA ROQE SHI DON ALLAH YA QI YA BAYAR 


Duk da cewa anfi samun wannan matsala cikin 'yan Izala, amma kuma mutane da dama na qin bada taimako don Allah. 


Abinda yasa na ambaci cewa anfi samun wannan matsala cikin 'yan Izala shine, sau da yawa akan sami masu lalura bisa kyakkyawan zato cewa matuqar sun nemi taimako wajen musulmi musamman ma a cikin masallaci yayin da suka gana da Allah yasa suke amfani da wannan dama. Sai dai matsalar da ake samu ita ce, idan mabuqaci ya miqe tsaye bayan sallah ya nemi taimako sai kaga 'yan qalilan ne suke bayarwa. 


Abinda suke kafa hujja da shi shine, wai bai bi hanyar data dace ba domin bai sanar da jagoran masallacin ba, wai hakan ya sabawa sunnah. Saboda hakane ana neman taimako ba bisa izninsu ba sai suji kamar an sanya musu ciwo ne. 


To, ku saurara kuji abinda Annabi (S. A. W. W) ke cewa kan hana mabuqaci yayin da ya nemi taimako don Allah. 


عن أبي عُبيدةَ مولى رفاعة عن رافع؛ أن رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قال:

"ملعونٌ من سألَ بوجهِ اللهِ، وملعونٌ من سُئلَ بوجهِ اللهِ فمنعَ سائلَهُ".

رواه الطبراني.


An karbo daga baban Ubaidata bararren bawan Rafa'ata, daga Rafi'u cewa, Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" TSINANNE NE (duk) WANDA AKA ROQE SHI DON ALLAH, KUMA TSINANNE NE (duk) WANDA AKA ROQE SHI DON ALLAH SANNAN YA HANA WANDA YA ROQE SHI (alhali yana da abin bayarwa) ."


           ABIN LURA 


Wannan hadisi ba yana magana kan hana maroqan da suka maida roqo sana'a bane, a'a, yana magana ne kan wadanda buqatar neman taimako ne ya taso musu. 


IMAM ALI (A. S) YA SAMI YABO 


Aya ce musamman ta sauko don yabonsa inda Allah ke cewa cikin 


                  سورة الإنسان 


بسم اللَّهِ الرحمن الرحيم.



           قوله تعالى 



 {وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَى حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا (8) إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزَاءً وَلَا شُكُورًا (9) إ


" KUMA SUNA CIYAR DA ABINCI BISA SONSA GA MISKINI DA MARAYA DA RIBATACCE . (Suna cewa) ABIN SANI MUNA CIYAR DA KU NE DON NEMAN YARDAR ALLAH, BAMU NUFIN (samun) SAKAMAKO DAGA GARE KU KO KUMA GODIYA ."


             

 قال عطاء عن ابن عباس: وذلك أن علي بن أبي طالب رضي الله عنه نوبة أجر نفسه يسقي نخلاً بشيء من شعير ليلة حتى أصبح وقبض الشعير وطحن ثلثه فجعلوا منه شيئاً ليأكلوا يقال له الخزيرة فلما تم إنضاجه أتى مسكين فأخرجوا إليه الطعام ثم عمل الثلث الثاني فلما تم إنضاجه أتى يتيم فسأل فأطعموه ثم عمل الثلث الباقي فلما تم إنضاجه أتى أسير من المشركين فأطعموه وطووا يومهم ذلك فأنزلت فيه هذه الآية.



Adda'u yace, (ya samo) daga Ibn Abbas (R. A) yace, 


" Aliyu ya nemawa kansa wani aiki na shayar da Dabino da daddare don a bashi lada da Sha'ir, da gari ya waye sai ya karbi wannan Sha'ir. Ya cire daya -bisa -ukunsa yayi wani abu don yaci ana ce masa GURASA. 


Yayin da ya sarrafa shi sai ga wani miskini ya zo masa, sai ya fito masa da wannan abinci (ya hanawa kansa). 


Sai ya dau kaso daya na biyu daga cikin kaso ukun ya qasa sarrafawa. Yayin da ya gama sarrafa shi sai ga wani maraya yazo ya roqe shi, sai ya ciyar da shi. Sannan ya qara daukar kaso daya (1) na qarshe don sarrafawa, yayin da ya gama sarrafa shi sai ga wani ribatacce daga Mushirikai yazo, sai ya ciyar da shi ya wuni cikinsa babu komai. 

Sai aka saukar da wannan aya a kansa. "


Wannan ba qaramar falala bace ga mutum ace ya aikata kyakkyawan aiki har aka saukar da ayar yabo gare shi. Madallah da wannan yabo daga Allah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         081379250 34


11th November, 2020/ 25th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post