Rbtw: J. I. R
Nan dai Ahmad ya ce, Allah ya kaimu", nan take Zainab ta ce Amin sweetheart. Ya koma gida, ya bar Zainab cikin kewa, ji take kamar kar ta tafi, shima Ahmad ya kuma cikin rashin jin dadi domin kuwa zai yi kewan kyakkyawan fuskar Zainab mai cike da murmushi.
A wayi garin Lahadi, Ahmad da safe ya shirya ya Kira abokinsa Nura don ya rakasa, su yi ban kwana da muradinsa Zainab. Nura ya zo ya same shi, suka tafi ba tare da sun bata lokaciba, saboda Zainab ta ce da safe zata tafi. Su ka isa gidan su Zainab, su samu ta gama shirya komai, tafiya kawai zata yi.
Ahmad, duk ya canza, saboda da bai son Zainab ta yi kusa da shi, da Nura ya fahimci Ahmad ya shiga kewa tun kafin yaga tafiyar Zainab, sai ya fara rar-rashinsa yana cewa, "Ahmad ka kwantar da hankalinka mana, Zainab fa taka ce, kuma ma meye na damuwa?, ba mutuwa zataiba, tafiya ba mutuwa ba ne. Nasan kwanakin ma da ta Fadi zai yi wuya ta yi, ka kwantar da hankalinka". Haka dai Nura yayi ta basa hakuri da kalmomi masu kwantar da zuciya. Ita ko Zainab ta yi shuru, ta kasa cewa komai, domin itama ta damu kamar wani wanda in ta tafi ba zata dawoba.
Ahmad ya matsa kusa da Masoyiyarsa, ya kalleta ya ce, "Farin cikina, na baki amanar kaina ki kula min da kanki, domin Zaki tafi kibarni cikin tunani mai tsanani, domin na shaku dake fiye da yadda ake zato, ki riken amana Zainab!". Cikin sanyin murya Zainab ta ce, "Kar kadamu zan kula da kaina, nima ka kulamin da kanka. Ni taka ce, amanar dake tsakaninmu ba shakka zan riketa, nasan da rabuwa ba mutuwa ba ne, amma masoya irinmu wadanda mu shaku, tana da ciwo tare da kewa mai tsanani, amma kar ka damu zan dawo gareka cikin lokaci. Ai ma zamu ke waya akai-akai". Ahmad ya ce, "To shikenan mu je na raka ki ki hau mota", ya dauki jakanta, su rakata har ta shiga mota. Su yi ban kwana.
Zainab ta sauka a garin kakaninta, ta tarar da ana shiri fara musu aikin hanya (kwalta). Haka nan dai ta karisa.
Tana isa gidan kakanta, cikin farin ciki, da kewa kakanta Hadiza ta yi wuf ta zo ta rungumeta tana cewa, "Allah sarki Zainabu na ke ce a garin namu, sannu-sannu" Hadiza ta kaita daki ta kawo mata ruwa, ta je ta kawo mata abinci.
Su zauna, Zainab ta ce, "Kaka ai na zo zan dan kwana biyu ne", sai Hadiza ta ce, "Kai amma amma na ji dadi, ya su Mariya, fatan kowa suna lafiya. Su Al amin", Zainab ta ce, "Kowa lafiya lau, suna gaisheki kaka".
Mu hadu a kashi na gaba, don jin ya rayuwar Zainab zai kasance a kauye, sannan ya Ahmad zai tsinci kansa bayan tafiyar Zainab.