Rbtw:J. I. R
Haka soyayyarsu ta ci gaba da tafiya lami-lafiya, ba tare da wani abu ba. Ahmad ya muhimmantar da soyayyarsu fiye da yanda ake tsammani,har ya kai da Ahmad ya zama wannan abun da ake kira "Dan kwali,ya ja hula", domin har school shi yake rakata wata rana; wata rana kuma ya je ya daukota. Suna tafiya suna shan soyayya abun sha'awa.
Akwai wata rana da Ahmad ya kira Zainab tana school,akan yana son ganinta,yana mai cewa, "Masoyiyata na zam mai nasara, a sannu-sannu kin bani ruwan zuman kauna. Haqiqa soyayya ta zamo min abun alfahri. Kina ina hasken idanuwata? ina son ganinki". Zainab ta ce, "Masoyina kuma farin-ciki na, ina school.Ni zan baka labari, don kuwa soyayyarka ita ce rabo mafi girma da na samu a rayuwa,ina alfahri dakai jigon rayuwa". Ahmad ya ce, "Lallai kam,ra'ayinmu ya zam daya,ina tabbatar miki ba zan baki kunyaba, kece zabi na daya tal. Allah ya barmu tare Saurauniyata, yanzu dai kar na ja ki da surutu in kun gama lecture na zo na dauke ki a mashin dina,na kaiki gida don ban son ki wahala min". Zainab ta ce, "Uhmm. Qalbi na, kamar ka sani dazu mu fito daga last lecture, yanzu kazo Main gate". Ahmad ya tafi ya je ya dauko muradinsa,ya kai ta har gida. Su yi sallama ya koma gida.
Bayan ya koma gida,ya huta.Se ya nema ummansa don ya bata labari,cewa ya samu macen da yake so da aure. Ya baiwa ummansa labari yana cewa, "Umma haqiqa zan miki albishir da cewa na sama miki sarkuwa tagari sunanta: Zainab". Ummansa budan bakinta ta ce, "Lahh! ashe Ahmad zan ji wannan labarin mai dadin ji, Allah ya nuna mana,ya kaimu lokaci mu sha biki". Ahmad cikin farin ciki ya ce, "Amin ummah nah".
Sun ci gaba da soyayyarsu ba tare da ko matsalaba. Ta sake mishi, shima haka. Ya kan kasance cikin ambatonta a ko da yaushe gaban abokanansa, su Nura, haka nan itama Zainab ta yawan ambatonsa gaban kawayenta, su Fatima.
Wata rana, ya tafi zance gun Zainab. Bayan da ya isa gidan su Zainab ya dau lokaci suna hira, take cewa, "My wallahi kamar kar ka tafi kamarni, jinina da naka sun hadu sun zam daya, ka kara rike amanar zuciyata har mu wayi ranar da zan mallakeka a matsayin Angona", Ahmad yayi dariya ya ce, "Ni ai na zama naki tun-tuni, abun da nake bukata gareki kara bani kulawa iya iyawarki, ina tabbatar miki da dani dake in sha Allah mutuwa zata raba", Zainab cikin murmushi ta ce, "Ko mutuwar ce ma, na fison mu tafi tare, saboda rayuwa ta bayanka, tamkar miya ce ba mahadinta, ba zan ji dadin rayuwa in ba dakaiba My favorite baby", Ahmad ya ce, "To mu ta addu'a Allah ya cika mana burinmu, kuma mu kula da amanar junanmu, tare da bai wa juna kulawa mai cike da gata".
Su ka ta yi hiransu, karshe sai Zainab take cewa, "Kasan meye My nice dream? Zan tafi ziyara can kauyen su mama, kuma in naje zan dade, domin zai kai kusan wata daya", Ahmad budan bakinsa sai ya ce, "Haba Zainab yanzu har wata, zan yi ban ga kyakkyawan fuskarki kiba, mai cike da haske dake haskaka qalbina, gaskiya ni ban so ki yi nesa da ni, kema kin san hakan zai sakani a kunci, ina son ki, ban son ki yi nesa da dani Zainab", Zainab ta ce, "Ka yi hakuri, mama ce ta takura sai na je, wai na dade ban jeba. Amma karka damu ba zan yi watan ba, zan yi kokari na yi sati biyu na gudo, nasan mun shaku dakai sosai, wanda rashin shakar numfashinmu kusa, zai kawo kewa, da yawan tunani a zukatanmu, mu yi hakuri zamu ke gaisawa ai ta waya", nan dai Ahmad ya hakura, ya ce, "Yau she zaki tafi", Zainab ta ce, "Jibi Lahadi l. In Allah ya kaimu, da safe". Ahmad ya ce, "Allah ya kaimu".
Mu hadu. A ci gaban wanan labarin, don jin ya tafiyar Zainab za ta kasance.