Kina So Mijinki Ya Riqa Ambatonki Gaban Kishiyarki Ko Da Bayan Ranki Ne???


 KINA SO MIJINKI YA RIQA AMBATONKI GABAN KISHIYARKI KO DA BAYAN RANKI NE ???


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KIYI KOYI DA NANA KHADIJAH (S. A) CIKIN ZAMANTAKEWAR AURENKU 



Zamantakewar Nana Khadijah (S. A) tare da Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance samfuri abin koyi ga duk mata muminai. 


Tausayi, girmamawa, ganin mutunci, riqe sirri, da taimako wanda Nana Khadijah (S. A) ta yiwa Annabi (S. A. W. W) ba zai iya misaltuwa ko kwatantuwa ta hanyar rubutu ko furuci ba, sai dai kawai ya zama duk abinda za a fada bai wuce ishara ba. 


Idan biyayya da riqon amana wani sirri ne na mallakar miji, to, Nana Khadijah tayi dacen samun wannan sirri wanda tayi amfani dashi har sonta ya mamaye zuciyar Manzon Allah (S. A. W. W), kuma ambatonta ya tabbata kan harshen fiyayyen halitta Muhammad (S. A. W. W). 


Adalci ne idan mutum ya aikata kyakkwaya ya zama an iya taskace shi a kundin tarihi wanda ambatonsa ba zai taba gushewa ba a tarihin duniya .


Ambaton Sayyidah Khadijah (S. A) ya wanzu kan harshen Manzon Allah (S. A. W. W) har bayan ranta, wanda hakan ya zama abin baqin ciki wajen Ummul-muminina A'isha, alhali ba abin baqin ciki bane illah ya zama anyi qoqarin sanin menene sirrin wannan al'amari don ayi koyi da shi. 


Ya zo cikin Riyadus-Saliheen qarqashin Babin da ke magana kan falalar yin biyayya ga abokan iyaye , wanda Ummul-muminina A'isha ta bada labari kamar haka; 


باب فضل بر أصدقاء الأب


حديث رقم :343


وعن عائشة رضي الله عنها قَالَتْ: 


مَا غِرْتُ عَلَى أحَدٍ مِنْ نِسَاءِ النَّبيِّ صلى الله عليه وسلم مَا غِرْتُ عَلَى خَدِيجَة رضي الله عنها، وَمَا رَأيْتُهَا قَطُّ، وَلَكِنْ كَانَ يُكْثِرُ ذِكْرَهَا، وَرُبَّمَا ذَبَحَ الشَّاةَ، ثُمَّ يقَطِّعُهَا أعْضَاء، ثُمَّ يَبْعثُهَا في صَدَائِقِ خَديجَةَ، فَرُبَّمَا قُلْتُ لَهُ: كَأنْ لَمْ يَكُنْ في الدُّنْيَا إلاَّ خَديجَةَ ‍!فَيَقُولُ: (إنَّهَا كَانَتْ، وَكَانَتْ، وَكَانَ لي مِنْهَا وَلَدٌ) مُتَّفَقٌ عَلَيهِ. وفي رواية: وإنْ كَانَ لَيَذْبَحُ الشَّاءَ، فَيُهْدِي في خَلاَئِلِهَا (1)، مِنْهَا مَا يَسَعُهُنَّ. وفي رواية: كَانَ إِذَا ذبح الشاة، يقولُ: (أَرْسِلُوا بِهَا إِلَى أصْدِقَاءِ خَديجَةَ). وفي رواية: قَالَت: اسْتَأذَنتْ هَالَةُ بِنْتُ خُوَيْلِد أُخْتُ خَدِيجَةَ عَلَى رَسُول الله صلى الله عليه وسلم، فَعرَفَ اسْتِئذَانَ خَديجَةَ، فَارتَاحَ لِذَلِكَ، فَقَالَ: (اللَّهُمَّ هَالةُ بِنْتُ خُوَيْلِدٍ).قولُهَا : (فَارتَاحَ) هُوَ بالحاء، وفي الجمعِ بَيْنَ الصحيحين للحُميدِي، (فارتاع) بالعينِ ومعناه: اهتم بهِ.ـــــــــــــــــــــ(1) خَلاَئِلِهَا : أي صدائقها. دليل الفالحين 3/252.



Daga A'ishatu (R. A) tace, 


" BAN TABA YIN KISHI KAN 'DAYA DAGA CIKIN MATAN ANNABI (S. A. W. W) BA, (amma) NAYI KISHI KAN KHADIJAH (R. A). KO DA SAU 'DAYA BAN TABA GANINTA (a zahiri) BA, SAI DAI (kawai Annabi) YANA YAWAN AMBATONTA. SAU DA YAWA IDAN YA YANKA AKUYA YAKAN GUTSUTTSURATA (part-part) , SA'AN NAN YA AIKA SHI ZUWA GA QAWAYEN KHADIJAH (don tunawa da ita). 


NI (A'ishatu) KUWA SAU DA YAWA NAKAN CE MASA : " KAMAR DAI BA A TABA YIN WATA (mata) A DUNIYA BA SAI KHADIJAH !" SHI KUWA YACE MIN; " AI ITA (Khadijah) TA KASANCE, KUMA TA KASANCE, KUMA (duk tsarkakakkun) 'YA'YAYENA DAGA GARE TA SUKE. "


Anyi ittifaqi kan wannan hadisi.


 A wata riwayar kuma : " IDAN YA YANKA AKUYA YA KANYI KYAUTARSA CIKIN QAWAYENTA DAGA ABINDA ZAI WADATAR DASU. 


A wata riwayar kuma, ya kasance idan ya yanka akuya yakan ce, " KU AIKA SHI ZUWA GA QAWAYEN KHADIJAH ."


A wata riwayar tace, " Haalatu Bnt Khuwailid 'yar'uwar Khadijah ta nemi izni a wajen Manzon Allah (S. A. W. W) sai ya gane (irin neman) iznin da Khadijah ta saba yi masa ne, sai ya zabura game da hakan, sai yace :


" YAA UBANGIJI ! HALATU BNT KHUWAILID CE FA !"


...............................................


Wannan shine abin fahari ga mace ace ta aikata kyakkyawan aiki wanda mijinta zai riqa ambaton sunanta ko da a bayan ranta ne .


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


10th November, 2020/ 24th Rabi'ul-Awwal,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post