@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KU ISAR ABINDA KUKA JI KAMAR YADDA KUKA JI SHI
Babban cin amanar farko da aka yiwa Annabi (S. A. W. W) shine lullube dukkan wata gaskiya da aka ji daga bakinsa don cimma wata manufa ta qashin kai.
89% na daga abinda aka ji daga gare shi a lullube ko an canza shi zuwa wata siffa me dauke da mummunar manufa, wanda hakan yayi sanadin fadawa cikin musifa da bala'i.
Allah (T) na cewa,
" KUMA KADA KU LULLUBE GASKIYA DA BATA, KUMA KU BOYE GASKIYA ALHALI KUNA SANE. "
Yazo cikin littafi mai suna (SAHIHUL-JAMI'USSAGEER) a babin da ke cewa,
(الترغيب في سماع الحديث وتبليغه ونسخه، والترهيب من الكذب على رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -).
KWADAITARWA GAME DA JIN ZANCE DA KUMA ISAR DA SHI DA TASKAKE SHI, DA KUMA TSORATARWA GAME DA YIWA ANNABI (S. A. W. W) QARYA
89 - (1) [حسن صحيح] عن ابن مسعودٍ رضي الله عنه قال: سمعتُ رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - يقول:
"نضَّر الله امرأً سمع منا شيئاً فبلّغه كما سمعه، فَرُبَّ مُبلَّغٍ أوْعى من سامعٍ".
Daga Ibn Mas'ud (R. A) yace, na ji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa;
" ALLAH NA QAUNAR WANDA YAJI WANI ABU DAGA GARE MU KUMA YA ISAR DA SHI KAMAR YADDA YA JI SHI, (domin) DA YAWA WADANDA AKA ISAR MUSU SUN FI KIYAYEWA FIYE DA WADANDA SUKA JI ."
رَواه أبو داود (1) والترمذي، وابن حبان في "صحيحه"، إلا أنه قال:
"رَحِمَ الله امرأً".
Abu Dawud da Tirmidhi da Ibn Hibban sun riwaito cikin sahihinsa (wannan hadisi), sai dai cewa yace, " ALLAH YAYI RAHMA GA MUTUMIN DA. "
A wata riwayar kuma ,
90 - (2) [صحيح] وعن زيد بن ثابت قال: سمعت رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - يقول:
"نضّر الله امرأً سمع منا حديثاً فبلّغه غيرَه، فربَّ حاملِ فقهٍ إلى من هو أفقهُ منهُ، وربَّ حاملِ فقهٍ ليس بفقيه،
ثلاث لا يَغِلُّ (2) عليهن قلبُ مسلمٍ: إخلاصُ العملِ لله، ومناصحةُ ولاةِ الأمرِ، ولزومُ الجماعة؛ فإن دعوتَهم تُحيط مَنْ وراءَهم. ومن كانت الدنيا نِيَّتَه؛ فرَّقَ الله عليه أمرَه، وجعل فقرَه بين
Daga Zaid Bn Thaabit yace, na ji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa,
" ALLAH NA QAUNAR MUTUMIN DA YA JI WANI ZANCE DAGA GARE MU KUMA YA ISARWA WANINSA (wanda bai ji ba), DA YAWA WANDA KE 'DAUKAR ILIMI ZUWA WAJEN WANDA YA FI SHI ILIMI (yakan qaru da wani abu daga gare shi), DA YAWA WANDA KE 'DAUKAR ILIMI BAI KASANCE MAI ILIMI BA (har sai yayi aiki da shi) .
MUTANE UKU ZUKATAN MUSULMI BA ZA SU JI WANI QULLI DA SU BA.
(1)- (mai) TSARKAKE AIKI DOMIN ALLAH,
(2)- (Da) MAI KYAUTATA WILAYAR AL'AMARINSA (a inda ya dace),
(3)- (Da) MAI LAZIMTAR JAMA'A.
DOMIN (su jinsin mutane ukun nan) DA'AWARSU (iri daya ce, kuma) TANA KEWAYE WADANDA KE BAYANSU. DUK WANDA KUMA DUNIYA ITA CE NIYYARSA, SAI ALLAH YA YANKE AL'AMARINSA A KANSA, KUMA YA SANYA TALAUCI A TSAKANIN IDANUWANSA ."
Saboda haka mu kasance masu isar da gaskiyar abinda muke ji daga bakunan malumanmu da kuma haqiqanin abinda yazo daga Manzon Allah (S. A. W. W), yin hakan shine adalci kuma mafi tsarki gare mu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470-08137925034)
23rd November 2020/ 8th Rabi'us-Sani, 1442.