Kada Ka Fifita Abinda Ke Qarewa Kan Tabbatacce, Domin Duniya Ba Gida Ne Na Tabbatuwa Ba !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Mafi girman abinda ke rudin mutane har su fifita duniyarsu kan lahirarsu shine Mulki da dukiya da mata da kuma 'ya'ya. 


Duk wadannan abubuwa ni'ima ce wacce Allah ke bayar da ita ga sashen bayinsa a matsayin jarrabawa daga cikin jarrabawowin da ake jarraba bayi. Ita ni'ima ba ta dawwama, domin komai dadewarka cikinta akwai lokacin da za ka rabu da ita. 


Allah (T) ya zargi duniya a gurare da dama don ya zama gargadi gare mu kamar yadda za mu gani cikin ayoyin dake tafe :-


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



     (SURATUL-YUNUS) 



إِنَّمَا مَثَلُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ مِمَّا يَأۡكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلۡأَنۡعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلۡأَرۡضُ زُخۡرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتۡ وَظَنَّ أَهۡلُهَآ أَنَّهُمۡ قَٰدِرُونَ عَلَيۡهَآ أَتَىٰهَآ أَمۡرُنَا لَيۡلًا أَوۡ نَهَارٗا فَجَعَلۡنَٰهَا حَصِيدٗا كَأَن لَّمۡ تَغۡنَ بِٱلۡأَمۡسِۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ ٤٢


" ABIN SANI MISALIN RAYUWAR DUNIYA KAMAR RUWA NE DA AKA SAUKAR DASHI DAGA SAMA, SAI TSIRRAN DAKE QASA SUKA GAURAYA DASHI NA DAGA ABINDA MUTANE KE CI DA KUMA DABBOBI, HAR IDAN QASA TA 'DAUKI KAYAN ADO (na tsire-tsire) TA QAWATU KUMA MASU ITA SUKA ZACI CEWA SU MASU IKO NE A KANTA SAI AL'AMARINMU (na jarrabawa) YAJE MATA CIKIN DARE KO YINI, SAI MU SANYA TA GIRBABBIYA TAMKAR DAI JIYA BATA WADATU (da ruwa) BA. KAMAR HAKA MUKE RARRABE AYOYI GA MUTANE MASU YIN TUNANI ."



        ( SURATUL-KHAHFI) 


وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ فَأَصۡبَحَ هَشِيمٗا تَذۡرُوهُ ٱلرِّيَٰحُۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقۡتَدِرًا ٥٤


(Yaa Muhammad) " KA BUGA MUSU MISALIN RAYUWAR DUNIYA KAMAR RUWA NE DA MUKA SAUKAR DASHI DAGA SAMA SAI TSIRRAN (dake) QASA SUKA GAURAYA DA SHI, SAI (wani lokaci) YA WAYI GARI A QEQASHE (ya bushe) ISKA NA YIN FATALI DASHI. ALLAH YA KASANCE MAI IKO NE KAN KOMAI ."



     (SURATUL-AL'IMRAAN) 



زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ ٤١


" AN QAWATAWA MUTANE SON SHA'AWA DAGA MATA DA 'YA'YA DA DUKIYOYI ABABEN TARAWA DAGA ZINARIYA DA AZURFA, DA DAWAKI KIWATATTU DA DABBOBI (na ci) DA HATSI. WADANNAN SUNE DADIN RAYUWAR DUNIYA . KUMA A WAJEN ALLAH KYAKKYAWAR MAKOMA TAKE ."

      

(SURATUL-HADEED) 


ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞ وَزِينَةٞ وَتَفَاخُرُۢ بَيۡنَكُمۡ وَتَكَاثُرٞ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِۖ كَمَثَلِ غَيۡثٍ أَعۡجَبَ ٱلۡكُفَّارَ نَبَاتُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَكُونُ حُطَٰمٗاۖ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٞ شَدِيدٞ وَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٞۚ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ ٠٢


" KU SANI CEWA ITA RAYUWAR DUNIYA WASA CE DA WARGI DA ADO DA ALFAHARI A TSAKANINKU DA GASAR WADATA CIKIN DUKIYA DA 'YA'YA, KAMAR MISALIN SHUKA NE WANDA YABANYARSA TA BADA SHA'AWA GA MANOMA, SA'AN NAN TA QEQASHE KA GANTA FATSI-FATSI (yellow) SA'AN NAN TA KOMA (abincin wuta ) BUSHASSHIYA. KUMA A LAHIRA AKWAI AZABA MAI RADADI (ga wanda duniya ta rudar dashi) DA KUMA GAFARA DAGA ALLAH DA YARDARSA (ga wanda duniyar bata rude shi ba). KUMA RAYUWAR DUNIYA BATA ZAMA BA FACE 'DAN WANI JIN DADI NA RUDI KAWAI ."


Wadannan misalan ayoyi kadai sun zama wa'azi ga mai hankali da tunani yasan cewa ita duniya ba komai bane. Kamar dai yadda muka shiga damina (rainy season) ne yanzu muka fito kaka, kuma nan gaba kadan za muga gonakinmu tamkar ma bamu taba yin noma cikinsu ba, domin za ta qeqashe shanu su cinye sauran abinda ya rage na daga busasshun ciyarwa da karmami. 


Jiya wasu muka gani akan mulki, wasu kuma da dukiya, amma yanzu sun zama abin tarihi, babu su ku kuma abinda suke gadara dasu sun gushe. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


9th November, 2020/ 23rd Rabi'ul-Awwal, 1442.


        (08126385470)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post