Jinsin Mutane Uku Da Ya Kamata A tausaya Masu !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Duk wata halitta ta Allah (T) ana son a tausaya mata ko da kuwa dabba ce wacce aka halatta mana cin naman su, ballantana ran dan Adam wacce ta fi komai girma. 


Cikin jinsin mutane akwai wadanda kan fada cikin wani yanayi mai tutuqar wahala wacce suke buqatar a tausaya musu , kuma tausaya musu bin umarnin Manzo (S. A. W. W) ne. 


Ya zo cikin riwaya kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 عَنِ ابْنِ صَدَقَةَ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ النَّبِيُّ ص‏ ارْحَمُوا عَزِيزاً ذَلَّ وَ غَنِيّاً افْتَقَرَ وَ عَالِماً ضَاعَ فِي زَمَانِ جُهَّالٍ‏[3].



(2) أمالي الصدوق ص 8.


Daga Ibn Sadaqata, daga Sadiq, daga iyayensa (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" KU TAUSAYAWA MADAUKAKIN DA YA QASQANTA ,


DA MAWADACIN DA YA TALAUCE, 


DA MALAMIN DA YA SAMI KANSA CIKIN ZAMANIN JAHILAI ."



NB:-


(1)- Akwai wadanda suka sami daukaka a doron qasa har ta kai suke ganin kansu tamkar babu wanda ke sama dasu a iko, amma daga baya su qasqanta zu zama tamkar ma ba a taba yinsu a doron qasa ba, kamar yadda Buhari zai kasance nan ba da jimawa ba Insha Allah. 


(2)- Duk wanda ya taso kuma ya rayu cikin wadata ya girma cikinta ba tare da ya san wahala ba, to, yayin da aka ce ya fada cikin jarrabawar talauci zai fi kowa damuwa da rikicewa, saboda haka yana buqatar a tausaya masa. 


(3)- Shi kuwa malamin da ya taso cikin jahilai yakan sha wahalar gwagwarmayar da zai yi fama da ita da jama'a, domin jahilcinsu zai sa su jahilce yadda duk gaskiyar da zai bayyana musu ba za su fahince shi ba sakamakon jahilcin da suka nutse cikinsa. Sayyid Zakzaky (H) babban abin misali ne a wannan zamani yadda yake fama da jama'ah, saboda haka ya kamata a tausaya masa bisa wannan girman aiki dake gabansa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


              (08137925034)


24th November, 2020/ 9th Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post