Iran: Da Sannu Zamu Zakulo Duk Masu Hannu A Kisan Wannan Babban Gwarzon Namu. — Inji Sayyid Ibrahim Raeisi



Nasir Isah Ali

-

Shugaban sashin shari'a na kasar Iran, sayyid Ibrahim Raeesi ya bayyana wa manema labarai a birnin Tehran cewar, jami'an tsaron Iran sun killace ko'ina kuma sun watsa komarsu suna farautar wadanda suka kashe masanin kimmiyar nan na kasar Mohsen Fakhrizadeh-Mahavadi,kuma da yardar Allah za'a kamosu baki daya,kuma zasu fuskanci shari'a domin girbar abinda suka shuka inji sayyid Raeesi.

Ya bayyana cewar hukumar leken asirin kasar da bangarorin tsaro da kuma jami'an tsaron ma'aikatar shari'a suna aiki tukuru domin gano makasan nasa, da su da iyayen gidansu,kuma da yardar Allah za'a kamosu.

Ya bayyana cewar,tun ba yau ba makiya cigaban jumhuriyar musulunci suke jin haushin nasarorin da Iran take samu ta fuskar kimmiya da fasaha,don haka ne suka kulla yaki da wannan cigaban. Kuma a zatonsu shine kashe masanan mu na wannan fannin zai lahanta wannan nasarar,amma kuma karya suke yi.

Sun tattara gungun yan ta'addansu na ciki da wajen kasar domin karkashe duk wani masani a wannan fannin domin gurgunta cigaban da ake samu,amma da yardar Allah ba zasu taba yin nasara ba.

-

Da yardar Allah nan ba da jimawa ba zamu zakulo kwamandojin wadannan yan ta'addan da su da wadanda suka tsara kisan,da kuma wadanda suka aiwatar da shi domin fuskantar shari'a.

Shi dai Injiniya Mohsen Fakhrizadeh-Mahavadi da farko an harba wa motarsa wasu abubuwa masu kara da turnuke wuri,sannan aka biyo shi da harbi babu kakkautawa daga bangarori da dama a yankin Damavand dake bayan birnin Tehran.Kuma an samu nasarar kai shi asibiti inda a karshe yayi shahada a can din sakamakon muggan raununkan da ya samu a jikinsa.

-------

NIA

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post