@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TARON DANGI DON KARE MARTABAR MANZON ALLAH (S. A. W. W)
Allah (T) na kishin Annabinsa (S. A. W. W) fiye da yadda namiji ke kishin matarsa, kuma ya kanyi taron dangi wajen daukar masa fansa kan dukkan wanda ya zalunce shi ko kuma yaci mutumcinsa.
Cikin dukkan yaqoqin da Annabi (S. A. W. W) yakan sami taimakon mahalicinsa wajen ba shi kariya da kuma dauka mataki ta kowacce fuska, musamman yadda yake turo Mala'iku ko iska don tarwatsa kafirai.
Don kada ya zama wani abin mamaki ga mazaje dangane da makircin mata ko cutarwarsu ga mazajensu Allah ya bamu labarin irin abinda matan Annabi (S. A. W. W) su kayi masa don cin zarafinsa, har ma ya gargade su cewa matuqar sun hada kansu don cutar dashi, to, za muga taron dangi daga gare Shi (T) don daukar masa fansa.
Anyi qoqarin kawar da haqiqanin wanda Allah ya shigar da shi cikin jerin Mala'iku masu taimakon Manzonsa (S. A. W. W), amma duk da haka Annabi (S. A. W. W) ya bayyanar mana dashi.
Ya zo cikin Tafsir (DURRUL-MANSUR) na Imam Suyudi qarqashin ayar da ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إِنْ تَتُوبَا إِلَى اللَّهِ فَقَدْ صَغَتْ قُلُوبُكُمَا وَإِنْ تَظَاهَرَا عَلَيْهِ فَإِنَّ اللَّهَ هُوَ مَوْلَاهُ وَجِبْرِيلُ وَصَالِحُ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمَلَائِكَةُ بَعْدَ ذَلِكَ ظَهِيرٌ (4)} ﴾
۞۞۞۞۞
" IDAN KUKA TUBA (daga wannan mummunan aiki naku na qoqarin cutar da Annabi), TO, ZUKATANKU SUN KUBUTA. AMMA KUMA IDAN KUKA HADA QARFI (wajen cutar da shi ku sani) ALLAH NE MAJIBINCINSA DA JIBRILU DA KUMA SALIHIN MUMINAI, KUMA BAYAN HAKA (tarin) MALA'IKU MA MATAIMAKA NE (gare shi) !"
Annabi (S. A. W. W) yayi bayani kan wanene wannan salihin muminai wanda Allah yayi magana a kansa.
Ku biyo mu cikin wadannan riwayoyi don gani da idonku.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وأخرج ابن أبي حاتم بسند ضعيف عن عليّ قال: «قال رسول الله صلى الله عليه وسلم في قوله: {وصالح المؤمنين} قال: هو عليّ بن أبي طالب».
Ibn Abiy Haateem ya fitar da (hadisi) da rarrauna isnadi zuwa ga Aliyu yace,
Manzon Allah (S. A. W. W) ya fada cikin fadinsa (T) " DA SALIHIN MUMINAI ." Yace,
" Shine Aliyu Bn Abiy 'Dalib ."
Ance wannan riwaya ta sama akai rauni cikinta, wataqila ko cikin Rijal na hadisin ne ke da matsala. Amma ga wasu riwayoyi nan biye damu.
ASMA'U BNT UMAIS
وأخرج ابن مردويه عن أسماء بنت عميس: «سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: {وصالح المؤمنين} قال: عليّ بن أبي طالب».
Ibn Mardawihi ya fitar daga Asma'u Bnt Umais (tace), " Na ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa; " KUMA DA SALIHIN MUMINAI ." Yace,
" ALIYU BN ABIY 'DALIB NE ."
IBN ABBAS (R. A)
وأخرج ابن مردويه وابن عساكر عن ابن عباس في قوله: {وصالح المؤمنين} قال: هو عليّ بن أبي طالب.
Ibn Mardawihi da Ibn Asakiri sun fitar daga Ibn Abbas (R. A) cikin Fadinsa (S. W. A), " DA KUMA SALIHIN MUMINAI ." Yace,
" SHINE ALIYU BN ABIY 'DALIB ."
Madallah da wannan salihin muminai wanda ke tarayya da Allah da Mala'ikunsa wajen taimakon Manzon Allah (S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th November, 2020/ 22nd Rabi'ul-Awwal, 1442.