Idan mutum Ya Na Son Ya Gwada Ma Na Shi Mutumin Kirki ne, To Ya Taimaki Al'ummah--Sheikh Ibraheem El-zakzay (H)


 

Daga:Aljawad Jibrin Mahmud Kagara 


Idan mutum yana son ya gwada mana shi mutumin kirki ne, toya taimaki Al'ummah, ba ya zo, da Bindiga ya kashe mutane ba.


Ya gwada aikin da suka yiwa Al'umma,

Me suka yiwa Al'umma 'Din nan?

Idan da sun yiwa al'ummah abin kirki ba za suji tsoron komai ba.

Awa insu gurare Shugaban KASA na tu'ka mota, sosai ya tu'ka ya shiga gari kuma ya gaisa da mutane.


Naga wani a Television ne, Wani shugaba yana tafiya yana ri'ke da Jikansa yana cewa "Kaga nan lo'kacin da akai Ya'kii duk an Lalata daga bayane aka gyaggyara" Sai yaron yace Kakaa menene ya'kii? Sai yace "In 'dan Ma'kiyin ka, baya Sonka sai ya kawo maka hari" Suna tafiya da 'Kafa Aaa! Mr Primeminister yauwa barka ya akai lafiya lafiya yana wuce wa.


 Inda ya cucesu ai ba zasu barshi ya wuce lafiya lau ba.

In dagaske ne, wadannan da ka za6e su da Gagarumin Rinjayee Suzoo su 'dan Wataya mana agariii, 

Su shiga 'dan Lunguu su gaisa da mutanen da suka za6e su.


Sai kaga kullum su kenan tunanin wa zasu kashee!

Toba Jarumta bane, wannan, Mune Jaruman wannan Al'ummah!

Wanda ku kunason ku kashe mu, mu kuma muna son, mu Cecekuu!

Ku kunason ku rusa Jikkunan mu, mu munaso mu Cecii Rayukan kuu!


Mu ceton Al'umma ya dame mu, ina ta dosa a cecesu a Kyautata Duniyar su, da lahirar su.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post