@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
ANA MAGANA DA KOWA GWARGWADON HANKALINSA NE
Shi kira (Da'awa) ana yinsa ne bisa hikima da kuma nazarin yadda za abi a isar da shi ta yadda zai yi amfani ga wadanda ake isarwa.
Idan baka iya yinsa ba, to, memakon a fahince ka zai ya zamana an qara nisantarka. Wannan dalili yasa Allah (T) ya umarci Manzonsa (S. A. W. W) da cewa yayi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinsa bisa hikima da wa'azi mai kyau.
Duk da cewa Annabi (S. A. W. W) mai kyakkyawar tarbiyya ce da sanin ya kamata, amma wannan umarnin da akayi masa sai ya qara masa taka-tsan-tsan wajen isar da saqo.
Yazo cikin riwaya daga Muhammad Al-Barqiyyu daga Sulaiman Bn Ja'afar Al-Ja'afariyyu ya daukaka shi (zuwa ga Annabi) yace,
Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" LALLE MU TARON ANNABAWA MUNA MAGANA DA MUTANE NE GWARGWADON HANKALINSU ."
- سن، المحاسن مُحَمَّدٌ الْبَرْقِيُّ عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ جَعْفَرٍ الْجَعْفَرِيِّ رَفَعَهُ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص إِنَّا مَعَاشِرَ الْأَنْبِيَاءِ نُكَلِّمُ النَّاسَ عَلَى قَدْرِ عُقُولِهِمْ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 106
Wannan hadisi na karantar damu ne cewa duk lokacin da mutum ya tashi yin kira (isar da saqo), to, ya riqa yin nazari game da hankalin wadanda yake son isar musu.
Za ka sami wasu da zurfin tunani, wasu rarrauna, wasu kuma hankalin su tamkar na dabbobi ne. Saboda haka a riqa sanin suwaye ake isar musu da saqo ko suwa ake kira.
Idan mutum bai bi irin wannan salo na Annabawa (A. S) ba, to, maimakon a fahince shi sai dai a qara nisantarsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd November, 2020/ 16th Rabi'ul-Awwal, 1442.