@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WA YAFI KIYAYE UMARNIN ANNABI (S. A W. W) TSAKANINSU ?
Sanin sassala da tarihin mutum na daga cikin Ma'auni na sanin Matsayin mutum wajen wani ko wajen wanda ya halicce shi.
Umar Bn Khaddab da Imam Ali (A. S) sun kasance manya daga cikin wadanda suka rayu tare da Annabi (S. A.W.W) har zuwa wafatinsa, kuma suna tare dashi cikin guraren daya halatta na yaqoqi daban-dabam.
Duk da cewa dukkansu suna tare dashi amma hakan ba zai hana a sami wanda yafi wani sanin maganganun Annabi (S. A. W. W) da kuma yin koyi dashi cikin umarni da hani ba.
Ya zo cikin MUSNAD KHULAFA'AR-RAASHIDEEN cewa Imam Ali (A. S) ya aikata wani aikin da Annabi (S. A. W. W) ya hane su, kuma Umar Bn Khaddab ya qalubalence shi.
Ga riwayar nan kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
101- حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ يَحْيَى ، قَالَ : أَخْبَرَنَا ابْنُ الْمُبَارَكِ ، قَالَ : حَدَّثَنَا مَعْمَرٌ ، عَنِ الزُّهْرِيِّ ، عَنْ رَبِيعَةَ بْنِ دَرَّاجٍ : " أَنَّ عَلِيًّا صَلَّى بَعْدَ الْعَصْرِ رَكْعَتَيْنِ ، فَتَغَيَّظَ عَلَيْهِ عُمَرُ ، وَقَالَ : أَمَا عَلِمْتَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَنْهَانَا عَنْهَا "
Hassan Bn Yahya ya bamu labari yace, Ib Mubarak ya bamu labari yace, Ma'ammar ya bamu labari daga Zuhriy, daga Rabee'ata Bn Darraaj (cewa),
" Lalle Aliyu yayi sallah raka'ah biyu bayan sallar la'asar, sai hakan ya fusata Umar, sai yace, " AMMA DAI KA SAN CEWA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA KASANCE YANA MANA HANI GAME DA HAKAN? "
Abinda ya daure min kai game da wannan magana shine, akwai wani guri dana taba karantawa inda Umar ke cewa da ba don Aliyu ba da ya halaka. Kuma ya fadi wannan magana ne sakamakon hukunce-hukuncen da ya riqa zartarwa na kura-kurai wadanda Imam Ali (A. S) ya riqa gyara masa ta hanyar amfani da ayoyin Alqur'ani.
Sannan kuma ya zo cikin Asbabun-Nuzul dangane da ayar da ke cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
بسم اللَّهِ الرحمن الرحيم.<br>قوله عز وجل
<span class=hd4>
" وَتَعِيَها أُذُنٌ واعِيَةٌ "
</span>
" KUMA (kunne) MAI KIYAYEWA ZAI KIYAYE ."
حدثنا أبو بكر التميمي أخبرنا عبد الله بن محمد بن جعفر أخبرنا الوليد بن أبان أخبرنا العباس الدوري أخبرنا بشر بن آدم أخبرنا عبد الله بن الزبير قال: سمعت صالح بن هشيم يقول: سمعت بريدة يقول: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لعلي: إن الله أمرني أن أدنيك ولا أقصيك وأن أعلمك وتعي وحق على الله أن تعي فنزلت
<span class=hd4>
" وَتَعِيَها أُذُنٌ واعِيَةٌ "
Abubakar At-Taimiy ya bamu labari, Abdullahi Bn Muhammad Bn Ja'afar ya bamu labari ,Waleed Bn Abban ya bamu labari, Abbas Al-Dauriy ya bamu labari, Bashar Bn Adamu Ya bamu labari, Abdullahi Bn Zubair ya bamu labari yace, " Na ji Salihu Bn Hasheem yana cewa, na ji Buraidata yana cewa, Manzon Allah (S. A. W. W) yana fadawa Aliyu (cewa),
" LALLE ALLAH YA UMARCENI DANA KUSANCEKA KADA NA NISANCE KA, KUMA NA SANAR DAKAI KUMA KA KIYAYE, KUMA HAQQI NE AKAN ALLAH KA KAKIYAYE ."
Sai aka saukar,
" KUMA KUNNE MAI KIYAYEWA ZAI KIYAYE SHI ."
Wannan hadisi na tabbatar mana ne cewa babu wani abinda Annabi (S. A. W. W) ya fada wanda Imam Ali (A. S) bai san shi kuma ya kiyaye shi ba.
Idan kuwa hakane za a sami wani wanda zai nuna masa ko tunatar da shi wani abu da aka ji daga Annabi (S. A. W. W) wanda shi ya manta shi alhali ya fi su kiyaye komai ?
Wannan dalili yasa nake son yin wasu tambayoyi kamar haka;
- Shin, dama yin sallar nafila bayan sallar la'asar haramun ne?
- Idan haramun ne, me yasa naga cikin littafan sunnah da Shi'ah aka kawo wasu salloli da ake yinsu bayan sallar la'asar don neman biyan buqata ?
- Shin, wa yafi wani sanin umarni da hani na Manzon Allah tsakanin Umar da Imam Ali (A. S) ?
- Sannan kuma wa yafi wani aikata abinda yayi musu umarni dashi a tsakaninsu ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th November, 2020/ 18th Rabi'ul-Awwal, 1442.