Hakuri Da Yin Uzuri Ga Mutane...Fita Na Uku (3)


 

Nayi magana akan hakuri a wancan rubutun, yanzu kuma zan danyi akan bada uziri a iya abinda nasani, Ngd sosai


Bada UZIRI : abinda yasa na hadasa da hakuri saboda bada UZIRI baya tafiya saida hakuri dole, don idan har baka yi hakuri ka tausasa zuciyarka ba, to bazaka taba iya ba mutum uziri ba, bare har katsaya kaji dalilin faruwar wani al'amari, kawai ranka na baci, ko wani abu yana faruwa zaka yanke hukunci akai ne batare da bada uxirin jin dalili ba.


Wannan ma yana taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu, domin idan har muna bama junanmu uziri, to tabbas zamu samu karancin aikata abubuwan da daga baya zamu dawo muna nadamar aikata su.


Shima wannan kar muce ai tsakaninmu da wane ko da wance babu bada uziri, saboda sun saba aikata aikin da suke aikatawa, A'a ya kamata ko wane lokaci suka aikata mu tsaya muji dalilin su na dai_dai wannan lokacin.


Don Imam Ali (as) acikin wani hadisi a littafin nahjul balaga da kuma mukarimul akhlaq yana cewa : ka bawa dan uwanka uziri sau 70/90. Amma a yanzu ko sau daya bama iya bama junanmu uziri, kawai da anyi mana laifi muke yanke hukunci.


Ya kamata mu kara samawa kanmu zaman lafiya ta wa'yannan hanyoyin tunda munata rasa sauran hanyoyin, yin anfani da hakurinmu da bada uziri zaya taimaka mana kwarai wurin kara samun zaman lafiya, da kaucewa aikin dana sani. Fatan Allah ya bamu ikon gyarawa baki daya. 


Nagode sosai


_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post