Hakuri Da Yin Uzuri Ga Mutane.. Fita Na Biyu (2)


 

Afuwan bari nadanyi magana akan hakuri duk da nasan inada karancin fahimta akan shi.


HAKURI: Dayawan mutane zasuce "ai nasan meye hakuri kums ai inada hakuri yanzu kuma me za'a fada mani akai," ni kuma sai ince, bawai nace baka sanshi bane ko kuma bakada shi bane, a'a a wuraren da yafi cancanta kayi amfani dashi ne baka anfani dashi. Domin dayawan mutanen mu bama anfani da hakurinmu inda ya kamata, sai kaga mutum yayi hakuri da mai kosan layinsu ya bata uziri,amma wallahi ya kasa hakuri da mahaifiyarsa, matar, yaransa ko kuma abokansa ya kuma kasa basu uziri, ni shaidane akan hakan.


Hakurin da kake fadar ai kana dashi ko kuma kina dashi baida wani anfani, idan ya zamana ka kebesa ne a iya wasu adadin mutane, kenan idan ba wa'yannan mutanen bane to ba wanda zaka dagawa kafa. Shi hakuri acikin zaman takewarmu wajibi ne, domin idan da ba hakuri da yanzu babu iyayenmu ma bare ayi maganarmu.


Mu zama masu hakuri acikin dukkanin ayyukanmu, musamman a zaman takewarmu da al'umma, bawai akan kudi,abinci,ko wani abu mai kamada haka ba kawai, a'a a kowane abu mu kasance masu hakuri, domin hakurin shine yake bada dama mu bawa junanmu uziri akan duk abinda sukayi Mana, kunga kenan zamu rage samun fadace_fadace da kuma aikin dana sani acikin al'ummarmu.


Allah yasa mu dace, insha Allah zan cigaba


_ Zarah A Zamsarf

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post