Hakuri Da Yin Uzuri Ga Mutane.. Fita Na Daya (1)


 

Tabbas wadannan abubuwa sunada matukar tasiri wurin fahimtar ko wace irin matsala da ake samu a rayuwa. 


Gaskiyar magana mutanen mu musamman hausawa, muna da karancin wayannan abubuwan acikin zaman takewarmu, bama bawa junanmu uziri sannan bama hakuri da junanmu.


Idan har babu hakuri da bawa juna uxiri, to kuwa tabbas zaman lfy zaya yi mana wahala, saboda idan abokin zamanka yayi maka laifii, kawai zakayi masa hukunci ne, ba tare da ka bawa zuciyarka hakuri da yi masa uziri kaji meye dalilin sa na aikata maka wannan laifnba.


Wannan shi yake haifar da dana sani acikin abubuwa dayawa na rayuwar mutanan mu, saboda akanyi hukunci ne akan rashin dai_dai da rashin fahimta. Bafa kowane laifi mutum yake aikatawa da gangan saboda son ransa ba, a'a akwai kurkure da kuma rashin sani.


Amma mutanenmu kamar jiran kuskurenka akeyi a hau akai ayi maka hukunci. Batare da ansan dalilinka na aikata hakan ba. Wallahi idan akace za ayi magana akan HAKURI DA BADA UZIRI za ayi littafi mai pages 1000 ba a gama ba saboda shine kawai acikin rayuwarmu baki dayanta. 


Insha Allah zan fadada magana akan HAKURI DA BADA UZIRI acikin rubutuna na gaba. Nagode


_Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post