@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SANYA KAYAN ALFARMA KO HAWAN ABIN HAWA BA YA DAGA CIKIN GIRMAN KAI
Nuna godiya ce ga Allah (T) idan yayi ma wata ni'ima ta wadata a ganta tare da kai, kuma aci a sha cikin wadatar da iyali ba tare da anyi musu qwauro ba.
Rashin fahinta ko jahilci kan sa ka ji wasu na zargin malamai kan cewa ba sa gudun duniya (ZUHUDU) yayin da suka gansu suna sanya kayan ado masu tsada ko kuma hawa abin hawa (mota) ta alfarma.
A fahinta irin tasu shine, sarakuna ko 'yan siyasa ko masu kudi ne kawai za su iya siffantuwa da wannan siffa, amma duk wadatar da Allah ya yiwa malami bai kamata ace ya godewa Allah ta wannan hanyar ba, godiyarsa kawai ta kasance ta hanyar sanya tsofin tsummokara ko hawa rubabben abin wanda wanda idan za su tafi wajen programme /wa'azi a riqa tura su suna isa a makare, idan sun isa su riqa bada uzuri, hakan shine Tawari'u.
Yazo cikin Ma'anil-Akbar kamar haka :
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
معاني الأخبار أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيٍّ الْكُوفِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ النُّعْمَانِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ طَلْحَةَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لَنْ يَدْخُلَ الْجَنَّةَ عَبْدٌ فِي قَلْبِهِ مِثْقَالُ حَبَّةٍ مِنْ خَرْدَلٍ مِنْ كِبْرٍ وَ لَا يَدْخُلُ النَّارَ عَبْدٌ فِي قَلْبِهِ مِثْقَالُ حَبَّةٍ مِنْ خَرْدَلٍ مِنْ إِيمَانٍ قُلْتُ جُعِلْتُ فِدَاكَ إِنَّ الرَّجُلَ لَيَلْبَسُ الثَّوْبَ أَوْ يَرْكَبُ الدَّابَّةَ فَيَكَادُ يُعْرَفُ مِنْهُ الْكِبْرُ قَالَ لَيْسَ بِذَاكَ إِنَّمَا الْكِبْرُ إِنْكَارُ الْحَقِّ وَ الْإِيمَانُ الْإِقْرَارُ بِالْحَقِّ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج2، ص: 142
Daga Sa'ad, daga Barqiyyi, daga Muhammad Bn Aliyul-Kufiy, daga Aliyu Bn Nu'uman, daga Abdullahi Bn 'Dalhata, daga baban Abdullah (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA DUK BAWAN DA KE DA GIRMAN KAI DAIDAI DA QWAYAR ZARRA (atom) CIKIN ZUCIYARSA. KUMA BA ZAI SHIGA WUTA BA BAWAN DA CIKIN ZUCIYARSA AKWAI IMANI DAIDAI DA QWAYAR ZARRA ."
Nace, na sanya fansarka (mahaifina da mahaifiyata) , lalle mutum yakan sanya tufafi (masu tsada) ko ya hau dabba (motar alfarma a wannan zamani) har aga kamar girman kai ne daga gare shi. Yace,
" BAI KASANCE HAKA BA, ABIN SANI GIRMAN KAI SHINE QIN GASKIYA (alhali an san gaskiyar ce). IMANI KUWA SHINE TABBATAR DA GASKIYA ."
Ma'ana, duk wanda zai ga ko ya ji gaskiya sannan yaqi karbar ta saboda bata fito daga bakin wanda yake so ba shine mai girman kai wanda ba zai shiga Aljannah ba. Imani kuwa shine yarda da tabbatar da gaskiya idan an ji ta ko daga bakin maqiyine ta fito.
Allah (T) ya kawo cikin Alqur'ani cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ كَذَّبَ بِآياتِ اللَّهِ وَ صَدَفَ عَنْها سَنَجْزِي الَّذِينَ يَصْدِفُونَ عَنْ آياتِنا سُوءَ الْعَذابِ بِما كانُوا يَصْدِفُونَ ."
(الأنعام)
" WAYE MAFI ZALUNCI DAGA WANDA YA QARYATA DAGA AYOYIN ALLAH KUMA YA KANGE (mutane) DAGA ITA ? DA SANNU ZA MU SAKAWA MASU KANGE (mutane) DAGA AYOYINMU DA MUMMUNIYAR AZABA SAKAMAKON ABINDA SUKA KASANCE SUNA KANGEWA ."
A wani guri kuma ya qara da cewa,
" وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ فَأَعۡرَضَ عَنۡهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُۚ إِنَّا جَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۖ وَإِن تَدۡعُهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ فَلَن يَهۡتَدُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا ." ٧٥
" KUMA WANENE MAFI ZALUNCI DAGA WANDA AKA TUNATAR (dashi) GAME DA AYOYIN UBANGIJINSA, SAI YA BIJIRE DAGA BARINSU, KUMA YA MANTA ABINDA HANNAYENSA SUKA GABATAR (na zunubi ) ? LALLE NE MU MUN SANYA ABUBUWAN RUFI AKAN ZUKATANSU DOMIN KADA SU FAHINCI SHI (gaskiya), KUMA A CIKIN KUNNUWANSU (muka sanya) WANI NAUYI, KUMA IDAN KA KIRAYE SU ZUWA GA SHIRIYA, TO, BA ZA SHIRYU BA A LOKACIN HAR ABADA !"
(SURATUL-KAHFI
:57)
To, irin wadannan mutane sune haqiqanin masu girman kai wadanda qamshin Aljannah ma ba sa suji ba ballantana su shigeta matuqar basu canza zuwa karbar gaskiya ba.
Daga wakilanmu na Bauchi.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
18th November, 2020/ 3rd Rabi'us-Sani, 1442.