@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Neman ilimi na kowanne fanni halas ne in ma bamu ce umarni ne na Allah (T) ba, domin an umarci bayi su neme shi don kyautata duniyarsu da lahirarsu. Babu wani ilimi da aka kebe shi kan cewa nemansa haramun ne matuqar dai ba na sihiri bane, domin shi Allah ya yi hani a kansa.
Cikin zamanin Annabi Sulaiman (A. S) an sami wasu mutane biyu (2) masu qaryar Annabta da ake kiransu HARUTA da MARUTA, sai ya kasance suna koyar da mutane sihirin yadda ake raba tsakanin miji da mata. To, duk wanda ya koyi irin wannan ilimi kuma har yake aiki da shi, ba shi da rabo a lahira, kamar yadda Allah (T) ke cewa,
.............وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٢٠١
" .......BABU ABINDA SUKE KOYARWA (na sihiri) GA WANI HAR SAI SUNCE, " ABIN SANI MU FA FITINA CE (gare ku) KADA KU KAFIRCE (ta hanyar bin umarninmu da koyarwarmu). KUMA SUNA KOYO DAGA GARE SU ABINDA ZA SU RABA TSAKANIN MIJI DA MATA DA SHI (ilimin nasu), ALHALI SU BA MASU CUTUWA NE DASHI BA DAGA WANI SAI DA IZNIN ALLAH. KUMA SUNA KOYON ABINDA ZAI CUTAR DASU BA ABINDA ZAI AMFANAR DASU (na sihiri) BA, ALHALI SUNA SANE (cewa) DUK WANDA YA SAYE SHI (sihirin) BA SHI DA WANI ABU NA RABO A LAHIRA, KUMA TIR DA ABINDA RAYUKANSU SUKA SAYA DA SHI, DA ACE SUNA SANI ."
(BAQARA:102)
Ilimin sanin shari'a (law) na daga cikin halattaccen ilimi wanda ake koyonsa kuma a riqe shi a matsayin sana'a wacce mutum zai riqa samun abinci ta hanyarsa. Ilimi ne da za kayi amfani da shi ka taimaki muslimci da kuma raunana wadanda ake zalunta.
Sai dai kuma mafi yawan masu irin wannan karatu (ilimi) yakan kai su ga halaka, domin ba sa amfani da shi don kyautata lahirarsu. Wadanda suka qware ta wannan hanya har suna iya lullube qarya da kuma boye gaskiya da shi, suna taimakon azzalumai, ana ganin su a matsayin sune masu ilimi wadanda ake alfahari da su idan mutum ya aikata zalunci ko kuma wani abin kunya.
To, ku ji tsoron Allah kan wannan aiki naku, domin duniya ba matabbata bace, komai yawan abinda kuke samu ta wannan hanya zai qare ko kuma ku mutu ku bar shi, sannan a lahira ba ku da wani kaso na alkhairi face wuta.
Allah (T) na bayyana muku cikin littafinsa mai tsarki cewa,
وَلَا تُجَٰدِلۡ عَنِ ٱلَّذِينَ يَخۡتَانُونَ أَنفُسَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ خَوَّانًا أَثِيمٗا ٧٠١
" KUMA KADA KUYI JAYAYYA (don taimako) AKAN WADANDA SUKA HA'INCI KANSU (ta hanyar zaluntar wasu), LALLE ALLAH BA YA SON WANDA YA KASANCE MAI HA'INCI KUMA MAI SABO ."
يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَلَا يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱللَّهِ وَهُوَ مَعَهُمۡ إِذۡ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرۡضَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطًا ٨٠١
" SUNA BOYEWA GA MUTANE (kar su gane cewa su azzalumai ne) KUMA BA SA BOYEWA GA ALLAH (domin Shi) YANA TARE DASU YAYIN DA SUKE KWANA (da nufin aikata) ABINDA BA YA (taba ) YARDA DA SHI NA DAGA MAGANA. KUMA ALLAH YA KASANCE GA ABINDA SUKE AIKATAWA MAI KEWAYAWA NE (da iliminsa )."
Sannan ya qara da cewa,
هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ جَٰدَلۡتُمۡ عَنۡهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَمَن يُجَٰدِلُ ٱللَّهَ عَنۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا ٩٠١
" GA KU YAA WADANNAN (lauyoyi) ! KUN YI JAYAYYA (a kansu) DON KU TUNKUDE MUSU (jin kunya) A CIKIN RAYUWAR DUNIYA, TO, WAYE (kuma daga cikinku) WANDA ZAI (iya) TUNKUDE MUSU (wannan jin kunyar) A RANAR QIYAMA ? KO KUMA WANENE (qwararren magana daga cikinku) WANDA ZAI KASANCE WAKILI A KANSU ?"
To, ku sani fa cewa,
وَمَن يَعۡمَلۡ سُوٓءًا أَوۡ يَظۡلِمۡ نَفۡسَهُۥ ثُمَّ يَسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَ يَجِدِ ٱللَّهَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا ٠١١
" KUMA WANDA YA AIKATA MUMMUNA KO KUMA YA ZALUNCI KANSA (ta hanyar zalunci ko boye gaskiya), SA'AN NAN (ya gane laifinsa har) YA NEMI GAFARAR ALLAH (ta hanyar tuba da neman afuwar wadanda ya zalunta) , TO, ZAI SAMI ALLAH MAI GAFARA MAI JIN QAI ."
وَمَن يَكۡسِبۡ إِثۡمٗا فَإِنَّمَا يَكۡسِبُهُۥ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا ١١١
" KUMA WANDA YA AIKATA ZUNUBI , TO, YA AIKATA NE AKAN KANSA, KUMA ALLAH YA KASANCE MASANI MAI HIKIMA. "
وَمَن يَكۡسِبۡ خَطِيٓـَٔةً أَوۡ إِثۡمٗا ثُمَّ يَرۡمِ بِهِۦ بَرِيٓـٔٗا فَقَدِ ٱحۡتَمَلَ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا ٢١١
" KUMA DUK WANDA YA AIKATA WANI KUSKURE KO YA AIKATA ZUNUBI (ta wannan hanya ta ku), SA'AN NAN YA JEFI WANI BARANTACCE (marar laifi) DA SHI, TO, HAQIQA YA 'DAUKI QIREN QARYA DA KUMA ZUNUBI BAYYANANNE ."
(NISA'I:107-112)
Saboda haka kawai ku yarda da laifinku ku nemi gafarar wadanda kuke zalunta ta hanyar hannayenku da harsunanku , kuma ku nemi gafarar Allah wanda Shi ya hane ku da aikata wannan mummunan aiki naku.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
28th November, 2020/ 13th Rabi'us-Sani, 1442.