Duk Wanda Ya Raina Babba Ba Ya Tare Da Annabi (S.A.W.W) !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KU TAUSAYAWA NA QASA DA KU KO KWA SAMI CETON ANNABI (S. A. W. W) 


An wayi gari yadda tarbiyya tayi qaranci cikin al'umma, manya basa tausayawa na qasa dasu, kuma qanana suka zama tsageru yadda ko kadan basu san girman na sama dasu ba ballantana su girmama su. Hakan kuwa na da alaqa ne da yadda suke ganin mahaifansu ba a bakin komai ba. 


Kun san matsalar ita ce, duk wanda bai ganin girman mahaifansa ba zai taba girmama na sama shi ba, domin mahaifi yafi cancanta a girmama shi ko wanne irin hali yake ciki .


Manzon Allah (S. A. W. W) ya tsoratar damu game da wannan rashin tarbiyya da kuma illarta. Ga dai riwayar kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


100 - (4) [صحيح] وعن عبد الله بنِ عَمر [و] رضي الله عنهما يبلُغُ به النبي - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قال:


Ya inganta daga Abdullahi Bn Umar cewa ya iso masa daga Annabi (S. A. W. W) yace, 



"ليس منا من لم يَرحمْ صغيرَنا، ويَعْرِف حقَّ كبيرِنا".


" BA YA TARE DAMU (duk) WANDA BA YA TAUSAYAWA QANANANMU , KUMA BAI SAN HAQQIN MANYANMU BA ."



رواه الحاكم وقال: "صحيح على شرط مسلم".


Haakeem ne ya riwaito, kuma yace ingantacce ne bisa sharadin Muslim. 


(SAHIHUT-TARGHEEBU WAT-TARHEEB) 


Aiki jaa-ja-jur a gabanmu, mu gyara tarbiyyarmu ko mu wayi gari ranar alqiyama cikin wata tawaga wacce ba ta Annabi (S. A. W. W) ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         08126385470


11th November, 2020/ 25th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post