Kashi na 6
Shaikh Zakzaky a jawabin da ya yi a ranar Litinin 7 ga watan Zulqa’ada, 1435 (1/9/2014) jim kadan bayan kammala karatun littafin Nahjul Balagah a muhallin Husainiyyah Baqiyyatullah, ya bayyana cewa:
“Da yake na yi magana ranar Laraba, na ji an ce; Hedikwatar Soja, za su yi mana raddi. Da yake na fadi cewa; ranar Litinin da ta wuce; sun yi yunqurin kashe ni a hanya. To, shi ne; aka ce; Hedikwatar Soji za su yi raddi. To, sai suka yi wani raddi, raddin zai ba ku dariya;
"Suka rubuta: ‘Defense Headquarters Response.’ Abin da suka ce; ‘The Nigerian Military Has No Plan To Frame Up Anybody Or Organization.’ A ‘heading’ sun ce wai, ko ‘Ill Petted Statement by Al-Zakzaky’ suke ‘Reputing’ a sama. Amma sai suka ce; ‘The Nigerian Military Has No Plan To Frame Up Anybody Or Organization. It’s Not In Our Character, Doctrine Or Practice. Anyone Who Is Not Planning To Cause Or Foster Violence & Breach Of Security Has No Cause To Fear Or Raise Alarm. The Military Will Not Succumb To Any Play To Distract It From Efforts At Containing Terrorism And Related Crimes Aimed At Undermining Security, Integrity & Constitution Of Nigeria As A United Country.’ Sing: Olukolade, Brig. General.'
"Dama da na ji an ce; za su yi ‘written’, kun san Sojoji akwai su da ilimi, akwai hikima kuma, saboda haka na san za mu ga ilimi da hikima. Wannan da shi da ba su ce komai ba duk daya. Inda suka ce; ‘Anyone Who Is Not Planning To Cause Or Foster Violence & Breach Of Security Has No Cause To Fear Or Raise Alarm.’ Muna da tambaya? A Juma’ar qarshe na Ramadan, 28 ga watan (Ramadan), 25 ga watan ‘July,’ wane laifi muka yi aka bude mana wuta da rana tsaka? Ko kuma ba Soja suka yi harbi ba?
"Kwamandan da ya yi umurnin harbin har yanzu shi ne Kwamandin Ofisa na FAR, Battalion din su a Basawa. Lieutenant Cruel Murderer Oku. Yana nan. Duk ‘ya’yana shi ya harharbe su. Ya ba ma’aikatan shi suka caccaka musu wuqa suka tattaka musu cikkuna a ganin idon mutane da rana tsaka.
"Ai mu ba wawaye ba ne, mu ce mun yi ‘Accusing’ duk ‘Military’ gaba daya. Ba ‘Military’ muka ce gaba daya ba, amma wasu suka yi. Tambaya su wadannan ba Soja ba ne? To, shi kenan, ba sai mu ce duk ‘Military’ ba ne. Su wadannan da suka yi tunda Soja ne, sai su ce mana wadannan sun yi da yawunsu ne ko ba da yawunsu ba. Ka ga yanzu idan mutum, dan mene zan zama ina fasa tafiya ba, saboda haka, kawai ina zaune za a zo a harbe ni. Ina ne aka rubuta, a wacce doka a ‘Nigerian Constitution’ ko a ‘Constitution Anywhere’ aka ce; idan mutum yana da ‘Uniform’ na Soja, yana iya kashe mutum idan ya ga dama? To, amma kashe mutane suka yi ‘at who’? Kuma har yanzu ba ku ce ba gaskiya ba ne, ba a yi kisan ba.
"Idan ‘Military’ suna son su wanke kan su; to, su kama ‘Murderers’ su hukumta su, ka ga sai ya zama shi Soja ba kisan kai yake yi ba, don ba mu san dokar da ta yarda ya kashe duk wanda ya ga dama ba. Tunda wasannan (shi Oku din nan) kisa ya yi da shi da Yaransa da rana tsaka, kuma har yana barazanar cewa; shi an ba shi ‘list’ ne na wadanda zai kashe, ya fada ne, da kuma yana fada ne ana ji, ya ce; shi an ba shi ‘list’ din wanda zai kashe ne, yanzu haka saura mutum 13, kuma zai kashe su.
"Kuma yake cewa; lokacin muna jana’iza ko ana jana’iza za a ji harbi ne kawai, zai zo ya ci gaba da harbinsa. Kuma akwai dana, Muhammadu, a lokacin har gidansa suka je, suka yi ‘Stationing’ Sojoji a wurin. Lokacin yana nan, sai ya ce; zai je ya dauko wani abin, sai wasu ‘yan uwa suka ce; a’a, gara mu mu je ko wani abu ne ya same mu maimaikon ka, sai suna zuwa sai Sojojin suka diddiro daga mota, da qyar suka tsira. Dole aka bar musu gidan.
"Saboda haka cewa yake yana da ‘list’ din wadanda zai kashe, zai kashe shugaban wadannan mutanen, kuma zai rusa Husainiyyah. To, kuma har yanzu shi ne Kwamanda na wannan Battalion din, yana nan, ‘Murderer’ yana nan, kuma sai dai in kun ce mana, wannan ‘crime’ din daidai ne a doka. Idan ba haka ba, rana tsaka mutum ya yi kisan kai ya zauna a yi mishi shiru, yana nufin ku ne masu kisan kan kenan.”
____
To, su sojoji sun ta nufin ya zama sun samar da wani yanayi ne na hargitsi da zai ba su damar ganin sun dira a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa a kowane lokaci. Don haka ne ma a wani Jawabinsa a ranar Asabar din 26 ga Zulqada, 1435 (20/9/2014) a muhallin Husainiyyah Baqiyyatullah, Shaikh Zakzaky yake cewa:
“To, in sun gan mu muna taro, sai su dauka mu ‘crowd’ ne. To, shi ‘crowd’ yana daga cikin dabi’arsa, mun karanta a ‘Sociology’, ‘Characteristic’ din ‘crowd’, akwai daga ciki cewa; shi ‘Crowd is a Leaderless’, ba shi da jagora, saboda haka, daga cikin dabi’arsa shi ‘Emotional’ ne, galiban sa, saboda haka idan mutum zai jagoranci ‘crowd’ yanka ihu zai yi. Zai ce; a yi kaza neeee, sai kawai shi kenan, sai kawai; yeeee, kawai sai a shiga yi.
"Saboda haka idan mutane suna zanga-zanga, wanda a kan titi kawai suka hadu, wannan ake ce ma zanga-zanga. Don haka ma muka ce; mu ba muna zanga-zanga ba ne, muna ‘Muzahara’ ne! Muna bayyana wani abu ne, ba muna zanga-zanga ba ne! Zanga-zanga kawai an rude ne kawai aka bayyana a bakin titi. To, yanzun nan duk wanda ya iya yanka ihu shi ne jagora. Sai ya kamfaci wani. In ana nan ana cikin wannan, sai wani dan sanda ya ce; a buge shi ne, sai ka ji ka-ka-kaf, kai ku daina ya isa haka nan. Wani ya ce; kai kashe shi ya kamata a yi, sai ka ji ka-ka-kau, to, shi kenan, ‘crowd’ kenan. Shi kawai bai da kan-gado. Shi kawai ba shi da jagora, kuma ‘Emotional’ ne kana iya juya shi yadda ka so.
"To, su jami’an tsaro har yanzu suna kallon mu ‘crowd’ ne, sai su zo su yanka ihu, ta nan ne ma muke gane jami’in tsaro. In ka ji mutum ya yanka ihu Malam ya ce; heee, a yi kaza neee! To, dube shi da kyau, za ka gan shi ko da gemun roba ko kuma bai da shi ya share, ya yi wani kamannu, wato ainihin dama daga Bariki ya zo. Wai shi ya dauka ‘crowd’ ne zai ja ‘crowd’ din ya riske shi ya yi yadda ya ga dama.”
A wani jawabinsa dangane da wannan yanayin, Shaikh Zakzaky yake cewa:
“Da yake su (jami’an tsaro) a tsammanin su bayan abin da suka yi, za a yi ta firfitowa ne ana ta qone-qone da buge-buge, su kuma sai su ji dadi, su yi ta kashe-kashe. Sai suka ga cewa; makamin mu daban da na su. Su na su Bindiga, mu kuma ba Bindiga muke amfani da shi ba. Ta yaya suka ga mutane tare da mu? Mun harba Bindiga ne jama’a suka zo? Da’awa muka yi, gaskiya muka rika. Babbar Makamin mu, ita ce gaskiya.
"Na san wani Dan Jarida ya tambaye ni dangane Palasdinu, ya ce; ya za ka ce dangane da yaqin da ake tsakanin Falastinawa da Isra’iliyawa? Kana ganin Falastinawa kuwa za su yi nasara ganin cewa makaman Isra’ila ya fi na su ‘yan Falasdin din?
"Sai na ce; ai makaman ‘yan Falastinu ba shi ne BINDIGA ba. Na’am suna harba duwatsu, na’am suna harba Rokoki, amma babbar makamin su, ita ce gaskiya. Ita kuma gaskiya ita take wanzuwa. Ko ba daɗe ko ba jima, lokaci ake jira. To, mu nan ma ko dutsen ma ba mu jefa ba. Kuma ba mu harba Roka. Namu makamin shi ne; gaskiya da muka riqa. Kuma wannan ne zai yi nasara.”
To, haka wannan yunqurin na ganin sun yi kisan kai ya ci gaba har qarshen wannan shekarar ta 2014, inda a ranar 19 ga Muharram 1436 (11/11/2014), Shaikh Zakzaky ke cewa:
“Azzaluman yanzu da na da duk tunaninsu qwara ɗaya ne, shi ne za su sheqar da jini, ‘la gairu’. Kashewa kawai! Kuma (kisan da suke yi) bai taba amfanarsu ba, kuma ba su taba dainawa ba. Haka nan har ya zuwa lokacin da (na nan duniya din) za su ga ‘jaza’i,’ sannan kuma qarshe kuma insha Allahul azim, kowanne zai je ga abin da ya yi aiki dominsa, shi ne qarshe Lahira, wanda kowa zai ga sakamakon abin da ya aikata. In ‘khairan, khairan,’ in ‘sharran, sharran’. Ta nan ainihin wanda suka sadaukar da rayuwarsu za su yi kyakkyawan qarshe, wanda kuma suka sheqar da jini za su yi mummunan qarshe. Wato riba biyu ga waɗanda suka yi imani suka dake, hasara biyu ga waɗanda suka butulce."
Za mu ci gaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)