Daga littafin: YUNKURIN KASHE SHAIKH ZAKZAKY


Daga littafin: YUNKURIN KASHE SHAIKH ZAKZAKY A TSAWON SHEKARU GOMA (2009-2019)

Kashi na 7


A ranar 22 ga Muharram 1436 (14/11/2014), Shaikh Zakzaky (H) yake bayyana cewa:


“Ɗazun abin da aka ce mana; an tara Sojoji a sansaninsu, an ce musu; Al-Zakzaky zai yi bore, saboda haka su zama cikin shiri komai na iya faruwa. To, me ya kawo sunan Al-Zakzaky kai da ka ke ‘training’? Kuma in ya yi bore, ina ruwanka da Boren? Na dauka idan ma wani abu ne, ba aikin ‘yan Sanda ba ne? Sai dai in dan Sanda ya gayyaceka ka taimaka masa, amma Soja da Bindiga an ce mishi Al-Zakzaky zai yi bore ya zama cikin shiri, komai na iya faruwa. 


"Wannan abin da aka gaya musu ɗazun kenan. Kuma aka ce su riqe bindigoginsu, yanzu haka bindigogin na hannunsu, kuma suna nan yanzu cikin shiri. Kuma sun shigo (Zariya) motoci ne ba kaɗan ba. Tun kwanaki suna ta shigowa, har da inda aka ga mota goma da Turawa zalla, sun shigo sun je Basawa, shekaranjiya wancan. Kuma yanzun mota goma, Mota 20 duk suna shiga. To, kuma duk ba za mu damu ba. Amma me ya kawo sunan Al-Zakzaky? Da yake shi Soja ana mishi tarbiyyah ne da cewa; su mutanen gari sune abokanan gabansa. Shi za shi ya yi kisan kai ne kawai!


"To, wala Allah su zama cikin shiri, kila sun shirya suna da wani ‘unit’ wanda zai sa baqin kaya, yaje ya yi ta’addanci, su ce; to, ka gani, dama mun gaya muku. Daga nan kuma sai su shigo gari, su shiga kisan kai. Ganin cewa; abin ya bayyana an san shirin su, bai damu magidantansu ba, amma kila ya dami su ‘agents’ ɗin su na nan.” Ya karkare. 


To, bisa hikimar Allah, haka aka qare wannan lokacin, dama watan Almuharram ne, wanda a ciki ake zaman Ashura, ba tare da sun iya samun nasarar afkawa Shaikh Zakzaky (H) ba. Sai dai a daren 30 ga watan Almuharram 1436 (22/11/2014) a muhallin Husainiyya Baqiyyatullah, Shaikh Zakzaky ya bayyana wani sabon shirin azzalumai a kan shirinsu na haramta Harkar Musulunci, inda yake cewa: 


“Wannan taron da muke yi ‘Movement’ ne, haka kuma Sallah da muke yi duk Movement ne, saboda haka yunquri na Musulunci yana nufin aikata shi a aikace. Ko da muke cewa Islamic Movement, ba qungiya ba ce. (Movement) Harka ko yunquri yake nufi, wato motsi na Musulunci. To idan ka ce ka hana, to kana nufin komai ma ba za a yi ba kenan. Domin ko Sallah ma ba za a yi ba kenan, tunda ka hana. To gwamnati tana so ta hana. Tana tsammanin za ta ce ta soke.


"Kasan kuma in suka soke, ‘yan Jarida za su ce an soke ‘Shiit Sect’ ko? An yi ‘Banning sect’ ɗin kenan. Wanda yake ko a dokarsu kowa yana iya yin addinin da ya ga dama. To kuma yana nufin kenan duk wani motsi ba za a yi ba, ba kawai Qudus da suka harba ba, har ma Ashura da Mauludi ba za a yi ba kenan. Duk tarurruka ma ba za a yi ba, kai har a gidanka ma ko karatu ma ba za ka yi ba. To an hana. Kamar sallolin nan da muke cewa za a yi duk ba za ka yi ba kenan, tunda ‘Movement’ ne, duk su ‘Movement’ ne a wajenmu, tunda motsi ne. ‘Concept’ ne a gurinmu ba qungiya ba.


"To, amma dai daga cikin abin da take sauwala musu shi ne za su ce sun yi ‘Banning Movement’ (IMN) ɗin, su ce ‘Terrorist Organization’ ne. Sai kuma daga nan sai su dira ma abin da suka kira “All-out-War’ har ya zama kafin Tattaki har sun gama. Kuma muna ganin suna take-taken waɗansu abubuwa haka nan. Amma su yi nasu mu yi namu. Abin da muke yi za mu fasa? (A’a). To ya rage musu ko su yi ko kar su yi. Insha Allahu. Zancen dai qwara ɗaya ne. Abu ɗaya ne rak! Mene kenan? Bindiga kawai! Za su yi harbi! Illa iyaka. Su ba su taɓa tunanin wani abu ba illa za su yi harbi, suna da bindiga. Shi kenan! La gairu!”


Za mu cigaba.


— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post