@ MA'ASUMAH NEWS UPDATED @
Ya zo cikin kalaman hikima na Imam Ali (A. S) yake cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
- وَ قَالَ ع لِبَعْضِ أَصْحَابِهِ- لَا تَجْعَلَنَّ أَكْثَرَ شُغُلِكَ بِأَهْلِكَ وَ وُلْدِكَ فَإِنْ يَكُنْ أَهْلُكَ وَ وُلْدُكَ أَوْلِيَاءَ اللَّهِ فَإِنَّ اللَّهَ لَا يُضِيعُ أَوْلِيَاءَهُ وَ إِنْ يَكُونُوا أَعْدَاءَ اللَّهِ فَمَا هَمُّكَ وَ شُغُلُكَ بِأَعْدَاءِ اللَّهِ.
Wata rana Imam Ali (A. S) yake fadawa Sahabbansa cewa;
" KADA KA SANYA MAFI YAWAN SHUGULGULANKA (damuwarka) GA IYALINKA DA KUMA 'YA'YANKA. IDAN IYALIN NAKA DA 'YA'YANKA MASOYA ALLLAH NE TO, AI ALLAH BA YA TOZARTA MASOYANSA. IDAN KUMA SUKA KASANCE MAQIYA ALLAH NE , TO, MENENE NA DAMUWARKA DA SHAGALTUWARKA GA MAQIYA ALLAH ?"
Wannan hadisi na karantar damu ne cewa, mu dai muyi qoqarin tarbiyyantar da iyalinmu baki daya, amma kada mu dora komai namu a kansu da yadda za su shagaltar damu. Nuna damuwarmu da soyayyarmu gare su na amfani ne in sun kasance mutanen kirki, kuma Idan mutanen kirki ne Allah (T) na qaunarsu, don haka ba zai kunyata su ko tozartar dasu ba.
Idan kuwa ba mutanen kirki bane damuwarmu gare su ba ta da amfani imma ba samun zunubi ba, domin son maqiyin Allah qin Allah.
Allah (T) ya gargadi Annabi Nuhu (A. S) yayin da yaga ya damu da al'amarin dansa kangararre wanda ya qi yin biyayya gare wajen amsa kiran Allah. Kuma yayi mar wannan gargadi ne don kada na baya irin mu mu damu da labarin 'ya'yanmu wadanda qiyayyarsu ga Allah ta bayyana.
Yana fada cikin Qur'ani cewa,
وَنَادَىٰ نُوحٞ رَّبَّهُۥ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ٱبۡنِي مِنۡ أَهۡلِي وَإِنَّ وَعۡدَكَ ٱلۡحَقُّ وَأَنتَ أَحۡكَمُ ٱلۡحَٰكِمِينَ ٥٤
" KUMA NUHU YA KIRA UBANGIJINSA (a lokacin da yaga dansa ya halaka cikin ruwa) YACE, " YAA UBANGIJI ! LALLE 'DANA NA DAGA CIKIN IYALINA, KUMA LALLE ALQAWARINKA GASKIYA NE, KUMA KAINE MAFI HUKUNCIN MASU HUKUNCI ."
قَالَ يَٰنُوحُ إِنَّهُۥ لَيۡسَ مِنۡ أَهۡلِكَۖ إِنَّهُۥ عَمَلٌ غَيۡرُ صَٰلِحٖۖ فَلَا تَسۡـَٔلۡنِ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۖ إِنِّيٓ أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ ٦٤
(Allah) YACE, " YAA NUHU ! LALLE SHI (wannan yaro) BA YA DAGA CIKIN IYALINKA, LALLE SHI (wani) AIKI NE WANDA BA NA QWARAI BA. SABODA HAKA KADA KA TAMBAYE NI ABINDA BA KA DA ILIMI A KANSA. HAQIQA NI INA YI MAKA GARGADI KADA KA KASANCE DAGA JAHILAI ."
(SURATUL-HUD:45-46)
Da Allah yasa wannan yaro mumini ne da bai halaka ba domin Allah ba zai tozarta shi ba. Amma da shike maqiyin Allah ne sai ya tafi ga halaka. Soyayyarka ga maqiyin Allah ba ta amfanarwa sai dai cutarwa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08127925034)
29th November, 2020/ 14th Rabi'us-Sani, 1442.
Allah ya saka da alkhairi Dan uwa
ReplyDelete