——Asperger
Yayinda ake gudanar da haramtacciyar shari'ar da akeyiwa Jagoran harka Islamiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da mai dakinsa Malama Zeenah a babbar kotun jihar Kaduna, almajiran Sheikh Zakzaky sun shiga sahun muzaharar kiran a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da Matarsa ba tare da wani sharadi ba, tare da bayyanawa al'ummar duniya cewa wannan shari'a da ake haramtacciyar shari'ar ce kawai da take hakkin Sheikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah.
Sai dai a yau Laraba jami'an tsaron Nigeria sun aukar da harin da suka saba kan almajirin Sheikh Zakzaky dake muzahara a Abuja. Misalin karfe 11 na safiyar yau aka masu muzaharar suka fito muzaharar cigaba da kiran asaki Sheikh Zakzaky a Nitel Junction Wuse II Abuja, take aka zarce da muzaharar cikin anguwar ta Wuse II bayan an shiga sahun muzaharar, inda suke tafe su na cigaba da kiran asaki Sheikh Zakzaky da Malama Zeenah da akaje gidansu aka kashe 'yayansu Uku gaban idonsu bayan an kashe almajiransa Dubbai, daga bisani kuma aka mishi ruwan harsasai shida mai dakinsa da rushe gidansu da kuma janshi kan gawarwakin 'yayansa, sannan tafi dashi aka tsare yanzu tsawon shekaru Biyar kenan ana tsare dashi duk da umarnin babbar kotun tarayya Abuja da ta bayar na asake shi a biyashi diya.
Muzaharar na tafiya cikin sahu a anguwar Wuse II Abuja, kwatsam sai karar harbin jami'an tsaro da saukar tiyagas kawai kakeji ta bayan muzahara, nan danan suka mamaye kan titi suna zage zage da iface iface, duk da wannan hali da ake ciki na tiyagas da suke ta harbowa kan masu muzaharar sai kabbarori kawai kakeji ke tashi daga bakin masu muzaharar, haka suka cigaba da karo karfi suna yunkurin dannowa domin kame masu muzaharar, alhamdulillah zuwa yanzu hada wannan rahoto ba labarin kama kowa, sai dai jikkatuwa da ba'adin masu muzaharar sukayi daga tiyagas da suka shaka. Wasu daga cikin hotunan muzaharar ta kafin harin jami'an tsaron.
18/11/2020