Cikakken Rahoton Zaman Kutun Zalumci Da Ake Karar Wanda Aka Kashe Wa Ya'ya 6 Da Almajirai Sama Da 1000 Na Yau Laraba 18 Ga Watan Nuwamba, 2020


 

Mai tattarawa Sa'id haruna 


'Yan uwa barkanmu da dawowa babbar kotun jihar Kaduna don ci gaba da shari'ar Shaikh Zakzakiy da mai dakin sa. Yanzu haka lauyoyin dukkan bangarorun sun bayyana. Alkali ya shigo an kira kes.


Sai dai wannnan karon an sami wani sabon lauya da ya tsaya wa Malama. In da Femi Falana da tasagarsa suke tsaya wa Shaikh Zakzakiy.


Yanzu haka Brig Gen SK Usman da Kanar Babayo da kuma Alhaji Gire duk sun iso kotu don ba da shaida. Lauyan Gwamnati, Bayero Dari ya kira shaidansa na farko, wato SK Usman. Alkali ya tambayeshi zai rantse ne ko zai yi alkawari? Ya zabi alkawari.


Ya yi alkawari cewa zai fadi gaskiya. Bayero ya fara tambayarsa cewa ranar 12/12/2015 Yana ina? Ya ce ranar suna Dutse jihar Jigawa wajen taron shugaban rundunar sojin Nijeriya. In da suka kamo hanyar zuwa Zaria don taron yaye daliban makarabtar koyar da aiki soji da ke Zaria. In da kuma za su kaiwa Sarkin Zazzau ziyara.


Amma suna cikin tafiya a Zaria aka tare musu hanya. Ya ce da ya sauka don ganin abin da ke faruwa sai ya tarar da yara matasa dauke da makamai. Ya yi ta rokonsu da su ba su hanya su wuce Amma suka ki. Suka ce sai Malam ne kawai zai iya ba su umarni su bude hanyar. 


Don haka na dauki waya na kira Malam Musa Almizan, saboda na san shi kuma shine Editan jaridar Almizan.


Dalilin da ya sa na kira shi dan ya bani lambar Malam Musa Yawuri (Hamza) ya aika min da lambar na kira Malam Musa Yawuri. Musa Yawuri na hannun daman Malam Zakzakiy ne. Ya ce ba abin da zai iya yi. Don haka ya kashe wayarsa. Ya yin da su kuma matasan suke ci gaba da kara yawa.


Bayero Dari ya tambayi SK Usman ko zai iya fadin adadin matasan? Ya amsa masa da cewa suna da yawa sosai don haka ba zai iya fadin yawansu ba.


SK Usman ya ce ana cikin haka sai ya ji harbin bundiga don haka dole ya boye. Don haka sai hanya ta bude suka wuce zuwa fadar Sarkin Zazzau.


Bayero ya tambayeshi ko ya san daga in da harbin bindigar ya fito? Ya ce a zatonsa daga Hussainiya ne harbin ya fito.

Bayero ya ce ko zai iya fadin lokacin da ya dauka Yana rokon yaran su bude musu hanya? Ya ce ya kwashe kamar mintuna 30 xuwa awa daya yana rokonsu.


Bayero ya ce ko zai iya bayyana yanayin da matasan suke ciki? Ya ce suna dauke da makamai kamar su Adda, sanduna da gwafa


SK Usman ya ce waya yarinya tada dauke da alkur'ani a hannunta ta so dukkan sa. Femi Falana SAN ya mike ya ce bai yarda da yadda Bayero ke sa wa wanda ke ba da shaida magana a baki ba. Don haka ya nemi alkali ya hana shi. Alkali ya ce a wannan mba matsala bane tun da bai kira sunan kowa ba.

Don haka SK Usman ya ce gaba da cewa lokacin a hanya fa bude an yi ta jifarsu da duwatsu har zuwa PZ.


Bayero ya tambayi SK Usman wace hira suka yi da matasan kafin a bude hanya? Lauyan Malama ya mike ya ce bai yarda da wannan tambayar saboda ba ta a cikin takardar da ya rubuta ta shaida. 


Daga karshe alkali ya tsawatar wa Bayero Dari. In da ya canza tamabayr zuwa cewa ya fada wa kotu abin da yaran suka fada masa. Don haka ya ce yaran sun fada musu cewa jiya an kashe musu mutane biyu za su yi musu Sallah ne. Don haka ya ce ai suma musulmi ne kuma za su kasance cikin wannan Sallah. Daga baya suka sami labarin cewa ashe rikici aka yi a wani kauye tsakanin su da wani bangaren musulmi a wani Kauye kusa da Zaria.


Bayero ya tambayi SK Usman ko akwai wani abu da zai fada wa kotu? Sai ya ce shi a iya rayuwarsa bai taba ganin tashin hankali irin na wannan rana ba.


Bayero ya tambayi SK Usman me ake nufi da Hussainiya? Ya ce abin da kawai ya sani shi ne yana wucewa ta hanyar kuma akwai wani fili mallakar Islamic Movement in Nigeria.

Bayero ya sake tambaya wanene Chief of Army Staff? Ya amsa da cewa Tukur Yusuf Buratai.


Lauyan MalamFalana SAN ya fara tambayarsa ko zai iya tuna cewa ya bayar da shaida a gaban kwamitin hukumar bincikr da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa?


Falana SAN ya ce ko zai iya tuna cewa sojojinsu sun kashe wadannan da ya kira matasa har 347? SK Usman ya ce shi ma a jarida ya karanta.


Falana ya sake tambayarsa ko a gabansa aka kashe wadannan matasa? Ya ce ba a gabansa ba ne.


Falana ya tambayeshi ko ya san cewa bunciken da JCI suka yi ya tabbatar da ceea Buratai ya rufe wadannan matasa 347 ba tare da yin abin doka ta ce ba?

SK Usman ya ce bai sani ba. Shima a jarida ya karanta


Ya ce a matsayinka na mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya za a iya tuna cewa ka futar da sanarwar manema labarai a ranar 12/12/2015? Ya ce eh zai iya tunawa.

A wannan takarda ka san cewa ka bayyana cewa abin takaici ne na rasa rayuwa. Ya ce ya san ya fitar da takarda a wannan rana Amma ba zai iya tuna abin da ke cikinga gaba daya ba.


Ko zai iya tunawa a takardar ya ce Shia sun yi yunkurin kashe Chief of Army Staff? SK Usman ya ce zai iya tuna ya fitar da takarda amma ba zai iya tuna ko ya fadi hakan ba.


Zai iya tuna cewa ya fadi a takardar cewa idan suka dawo da doka za su fice daga wuraren da suka mamaye su mika wa yan sanda? Ya ce ba zai iya tuna wa ba.


Lokacin da ya ke lokacin da kake rokin matasa da su ba ki hanya ku wuce akwai sauran mutane da aka takura wa a hanyar? Ya ce bai sani ba saboda motocin su na da yawa. Falana SAN ya sake tambayarsa motocin kadai ko har da na sauran mutane? Ya ce bai sani ba

Ko zai iya fadin nisan da ce tsakanin su da Hussainiya lokacin a aka tare su? Ya ce ba zai iya sani ba. To ya aka yi har ya ji karar bundiga? Ya ce bai sani ba


Wa ya buda musu hanya suka wuce? Ya ce bai sani ba amma dai akwai wadanda alhakin kare rayuwar Chief of Army Staff din haka yana zaton su ne. Sojoji ne su ko farar hula? Ya ce bai sani ba


Lokacin da aka tareku shin kun fada wa yan sanda? A matsayinka na mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya ba ni da hulda da yan sanda. Saboda haka ban sani ba. Aikina shi ne hulda da yan jarida da wayar da kan al'umma


Shin kun harba riyagas ko harsashe ne kuka sami hanya kuka wuce? 


SK Usman ya ce bai sani ba SK ya kara da cewa ba su da tiyagas


Ko ya san cewa sojoji sun yi amfani da harsashe mai rai wajen buda hanya su wuce? Ya ce bai sani ba.


Ko zai iya tuna cewa ya fada wa JCI cewa Kofur Dan Kaduna Yakubu ya mutu a wajen. Ya ce eh zai iya tunawa.


Zai iya tuna cewa ya je gaban wata kotu ya ba da shaida a shari'ar da aka yi wa wadanda aka kama? Ya ce eh zai iya tunawa.

Ko ya san cewa an tuhumi mutane 100 a wannan kotun da kaifin kashe Dan Kaduna? Ya ce shi shaida ne, don haka bai san yawansu ba. Shin ko ya yi magana da Shaikh Zakzaky a wannan rana ta 12/12)2015? Ya ce ya yi magana da Malam Musa Yawuri. Aka sake maimaita masa ya sake fadin Malam Musa Yawuri. Daga karshe alkali ya yarda cewa bai yi magana da Shaikh Zakzaky ba.


Shin ko ya san cewa sojoji sun kwashe kwanaki biyu a Zaria suka abin da suka kira operation? Ya ce bai sani ba. 


Ya ce ya san cewa a matsayinsa na mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya ya kwashe kwanaki uku yana kare abin da ake yi a Zaria. Ya ce shi dai kawai abin da ya sani shi ne abin da ya faru a 12/12/2015. 


Kana nufin ba da san abin da ya faru a 13/12/2015 da 14/12/2015? Ya ce bai sani ba.


Shin ya zai iya tuna cewa ya bayar da takardar yada labarai cewa an kama Shaikh Zakzaky a ranar 14/12/2015? Ya ce eh ya sani. 


Shin ko ya san cewa shaikh farar hula ne? Kuma sun daukeshi sun kai shi bariki? Ya ce bai sani ba


Shin ko ya san Shaikh Zakzaky a rayuwarsa? Ya ce bai taba sanin sa ba sai bayan an kama shi in da ya ganshi a DSD ofis a Abuja.


Shin ko lokacin da aka tare musu hanya Shaikh Zakzaky na wurin? Ya amsa da cewa in da yana wurin da bai kira waya ba. Falana SAN ya a ce bai yarda da wannan amsar ba. Amma alkali ya ce abin da SK Usman ke nufi shi ne Shaikh Zakzaky ba ya wurin.


Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauayan Malama ya mike


Shin ko zai tabbatar da maganar na ceea ya kwashe mintuna 30 xuwa awa daya yana rokon matasa da su ba su hanya? Ya ce eh haka ne.


A wannan tsawon lokacin ko zai iya shaida mutum daya daga cikin matasan? Ya ce bai san su ba.


Lauyan Malama ya karanta masa in da yake cewa sun yi harbi a sama don samun hanya su wuce. Shin wannan karya ka yi wa kotu? Ya ce shi ba makami a hannunsa lokacin


Lauyan Malama ya ce shi da sauran tambaya. Kotu ta sallami SK Usman. An kira Col Babayo Muhammad wanda ya bayyana cewa shi ne Commander 25 Briget Damboa jihar Borno


Bayero Dari ya Fara da tambayarsa cewa a shekarar 2015 yana ina Ya ce a lokacin yana kwamanda sector 2 na operation yaki a jihar Kaduna


Me ya sani kan abin da ya faru a ranar 12/12/2015? Ya ce an sami matsala da Islamic Movement in Nigeria a Zaria da tawagar Chief of Army Staff a kan hanyar sa ta zuwa Zaria don ziyarar Sarkin Zazzau da kuma kaddamar da sabbin sojoji a Depot Zaria. Ya ce a wannan ranar ne aka bashi umarnin ya dauki sojoji 40 ya tafi Zaria. Ya ce an turasu ne don su dawo da tsaro a Zaria. Ya ce daga isarsu aka Fara attacking din su.


Ya ce an ce su kamo Shaikh Zakzaky sannan sun bincika makamai a gidan Shaikh Zakzaky. Ya ce don haka aka tura shi Danba (Denbo) ya ce da ya ce ya zagaye wurin. Sai wani mai fararen kaya ya fito da takobi a hannunsa yana cewa Allahu Akbar ya tunkaro su.Don haka ya ja da baya ya fada wani masallaci. Ya ce yana shiga masallacin wata mace da wasu maza suka suka rikeshi da bindigarsa da ke dauke da harsasai 60. Suka kwace bindigar da harsasai suka caka masa wuqa a baya. Suka barshi kwance sun dauka ya mutu.


Col Babaye ya ci gaba da cewa yana dauke da rohotin asibiti kan wannan raunin da suka yi mishi.


Falana SAN ya ko ya san sojoji sun kashe yan Shia 347? Babayo ya ce bai sani ba.

Ya ce ya san na ranar 12/12/2015 amma ranar 13/12/2015 ba ya cikin hankalinsa saboda ranar ne aka caka masa wuka kuma sai da ya yi wata 8 a asibiti.


Shin zai iya tuna cewa ya je JCI ya ba da shaida? Ya ce eh zai iya tunawa.


Ko zai iya tuna cewa ya bayyana cewa an kashe yan Shia 347 kuma an yi musu janazar bai daya a Mando? Ya ce bai sani ba.


Ko zai iya tuna cewa an kashe soja lokacin rikicin? Ya ce eh zai iya tunawa domin an kawo gawar lokacin da ya ke kwance a asibiti 44. 

Ko an kashe fararen hula lokacin rikicin? Ya amsa cewa bai sani ba.


Ko kana wurin da aka rufe hanya? Ba na wurin.


Ko ka taba ganin Shaikh Zakzaky? Ko sojojinka ne suka kama Shaikh Zakzaky? Ba su bane.


Kace kun je bunciken makamai ne a Dambo, ko kun yi aikin da kuka je yi? Ba su yi ba.


Shin kafin ki tafi bunciken kun nemi takardar a kotu? Ba mu nema ba.

Ko kasan cewa sojoji suka kama Shaikh Zakzaky da matarsa? Ya ce eh ya sani.


Ko kasan cewa su farar hula ne? Ya ce eh ya sani.Ko kasan cewa an harbeshi har ya rasa idon sa? Ya ce bai sani ba. 


Shin kasan cewa mutane 347 ne da kuka kashe ne suka kashe Yakubu Dan Kaduna? Ya ce bai sani ba.Ranar 20/6/2017 ka ba da shaida a kotu in da ake tuhumar Shia 100? Ya ce eh ya ba da shaida.


Shin kasan cewa dukkan wadannan mutane da ka ba da shaida a kansu kotu ta sallamesu? Ya ce bai sani baShin ko kasan cewa ba soji ko daya da aka tuhuma da kaifin kashe fararen hula 347? Ya ce bai sani ba.


Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya tashi.


Bayero Dari ya nemi kotu da ta dage zaman sai gobe saboda a ba mutane damar shiga gari. Domin an tare koina a garin. Falana ya yi nasa ba'a cewa a kira Buratai ya zo ya bude hanya


Kotu ta dage zaman yau sai zuwa gobe

#Criminal_Buhari_Free_Zakzaky_dole

18/11/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post