Babu Mahaukaci Kamar Mai Yin Hani Ga Mummunan Aiki Kuma Shi Yana Aikatawa !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Ba rasa masu karatu ko yin wa'azi aka rasa a wannan zamani ba sai dai qarancin masu aikata abinda suke fadawa al'umma. 


Da yawa za ka sami masu yin wa'azi ba sa aikata abinda suke fada, ko kuma ba sa nisantar munanan ayyukan da suke yin hani a kansu. Wannan dalili yasa aka sami qarancin masu aiki da abinda suke ji daga bakunan malumansu. 


Ko da shike wasu na cewa wai kayi aiki da fadar malam amma kada kayi aiki da aikinsa, wanda hakan ke tabbatar da cewa abinda malaman ke fada ya sha bamban da ayyukansu. Amma malamai na kirki aikinsu na zuwa daidai ne da abinda yake fada. 


Shi yasa ma Imaman Ahlul-Bait (A. S) ke cewa,


  " LALLE YIN KIRA (da'awa) TA HANYAR AIKI YAFI YIN KIRA DA BAKI (ba aiki) ."



To, duk mai irin wannan halayya ko dabi'a ya sani cewa Allah (T) na kargadinsa da cewa, 



 " أَتَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبِرِّ وَتَنسَوۡنَ أَنفُسَكُمۡ وَأَنتُمۡ تَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ " ٤٤


" YANZU ZA KU RIQA UMARTAR MUTANE NE DA (aikata) AYYUKAN ALKHAIRI KU KUMA KUNA MANTAWA DA KAWUKANKU ALHALI KUNA KARANTA LITTAFI (dake nuna muku Illar yin hakan)? ASHE BA ZA KU HANKALTA BA ?"


              (BAQARA:44)



Su bayin Allah na kirki wadanda ake son yin koyi dasu ayyukansu ba sa sabawa fadinsu, duk abinda suka hane ku a kansu ba za ku same su suna aikata shi, sannan kuma sun fi ku aikata abinda suke umartar ku da aikata shi. 


Annabi Shu'aibu (A. S) ya gargadi mutanensa game da tauye mudu da sikeli da suke yi yayin awo ko aunarwa, kuma hakan bai yi musu dadi ba shine suke cewa; 



" قَالُواْ يَٰشُعَيۡبُ أَصَلَوٰتُكَ تَأۡمُرُكَ أَن نَّتۡرُكَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَآ أَوۡ أَن نَّفۡعَلَ فِيٓ أَمۡوَٰلِنَا مَا نَشَٰٓؤُاْۖ إِنَّكَ لَأَنتَ ٱلۡحَلِيمُ ٱلرَّشِيدُ " ٧٨ 


" SUKA CE, " YAA SHU'AIBU ! YANZU SALLARKA CE TAKE UMARTARMU DAMU BAR ABINDA UBANNINMU KE BAUTAWA KO KUMA (kada) MU AIKATA ABINDA MUKE SO CIKIN DUKIYARMU? LALLE KAI MAI HAQURI NE KUMA SHIRYAYYE (suna fada masa cikin izgilanci ."


Da yaji abinda suke fada masa sai yace; 



" قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَرَزَقَنِي مِنۡهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أُخَالِفَكُمۡ إِلَىٰ مَآ أَنۡهَىٰكُمۡ عَنۡهُۚ إِنۡ أُرِيدُ إِلَّا ٱلۡإِصۡلَٰحَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُۚ وَمَا تَوۡفِيقِيٓ إِلَّا بِٱللَّهِۚ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ ٨٨ "



" YACE, " YAA KU MUTANENA ! KUNA GANI IDAN NA KASANCE AKAN HUJJOJI BAYYANANNU (na shiriya) DAGA UBANGIJINA KUMA YA AZURTANI DA ARZIQI MAI KYAU DAGA GARE SHI (me kuma za kuce a kaina) ? NI FA BA NUFINA NE NA SABA MUKU CIKIN ABINDA NAKE HANARKU A KANSA BA, NUFINA KAWAI SHINE NAYI GYARA GWARGWADON IKO, KUMA DACE NA (ba ga kowa yake ba) SAI GA ALLAH, A GARE SHI NA DOGARA KUMA GARE SHI NAKE MIQA AL'AMARINA ."


              (HUD:87-88)


Wannan ita ce siffar da dukkan wani mai wa'azi ya kamata ya kasance, idan yayi hani, to, ya kasance shi yafi kowa hanuwa. 



To, dangane da wadanda ayyukansu ke saba abinda suke fadawa mutane kuwa, Annabi (S. A. W. W) ya siffanta su da Fitina ce. 


Ga dai riwayoyin kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


رواه البيهقي (1).


130 - (8) [صحيح لغيره] ورُوي عن أبي بَرزةَ رضي الله عنه قال: قال رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -:

"مَثلُ الذي يُعلِّمُ الناس الخيرَ وينسى نفسَه، مَثَلُ الفَتيلة؛ تُضيءُ على الناسِ، وتَحرقُ نَفْسَها".

رواه البزار (2).


An riwaito daga Abu Barzata (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" MISALIN WANDA KE SANAR DA MUTANE ALKHAIRI SHI KUMA YANA MANTAWA DA KANSA, MISALIN FITILA CE, TANA HASKAKAWA MUTANE KUMA TANA QONA KANTA ."



A wata riwayar kuma, 



131 - (9) [حسن صحيح] وعن جُندُب بن عبد الله الأزدي رضي الله عنه -صاحبِ النبي - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -- عن رسول الله - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قال:

"مَثَلُ الذي يُعلِّمُ الناسَ الخيرَ وينسى نفسَهُ، كمثل السِّراجِ؛ يضيء للناسِ وَيَحرقُ نفسه" الحديث.


An karbo daga Jundubi Bn Abdullahi Al-Azdiy (R. A) sahabin Annabi (S. A. W. W), daga Manzon Allah (S. A. W. W) yace :


" MISALIN WANDA KE SANAR DA MUTANE ALKHAIRI KUMA YANA MANTA KANSA (wajen aikatawa), KAMAR MISALIN FITILA CE, YANA HASKAKAWA DON MUTANE KUMA YANA QONA KANSA ."


رواه الطبراني في "الكبير"، وإسناه حسن إن شاء الله تعالى (3).


'Dabarani ya fitar da shi cikin littafinsa (AL-KABEER) , kuma isnadinsa mai kyau ne insha Allahu (T). 


(SAHIHUL-TAIGHEEB WAT-TARHEEB) 



An sami wata riwaya kuma dake siffanta yadda mai irin wannan hali zai kasance, siffar babu dadin ji, amma dai ku biyo mu don ji da gani cikin riwayar kamar haka :


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


24 - باب تغليظ عقوبة من أمر بمعروف أَوْ نهى عن منكر وخالف قوله فعله


Babin narkon azaba ga wanda ke yin umarni game da kyakkyawa ko kuma yin hani game da abin qi, amma aikinsa na sabawa fadinsa. 



حديث رقم :198


وعن أَبي زيد أسامة بن حارثة رضي الله عنهما قَالَ:


سمعت رَسُول الله صلى الله عليه وسلم يقول: (يُؤْتَى بالرَّجُلِ يَوْمَ القيَامَةِ فَيُلْقَى في النَّارِ، فَتَنْدَلِقُ أقْتَابُ بَطْنِهِ فَيدُورُ بِهَا كَمَا يَدُورُ الحِمَارُ في الرَّحَى، فَيَجْتَمِعُ إِلَيْه أهْلُ النَّارِ، فَيَقُولُونَ: يَا فُلانُ، مَا لَكَ؟ أَلَمْ تَكُ تَأمُرُ بالمعْرُوفِ وَتنهَى عَنِ المُنْكَرِ؟ فَيقُولُ: بَلَى، كُنْتُ آمُرُ بِالمَعْرُوفِ وَلا آتِيهِ، وأنْهَى عَنِ المُنْكَرِ وَآتِيهِ) مُتَّفَقٌ عَلَيهِ.قوله: (تَنْدلِقُ) هُوَ بالدالِ المهملةِ، ومعناه تَخرُجُ. وَ(الأَقْتَابُ): الأمعاءُ، واحدها قِتْبٌ


An karbo daga baban Zaid Usamata Bn Haarithata (R. A) yace:


Naji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa, 


" ZA AZO DA WANI MUTUM RANAR ALQIYAMA SAI A JEFA SHI CIKIN WUTA, SAI DUK KAYAN CIKINSA SU FITO WAJE, YA RIQA JIJJUYAWA DASU KAMAR YADDA JAKI KE JIJJUYAWA A TURKE. SAI 'YAN WUTA SU TARU GARE SHI (suna kallonsa), SUNA CEWA :


" YAA WANE ! MENENE (haka muke gani ) GARE KA ! ASHE BA KAINE KAKE YIN UMARNI DA KYAKKYAWA KUMA KANA YIN HANI GAME DA MUMMUNA BA ? SAI YACE : NA'AM, NA KASANCE INA YIN UMARNI DA KYAKKYAWA AMMA BANA ZUWA GARE SU, KUMA INA HANI GAME DA MUMMUNA AMMA INA JE MUSU ."


Anyi ittifaqi kan inganci wannan hadisi. 

     

      (RIYADUS-SAALIHEEN)


To, gaskiyar magana babu wani cikakken mahaukaci kamar wanda zai gane gaskiya har ya umarci mutane da aikata amma shi yayi watsi da wannan gaskiyar, ko kuma ya gano wani sharri har ya hani mutane game da aikata shi amma kuma shi yana aikatawa. 


Wannan abu shi ke tashe cikin nasu daura kwali (headtie) a kawukansu da sunan malamai. 


Allah ya bamu ikon aikata daidai. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


      ( 08137925034)


13th November, 2020/ 27th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post