Muna Allah wadai da kisan da ƴan Boko Haram suka yi Zabarmeri ta jihar Borno, dama sauran kashe kashen da akeyi a sassan Arewacin Najeriya.😭😭😭
Duk rai raine, koda na dabba ne madamar aka rabashi da gangar jiki ba akan ƙa'da ta shari'a ba to sunan abinda akayi Zalunci kuma Allah bazai bari ba.
Miyasa a wajen 'ƴan Arewa ran ɗan shi'a yake a banza ba'a bakin komi yake ba saɓanin na saura?
Miyasa da rana tsaka Sojojin Najeriya suka kwashe awa 48 babu dare babu rana suna buɗe wuta ga ƴan shi'a mata da maza harda tsofi amma ɗan Arewa yadunga murna yana jin daɗi harda shirya walima?
Miyasa bayan sun kwashe waɗan'nan awoyin suna aikin ta'addanci duniya na kallo, kuma suka turo matasa ƴan Iska suna ma gawarwakin da suka kashe sata, suna sace wayoyi da Zabba gami da kuɗin da ke aljifan gawarwakin musulmi?
A hasashen masana masu adalci suntabbatar da acikin awa 48 a Zariya sojoji sun kashe sama da mutum dubu, sun ɓatar da sama da mutum ɗari bakwai (haryanzu ba'asan suna raye ko basu raye ba).
A ƙididdigar Gwamnatin Kaduna kuma dabakin su, a hukumance sunce sunkashe mutum 347, shin waɗan'nan ba Ƴan Adam bane? Shin su basu cancanci a tausaya masu ba?
Shin kisan waɗan'nan bayin Allah bai isa ya saukar da fushin Allah akan mutanen ƙasar nan ba?
Idan har Boko Haram (marasa kaki) zasu fito suyi ta'addanci, su yanka mutum 70 a ƙididdigar RFI har kowa da kowa yayi tofin Allah tsine akan kisan, Amma ƴan'uwansu masu kaki sufito suyi kisan linkin-balinkin waɗan'nan amma munafukan Arewa sukama bakin su suyi shiru wasuma harda murna, babu abinda zai hana Allah yayi fushi da mu yayi ta yanko mana bala'i, ya jarabamu da Azzaluman Shugabanni, kuma muroƙi Allah ya kawar dasu Allahn yaƙi karɓar Addu'a.
Yakamata muzama masu adalci masu kishi, koda baka da tunani irin na Musulunci kazama mai tunani irin na ɗan'adamtaka.
Kada ka fifita ran wani akan na wani, koda ran mai bautar gumaka ne, madamar kasan cewa rai ne, saboda Allah yana kishin abinsa, kai yamafi son ran kafiri bisa ga ka'abar da kake kallo kanayin sallah, saboda yace da a kashe rai ɗaya (ko na wanene) gara ka rusa ka'aba.
Aƙarshe muna Allah wadai da masu kisa na ɓoye da na bayyane Allah ka tona masu Asiri, Allah muntuba Allah ka yafemana kuskuren da mukayi, Allah ka ƴantar mana da Jagora Shikh Ibrahim Zakzaky daga Hannun masu kisan dake tsare dashi.