Muhsin Fakhrie Zadeh ya yi Shahada da Azuhur din yau Juma'a, a gundumar Damawoun, a cikin birnin Tehran na kasar Iran.
Ana kirga Muhsin Fakhriy Zadeh a jerin masana mafiya tasiri a fagen binciken ilimi a kasar Iran.
Majiyoyin labarai sun baiyana cewa wannan babban masanin an kai musu hari ne da azzuhurin yau Juma'ah, shi da mai tsaron lafiyar shi, a wani hari da ba'a San wadanda suka kai musu shi ba, harin da ya yi sanadin shahadar masanin, tare da jikkatar mai tsaron nashi a wannan hari na ragwantaka da ta'addanci.
Wannan masanin dai, Natenyahu na Isra'ila ya taba fadawa kafofin watsa labaran Isra'ila cewa, an yi yunkurin a kashe shi amma ba'a yi nasara ba a shekarun baya.
An ce sunan Muhsin Fakhri Zadeh na cikin jerin sunayen Mutanen Iran, da suka shiga rukunin sunayen mutane 500 mafiya tasiri a duniya, kamar yadda Mujjallar Amurka mai suna "Foreign Policy" ta baiyana.
Allah ya karbi shahadar shi ya bashi dubban daruruwan magada a wannan sabga ta shi.