Daga Jafar Mustapha Sarina.
A ranar Asabar 7/11/2020 a wurin bikin murnar zagayowar ranar Haihuwar Shaikh Muhammad Mahmud Turi. Kwamatin da aka dorawa nauyin gabatar da taron duk shekara, suka kaddamar da Mu'assasar mai suna (Shaikh Turi Foundation). Duk domin cigaba da wasu aiyukan alkairi da Shaikh Muhammad Mahmud Turi. Ya ke gabatarwa a lokacin da yake tare da yan uwa.
Malam Uzairu Hussaini. kwamandan Harisawan Kano, shine ya kaddamar da Mu'assasar. Lokacin da yake kaddamar da Mu'assasar ya bayyana manufa da ayyukan da zasu gabatar. na tallafawa Iyalin Shahidai da kuma sauran al'umma gaba daya. Malam Uzairu Hussaini a cikin jawabin sa yake cewa "wannan mu'assa an samar da Ita ne domin dorawa da aikin da shaikh Turi. Yakeyi na tallafawa Iyalan shahidai da kuma ciyar dasu. Sannan a kasan wannan 'foundation' akwai (Shaikh Turi Relief foundation). Shikuma wannan bangaran zai dinga samarwa da al'umma, kayan Masarufi akan farashi mai sauki, sabanin yadda ake sayar da kayan masarufi a gari. Wannan tsarin an masa suna da cikar Burin Sheikh Turi" Malam Uzairu Hussaini ya kara da cewa "Wannan Ma'assa za ta dinga sayar da kaya kamar su Magani. da sauran kayan Masarufi a akan farshi mai sauki don Tallafawa Mutane. Kamar yadda Sheikh Turi yake tausayawa al'umma"
Malam Uzairu Hussaini. Bayan ya kammala jawabin sa, ya gabatar da Sakatare na mu'assasar Eng. Prof. Bala Abdullah. ya kara bayani sisai akan aikin, wannan Mu'assasar. Inda yake cewa " wannan kayan abincin da yan uwa suke gani wannan mu'assasa, ta tarashi ne domin rabawa Iyalan Shihuda. Wannan ba yana nufin Yan uwa za su daina bada Hakkin Shuhada'u bane. Ko daina biyan kudin tsarin ciyarwa na Iyalan Shahidai da ake dashi a Da'iran ce. Ita Wannan Mu'assasa za ta dinga dubawa ne gibin da aka samu a gidajen Shahidai tana bi tana cikewa, don haka aikinta tallafawa ne ba an daina bada Hakkin Shuhada bane, ko biyan tsarin ciyarwa. Wannan kuma kokari ne, na ganin an cikawa Sheikh Turi burinsa. na Tallafawa Iyalan Shahidai, kamar lokacin da yake waje, duk wani Gidan Shahidai da aka samu matsalar abinci, nan take Sheikh Turi yake dauka a abincin gidansa ya kaiwa Iyalan da kansa. Yana kuma ajiye wani abu a aljihunsa da yake tallafawa Iyalan Shahidai"
Prof ya kara da cewa "Assasar zata tallafa a Harka Ilimin Yan uwa, kamar yadda Sheikh Turi yake tallafawa yan uwa da ma wasu 'Ya'yan Mutanen Unguwar da yake zaune"
Alhaji Ibrahim Dangoshi Shine Chiyaman na mu'assasar, shima ya kara jawabi akan aiyukan mu'assasar. In da yake cewa" Wannan mu'assasar za ta fara aiki daga yanzu ne. Har zuwa kowanne lokaci Insha Allah" tun a wajan Alhaji Ibrahim Dangoshi yayi kira ga yan uwa masu San shiga wannan aikin alkairin suba da tasu gudunmawar. Take yan uwa suka dinga rige rigen zuba kudi, a yan mintuna aka tara kudi masu tarin yawa. Shima kuma Alhaji Ibrahim Dangoshi yayi alkawarin bada kudi masu yawa. Tun ranar wannan mu'assasar ta kawo taliya da shinkafa. Cikin mota yar kurkura ta rabawa Iyalan Shahidai.