An gabatar da Muzaharar Mauludi Annabin Rahama (S) Hadi Da FreeZakzaky a Sabon Garin Narabi, Yankin Jos


 

Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) sun fito kaman yadda suka saba fitowa don nuna Murna da Haihuwar Fiyayyen Halitta Muhammad (S), Bayan idar da Sallar Jumma'a Muzahar Mauludi Manzon Allah (Saww) ta daga A Sabon garin narabi dake yankin Jos. 


An dauka dogon zango ana tafiya Inda Yan Fudiyya da Harisawa tare da Yan Jaishi Amirul Muminin (As) suka taka faretin ban girma zuwa ga Shugaban Halitta Muhammad (S). 


Daga karshe bayan an iso inda za a kulle Muzahar Malam Idris Muhammad (Baba Idi) shine yayi jawabin kullewa bayan ya kammala Sai Sayyid Adam Jubulwa yayi Addu'a


Muzahar ta isar da sako zuwa inda ake da bukatan ya isa 

Muna fatan Allah ya maimaita mana. 


Daga Almustapha A Abdullahi


Ga wasu hotuna
















Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post