Allah Ba Ya Tufka Ba Tare Da Yayi Mata Hanci Ba !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MUBAYA'AR DAKE AMFANI ITA CE WACCE AKA 'DORE A KANTA 


Kamar yadda wani hadisi ke cewa za ka samu wani mutum na aikata kyawawan ayyuka wadanda da zai mutu a kansa zai shiga Aljannah, amma har sai ya kasance tsakaninsa da ita (Aljannah) bai wuce zira'i guda ba sai littafinsa ya rinjaye shi, sai ya aikata ayyukan 'yan wuta, sai ya shige ta, haka ma mai aikata munanan ayyuka........... 


Al'amarin mubaya'a ga jagora abu ne mai girman gaske wacce idan aka yi ta ba a warware ta komai rintsi, kuma ko da daga baya mutum ya zama wani a fahintarsa.


 A yayin da mutum yayi mubaya'a ga wanda Allah yace ayi masa mubaya'a , to, a wannan lokaci yana cikin yardar Allah, kuma ya sami shaida (stump) na imani. Saboda haka a daidai wannan lokaci yana cikin nasu da'a ga Allah. 


Allah ya yiwa wasu Sahabban Manzon Allah (S. A. W. W) shaida mai kyau a yayin da suka miqa mubaya'arsu gare shi (S. A. W. W). 


Allah (S. W. A) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


لَّقَدۡ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ يُبَايِعُونَكَ تَحۡتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَثَٰبَهُمۡ فَتۡحٗا قَرِيبٗا ٨١


" HAQIQA ALLAH YA YARDA DA MUMINAI A LOKACIN NAN DA SUKE YIN MUBAYA'AH GARE KA A QARQASHIN BISHIYA (saboda) YA SAN ABINDA KE CIKIN ZUCIYARSU, SAI YA SAUKAR DA NUTSUWA A KANSU , SAI WANI BUDE MAKUSANCI YAZO MUSU.


(SURATUL-FATHI :18)


Wannan ita ce tufka wacce Allah ya yi akan Sahabban da suka yi mubaya'a ga Annabi (S. A. W. W) a qarqashin wata BISHIYA. 


Saboda wannan shaida da akayi musu a tunanin mutane suke cewa ai sun sami Lasisin shiga Aljannah tun daga wannan lokaci, kenan sun zama abin koyi kuma madubi wajen kallo da kuma koyi da ayyukansu. 


Sai dai wani abu kuma wanda kan iya canza qwaqwalen mutane shine, hancin da ya yiwa wannan tufka tasa mai qarfi! 


Ya kafa wani sharadi wanda sai an kiyaye shi ne kawai wannan mubaya'ar za tayi amfani ga wanda yayi ta . Ga sharadin nan kamar haka, 


إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ ٱللَّهَ يَدُ ٱللَّهِ فَوۡقَ أَيۡدِيهِمۡۚ فَمَن نَّكَثَ فَإِنَّمَا يَنكُثُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِمَا عَٰهَدَ عَلَيۡهُ ٱللَّهَ فَسَيُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا ٠١


" LALLE WADANNAN DA KE YI MAKA MUBAYA'A ABIN SANI ALLAH SUKE YIWA MUBAYA'A (don Shi yayi umarni da suyi maka), YARDAR ALLAH NA BISA YARDAR SU. (Amma fa su sani cewa) WANDA YA WARWARE YA WARWAREWA KANSA NE, KUMA WANDA YA CIKA ABINDA YAYI ALQAWARINSA GA ALLAH , DA SANNU ZA AZO MASA DA WANI LADA MAI GIRMA !"


 (SURAATUL-FATHI :10)


Wannan ya zama babban ma'auni wanda za mu riqa don auna mubaya'ar da muke yiwa jagora Sayyid Zakzaky (H). 


Duk wanda ya miqa mubaya'arsa gare shi ya sami shaidar yabo daga Allah. Amma da zarar ayyukansa da zantukansa sun canza daga haqiqanin koyarwar jagora kuma ya zamana ya miqa Wilayarsa zuwa ga wani na dabam ko kuma ya fito da wata da'awa wacce kan iya wargaza ko alamta cewa gaban kansa yake yi, to, ya zama ya warware wancan bai'ar da yayi ta farko, kenan ya fice daga cikin wancan da'ira ta mabiya masu cikakkiyar wilaya. 


Ya zama tamkar yadda wasu magabata suka warware bai'arsu ga Manzon Allah (S. A. W. W) ta hanyar bijirewa umarninsa. 


Ya zama dole a kiyaye ko a tsare wannan martaba don mubaya'arka ta amfanar da kai a bayan ranka. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


            (08137925034)


26th November, 2020/ 11th Rabi'us-Sani, 1442

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post