@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AZZALUMAI BA ZA SU TABA SON JIN MURYAR SAYYID ZAKZAKY (H) BA
Alqawari ne na Allah (T) cewa zai jarrabi bayinsa a duniya ta hanyoyi daban-dabam cikin dukiyoyinsu, ko rayukansu ko amfanin gona ko kuma a gangar jikinsu.
Wannan dalili yasa yake mayar da wani makaho, kuturu, gurgu, kurma, babe ko kuma Mahaukaci, wani kuma ayi shi marar haihuwa (bakararre).
Cikin irin wadannan jarrabawowi yakan jarrabci kowa har ma Manzannisa (A. S) da bayinsa salihai, kamar yadda ya jarrabi Annabi Ayuba da Musa (A. S).
Annabi Musa (A. S) ya sami matsala kan harshensa har takai mutane ba sa iya fahintar maganarsa sosai, har ya roqi Allah da cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَٱحۡلُلۡ عُقۡدَةٗ مِّن لِّسَانِي ٧٢ يَفۡقَهُواْ قَوۡلِي ٨٢ وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي ٩٢ هَٰرُونَ أَخِي ٠٣ ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي ١٣ وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي ٢٣
" KUMA KA WARWARE QULLI DAGA HARSHENA. SU FAHINCI MAGANATA. KUMA KA SANYA MIN MATAIMAKI DAGA IYALINA. HARUNA 'DAN'UWANA. KA QARFAFI HALITTATA DA SHI . KUMA KA SHIGAR DA SHI A CIKIN AL'AMARINA (yadda zai zama mai bayyanarwa al'ummata saqon da nazo musu da shi don harshensa ya fi nawa fitar da magana dalla-dallah) ."
(SURATUL-'DAAHA:27-32)
A wani guri kuma yace;
" قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ ٢١ وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ ٣١ ."
" Yace, " YAA UBANGIJI INA JIN TSORON KADA SU QARYATA NI. KUMA QIRJINA YAYI QUNCI (saboda baqin cikin haka), KUMA HARSHENA BA ZAI SAKU (ta yadda zan iya yi musu bayani) BA, (saboda haka) KA AIKA ZUWA GA HARUNA (ya tafi a madadina) ."
(SHU'ARAH :12-13)
Kunga wannan jarrabawa ce wacce Allah ya jarrabe shi da ita, amma kuma yana nan cikin hankalinsa ba tare da gushewar hankali ba har ya koma ga mahalicinsa (S. W. A).
Shi kuma Annabi Ayuba (A. S) ta kai yadda har gabobin jikinsa na datsewa/guntulewa saboda cutar da Allah ya jarrabce shi da ita, har Allah ya umarci Annabi Muhammad (S. A. W. W) cewa ya bamu labarinsa.
" وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍ ١٤ ."
" KUMA KA AMBACI BAWANMU AYUBA (a gare su) A LOKACIN DA YA KIRAYI UBANGIJINSA, YACE, " LALLE NI SHADAN YA SHAFE NI DA WAHALA DA KUMA AZABA (ta cutarwa, ka kawo min sauqi). "
(SURATUL-SAAD:41)
A wani guri kuma yace,
۞وَأَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ ٣٨ فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَكَشَفۡنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرّٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰبِدِينَ ٤٨
" DA KUMA AYUBA A LOKACIN DA YA KIRAYI UBANGIJINSA, (yace), " LALLE NI CUTA TA SHAFE NI (kuma ta ci qarfina har kusan duk sassan jikina ya lalace kamar yadda ka sani kuma kake gani) ALHALI KAI NE MAFI RAHMAR MASU RAHMA. SAI MUKA KARBA MASA, MUKA KWARANYAR DA ABINDA KE GARE SHI NA CUTA, KUMA MUKA KAWO MASA IYALINSA (wadanda suka guje shi don ganin halin da yake ciki ta jarrabawa) DA MISALINSU TARE DA SU, RAHMA DAGA GURIN MU DA KUMA TUNATARWA GA MASU IBADA (su san cewa Allah na jarraba bawansa a hanyarSa, kuma yana da iko ya bashi duk abinda yake so) ."
(ANBIYA :83-84)
Duk da irin wannan jarrabawowi amma yana nan cikin hankalinsa yadda yake fahintar komai, kuma yayi bayani dalla-dallah kowa ya fahince shi.
Ku biyo mu cikin wannan hadisi dake tafe insha Allah,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الكافي مُحَمَّدُ بْنُ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنْ عُثْمَانَ النَّوَّاءِ عَمَّنْ ذَكَرَهُ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَنَّهُ قَالَ: إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَبْتَلِي الْمُؤْمِنَ بِكُلِّ بَلِيَّةٍ وَ يُمِيتُهُ بِكُلِّ مِيتَةٍ وَ لَا يَبْتَلِيهِ بِذَهَابِ عَقْلِهِ أَ مَا تَرَى أَيُّوبَ كَيْفَ سُلِّطَ إِبْلِيسُ عَلَى مَالِهِ وَ عَلَى وُلْدِهِ وَ عَلَى أَهْلِهِ وَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ مِنْهُ وَ لَمْ يُسَلَّطْ عَلَى عَقْلِهِ تُرِكَ لَهُ لِيُوَحِّدَ اللَّهَ بِهِ.
Cikin Usulul-Kafiy, daga Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad, daga Muhammad Bn Sinaan, daga Usmana An-Nawwa'i, daga wanda ya ambata masa daga Abu Abdullahi (A. S) cewa yace:
" LALLE ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YAKAN JARRABI MUMINAI DA KOWACCE IRIN JARRABAWA, KUMA YA KASHE SHI DA KOWACCE IRIN MUTUWA (jinya, ruwa, gobara ko kuma wani ya kashe shi), AMMA BA YA JARRABTARSA DA GUSHEWAR HANKALI. BA KWA GANIN AYUBA NE YADDA SHAIDAN YA SALLADU AKAN DUKIYARSA DA 'YA'YANSA DA IYALINSA (matansa) DAMA DUKKAN WANI ABU DAKE GARE SHI, AMMA BAI SALLADU (samu iko) KAN HANKALINSA BA, YA BAR MASA DON YA SAMI DAMAR KADAITA ALLAH DA SHI ."
Sayyid Zakzaky (H) ma ya sami irin wannan jarrabawa daga Allah yadda ya rasa 'ya'yansa da wasu danginsa. Har jinin jikinsa sai da ya tsiyanye kuma ya rasa ido daya (1) amma idan yana magana ba za ka taba tsammanin wata cuta ta taba shafarsa ba, kuma muryarsa azzalumai ke tsoron ji, saboda haka ba za su taba son jin muryarsa ba.
A qarshe muna kammala wannan rubutu namu da ayar nan dake cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ ١٥ ."
" LALLE MU MUNA TAIMAKON MANZANNINMU DA WADANDA SUKA YI IMANI A RAYUWAR DUNIYA DA KUMA RANAR DA MASU SHAIDA KE TSAYAWA ."
(SURATIL-GHAFIR:51)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
22nd November, 2020/ 7th Rabi'us-Sani, 1442.