Akwai Gyara Cikin Harkar Maulidin Manzon Allah (SAWW)..!!!

Irin shigar da Akeso Kowace Macce Tayi a Zagayen Maulidin Nabeey (s)

Irin Shigar da akeson kowace Macce tayi a bikin Maulidi
 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SON ANNABI SHINE YIN KOYI DASHI 


Duk da cewa an riqa cin karo da irin wadannan kwama-calar hukunci a zamanin baya amma hakan bai canza haqiqanin hukuncin abubuwan ba. 


A shari'ar muslimci ba a qirga sakin aure a cikin lissafi har sai sakin da akayi shi bayan tsarki. Da ace mutum zai yiwa matarsa saki uku (3) cikin tsarki 1, to, wannan saki yana Matsayin saki daya (1) ne ba uku ba, amma sai wani yace duk wanda yayi saki uku a lokaci guda yana matsayin uku (a tasa fatawar) tunda dai sun maida al'amarin saki a matsayin abin wasa, ba zasu komawa junansu ba har sai tayi wani aure tare da sabon miji. 


To, irin wannan hukunci ne wasu ke yiwa harkar maulidi a wannan zamani. 


Al'amarin Maulidin Manzon Allah (S. A. W. W) yafi qarfin a kira shi halas, idan an taqaita a kira shi sunnah, amma bisa haqiqaninsa aiki ne wajibi kan dukkan muminai tunda Allah ya tilasta dukkan wata halitta tasa ta nuna farin cikinta na samuwar Manzon Allah (S. A. W. W) ta hanyar da Allah ya nufe ta da shi. Misali :-


Aljanu, Dabbobi, Duwatsu, Wuta, dama wasu daga cikin manyan Kafiran Makkah a ranar da aka haife shi (S. A. W. W). 


Sai dai wani abin takaici shine yadda ake aikata ko shigar da haram cikin harkar Maulidi, musamman yayin da ake yin zagayen ranar 12 ko 19 ga watan. 


Irin shiga da fitar da 'yammata ke yi kwata-kwata ya sabawa koyarwar muslimci. Za kaga budurwa wacce ta fi wata matar aure a duk wata siffa da mace, amma ta fitar da duk wata siffar halittarta babu Hisabi tana tiqar rawa kan titi da sunan wai hakan soyayyar Manzon Allah (S. A. W. W) ce, kuma malumansu na ganin hakan duk addini ne. 


Ba fitar mace ne haramun ba, amma dole ta kasance cikin Hisabi kuma cikin siffa wacce Annabi (S. A. W. W) ya koyar da matansa da 'ya'yansa da kuma dukkan matan muminai. 


Allah (T) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ يُدۡنِينَ عَلَيۡهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يُعۡرَفۡنَ فَلَا يُؤۡذَيۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا "٩٥


" YAA KAI ANNABI ! KA FADAWA MATANKA DA 'YA'YANKA (mata) DA KUMA MATAN MUMINAI (cewa) SU KUSANTAR DA QASA DAGA TUFAFINSU (yayin da za su fita ko suka fita waje) . HAKAN SHI YAFI KUSA AN GANE SU (cewa su matan kirki ne) BA ZA A CUTAR DASU (ta hanyar furuci ko kallon banza ba), KUMA ALLAH YA KASANCE MAI GAFARA NE (kan abinda suka aikata a baya cikin rashin sani) MAI JIN QAI (ga wanda yabi dokarsa) ."


               (AHZAB :59)


Sannan kuma yazo cikin hadisi kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وأخرج أبو داود وابن مردويه والبيهقي عن عائشة: أن أسماء بنت أبي بكر دخلت على النبي صلى الله عليه وسلم وعليها ثياب رقاق، فأعرض عنها وقال: «يا أسماء إن المرأة إذا بلغت المحيض لم يصلح أن يُرى منها إلا هذا، وأشار إلى وجهه وكفه».


Abu Dawud da Ibn Mardawihi da Baihaqi sun fitar daga A'isha cewa : Lalle Asma'u Bnt Abubakar ta shiga ga Manzon Allah (S. A. W. W) kuma a kanta akwai tufafi shara-shara (very light) , sai ya kawar da kansa daga gare ta wannan yace, 


" YAA ASMA'U ! LALLE ITA MACE IDAN TAKAI MATAKIN YIN HAIDHA (al'ada) BAI KYAUTATU AGA (wani abu) DAGA GARE TA BA SAI DAI WANNAN ." Yayi nuni zuwa ga fuskarsa da kuma tafukansa (na hannu). 



    RIWAYAR ABU DAWUD 

 وأخرج أبو داود في مراسيله عن قتادة أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إن الجارية إذا حاضت لم يصلح أن يرى منها إلا وجهها ويداها إلى المفصل» والله أعلم.


Abu Dawud ya fitar cikin (hadisansa) mursalai zuwa ga Qatadata , daga Annabi (S.A.W.W) yace, 


" LALLE ITA KUYANGA IDAN TAYI HAIDHA BAI KYAUTATU A GANI DAGA GARE TA BA SAI DAI FUSKARTA DA HANNAYENTA SUWA MARABA (mufassal) ."


Yanzu mafi yawan yara matan da ake fita dasu zagayen Maulidi sun kai wannan matsayi amma wasu babu hisabi a jikinsu sai dai Atamfa da Shaddodi dauke da kwalliya jikinsu ko kuma an sanya kaya shara-shara ana gwangwajewa akan titi. 


Lalle wannan ba soyayyar Ma'aiki (S. A. W. W) bace, domin an saba koyarwarsa. Soyayyarsa ita ce yin koyi dashi cikin komai namu. 


Amma matuqar za mu saba koyarwarsa cikin ayyukanmu ba za mu taba samun wani lada kan hakan ba sai dai tarin zunubi. 


Munin abin yafi akan malaman wadannan yara 'yan Islamiyyu, domin su suke karantar dasu hakan a aikace. Su suke fitar musu irin dinkin da za suyi, kuma a gabansu ake aikata irin wannan munanan ayyuka amma basa hanawa. 


Saboda haka yin gyara ya zama wajibi, amma mu sani cewa aikata haram cikin halas ba zai canza halas ta koma haram ba komai munin abinda ake aikatawa, sai dai kawai a gyara zuwa aikata abinda ya dace. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


08126385470-08137925034


15th November, 2020/ 28th Rabi'ul-Awwal 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post