ALLAH MUN GODE DA NI'IMAR SU MALAM GAREMU.
Wani aiki ya kai ni Kazaure na hqdu da yan uwa mu na hira kan Malam (h) da jahiliyya da irin kallon da su ke masa. To shi ne muka gangaro ga cewa ai ko kusa su Malam ba ordinary mutane ba ne.
Wannan sai ya kai mu ga tattauna wasu karamomi da mu ka iya sani kan Malam (h). To wani Dan uwa da yake buga ma Shahid Alh. Shafi u Kazaure mandir I sai ya kawo wani labari da ya dau hankalina sosai ya kuma matukar burge ni da sa ni yi ma Allah godiya, kuma ga shi ku ji.
A shekarar da su Malam su ka kaddamar da gidauniya don neman infaki shi wannan dan uwa a tawagar Alh. Shafi'u sun je Gombe to bayan kare programme sai su ka kama hira da Amir din Gombe na wancan lokacin Mal. Muhd Wanzam sai yake ba su wannan labarin.
Ya ce akwai wani Ba'ame dan giya da shan kwayoyi kusan kullum sai ya wuce ta kofar Markaz (ta da) a bugensa don nan ne kamar hanyar da ya fi bi. To kuma kullum din in dai ya ga Mal. Muhd sai ya gaishe shi ya ce masa Malam yaushe za mu je Zariya na gaida Malam (h)? Sai shi kuma Mal. Muhd ya ce masa insha Allah, kusan ko da yaushe haka ya ke fadi. Bisa dabi'a yawanci haka za a yi, domin mutum dan kwaya kullum cikin maye ai haka za a masa.
To ana nan sai da'irar Gombe su ka kai ma Malam (h) ziyara, cikin maganganun Malam sai ya zo wata gaba sai ya ke cewa.... Ta yiyu ka ga wani na son zuwa wajanmu amma kuma ba mutumin kirki ba, wala'Allah ma mashayi ko dan giya, to ba naka ba ne ka kange shi zuwa gare mu ba, naka shi ne ka masa iso.... (ba lallai hakan ya zama kalaman su Malam ba kwabo da kwano).
Ai sai Mal. Muhd ya ji wannan kam kai tsaye da shi ake, nan ya kagara a gama ziyara su dawo. To kuwa suna dawowa washe gari ya zauna jiran wannan bawan Allah mashayi. Can kuwa sai ga shi ya zo wucewa su ka gaisa kamar yadda su ka saba, mashayi ya kara fadin abin da ya saba na cewa Malam yaushe za a kai ni na gaida Malam? Take Mal. Muhd ya ce masa gobe! Mashayi ya sha mamaki, ya ce gobe goben nan Malam? Mal. Muhd ya ce kwarai. Ya ce to ka ce na je na kimtsa na sa kayana na musamman, lallai gobe zan kure adakata, zan ci kwalliyar zuwa gaida Malam. Ai kuwa ana asuba zan zo nan kofar gidanka, Mal. Muhd ya ce to ina jiranka.
Ai kuwa Mal. Muhd ya ce washe garin da sassafe sai ga shi ya yo shigarsa mai kyau kuma dai ba warin giya ba kuma alamun afa kwaya, a haka ya dauke shi sai Zariya.
Bayan sun isa gidan Malam (h) sai aka yi arashi ranar ana iftar. Wani karin abin mamaki shi ne Malam (h) na ganin Mal. Wanzam sai ya ce masa ina bakona? Wuf ya ce Akramakalla ga shi. Su Malam su ka ce to Masha Allah.
Sai Malam ya zuba shayi a kofinsa har ya kurba sau daya sai ya ce af ai kuwa bakona ma ya kamata na fara ba, sai Malam (h) ya mika ma wannan bawan Allah da aka zo da shi wannan shayi shi kuma ya sake zuba wani.
Mal. Muhd ya ce wallahi tun daga wannan ziyara mutumin nan bai kara shan komai ba, kawai sai gani aka yi ya koma salihi karshe ma dai ya zama dan uwa. Har ma shi Mal. Muhd ya ke ce ma su Alh. Shafi'u da kun lura da wani mai bulun shadda da ya zo ya rika lika wazobiya ana waje to shi ne. Ya ce wallahi ta sanadinsa mutane da dama sun kara fahimtar harka. Da dama sai su ka rika cewa ai tun da na kai shi Zakzaky ya ba shi rubutu shike nan ya shiriya. Ya ce wasu kuwa har gida suke biyo shi wai da Allah a san musu rubutun nan na Malam saboda yayansu. Ya ce to duka dai na kan ce ba wani rubutu da Malam (h) ya ba shi, shayi kawai na san Malam ya ba shi shi ma irin wanda aka saba sha ne duk ranakun azumi na Alhamis da Litinin.
Wannan labari ya sa ni kara gode ma Allah(T) da wannan ni'ima da ya yi mana ta zama ma biyan Malam (h).