A 2015 Saudiyya Ta Qaddamar Da Yaqi A Yemen, Har Zuwa Yau Tana Kashe Mutane, A 2015 Din Ne Gwamnatin Buhari Ta Qaddamar Da Harinta Ta Kashe Mutane Sama Da 1000, Duk Don Son Sai An Kashe Sheikh Zakzaky Bisa Umurnin Saudiyya, America Da Israel !!!


Ma'asumah Nigerian News Update


 *Tare da Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) 070-32803940 Azare*


 Kowa yasan cewa Saudiyya ce ta qaqabawa Yemen yaqi take yaqarta, tun 2015 take ta kashe mutane ta hanyar munanan Hari da take kaiwa qasar, zuwa yau Allah ne kadai yasan adadin mutanen da Qasar Saudiyya ta kashe, a Yemen!

 Wannan wane irin zalunci ne?


 Haka zalika kowa yasan cewa a 2015 ne Sojoji suka farwa 'yan Shi'a mabiya Shehin Malaminnan Sheak Zakzaky da kisa da nufin son kashe, shi Malamin, bisa Umarnin Buhari da qaryar an tarewa shugabansu hanya. Gwamnatin Buhari ta qaddamar da wannan harin ne shima bisa Umarnin Saudiyya, da Amirka da Isra'ila, wannan Yariman Saudiyya ya fito ya gayawa duniya cewa sune suka sa, ayi wannan kisan a wata hira da yayi! Wannan duniya taji ta kuma shina!!!


 *KUMA HAR ZUWA YAU SUNA CIGABA DA KISA, TARE DA SON KASHE SHI, SHEHIN MALAMIN SUNA TSARE DA SHI BAYAN HARBINSA DA SUKA YI DA HARSASAI MASU GUBA, SUNA JIKINSA HAR ZUWA YAU DINNAN BA A CIRE MASA SU BA, SUNA FAMA DA JINYA SHIDA MATARSA BABU MAGANI.*

*YAU SHEKARA BIYAR KE NAN, DUDA UMARNI KOTU NA A SAKE SHI A KUMA BIYASHI DIYYAR BARNAR DA AKA YI MASA, A KUMA GINA MASA GIDA DUK INDA YAKE SO A FADIN QASARNAN* Amman sun qi, wannan wane irin zalunci ne?


 Amirka da Isra'ila suna ingiza Saudiyya tana kashe Musulmai. Don sabanin fahimta na Addini.


 Shin miye hukunci wanda ya kashe Musulmi da ya yi kalmar Shahada?


 *DA DARASI MAI KYAU CIN WANNAN HADISIN*👇


 Mu tuna fa cewa "Wata rana Manzon Allah ya tura yaqi, sai ya zamana da akaje yaqin wani daga cikin Sahabbai ya kashe wani, wanda kafin ya kashe shi ya nufo shi zai kashe shi kenan sai mutumin ya yi kalmar Shahada! 

Amman duda ya yi kalmar Shahadar nan sai da Sahabinnan ya kashe shi!


 Da Sahabbai suka dawo suka labartawa Manzon Allah cewa wane ya kashe wani a filin yaqi duda cewa ya yi kalmar Shahada! 


 Manzon Allah fuskarsa ta canza ransa ya baci, yace ka kashe shi? duda ya yi kalmar Shahada!


 Sahabinnan ya amsa da cewa ai ya yi tane don tsoron kada a kashe shi!


 Manzon Allah yace masa shin ka shiga zuciyarsa ne ka gani? Sahabin yace a'a!


Manzon Allah Yace masa toh! Ya za kayi da Kalmar Shahadar sa a ranar gobe qiyama, idan tazo nema masa hakkinsa?"


 Kunga kenan kashe Musulmai da Saudiyya take yi ba koyarwar Musulunci bane ba! Ba koyarwar Manzon Allah bane ba, bai dace da sunna ba!!!


 Komi ya fito fili ga mai hankali cewa Saudiyya a Amirka da Isra'ila takewa aiki su take bi, ta shiga rigar Musulunci ne amman ba Musulunci take bi ba!


 Saudiyya ce ta bude Gidan ca-ca da Gidan Rawa! ya isheka ka gane cewa, Saudiyya ba Musulunci take ba.


 Insha Allah Saudiyya da Qawayenta Amirka da Isra'ila baza suci Nasarar Tarwatsa Musulunci ba.

 

 Abinda bakwaso kuji, insha Allah Musulunci shi zai yi iko da Duniya!!!


 Amirka da Isra'ila suna amfani da Saudiyya suna cutar da Musulunci da Musulmai, suna raba kayin Musulmai da sunan ban-bancin fahimta suna kashe Musulmai da shiga rigar Musulunci!!!


 Insha Allah qarshenku yazo!!! Wa 'yanda kuke kashewa sune da Nasara! Don basu da gata sai Allah!!

 Allah kuma ya isar musu!!!


 Zan rufe da wannan don mai hankali ya qara gane Saudiyya da kyau.

 Allah yace:- *"Lan tarda ankal Yahudu wanlan Nasara Hatta Tattabi'a Millatahum" Fassara:- "Yahudu da Nasara baza su taba yadda da kai ba (Musulmi) har sai kabi su"*


  Mu lura yanzu za muga cewa Amirka da Isra'ila sun yadda da Saudiyya har sun riqeta qawa suna hulda tare, Wanda duniya tasan qawancensu, sabida Saudiyya ta bisu ta saki Musulunci!  


 Suna amfani da ita suna cutar da Musulunci, suna shinan Sirrin Musulmai, suna bata koyarawar Musulunci sai irin nasu Musulunci da suke so ayi!

 Amirka da Isra'ila suna amfani da Saudiyya suna haifar da 'yan ta'adda da sunan Musulunci, suna gurbata tunanin Musulmai. Da sauran muggan abubuwa da tanadi da suka yiwa Musulunci da Musulmai!!!


 Amman ta Allah ba tasu ba!


 Da sannu Musulmai za su gane makircinku garesu da kuma Musulunci.


 Kun hana Buhari ya saki Sayyid Zakzaky kun sakashi ya yi masa wannan zaluncin, zalunci mai tsanani!!! Allah ne gatan sa!

 

 Kamar yadda Allah ya tasar dashi bayan kashe shi da kuka yi! Shine mai fito dashi koda bakwa so!!!


Ku ziyarce mu a www.maasumah.com.ng

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post