Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu.
Yau ma kamar kullum Yar uwarku che Mae rauni.
Khadija lawan daura ne✍️
Zanyi tsokachi akanmu,(Yan uwa) ko nache Zan bamu shawara ne a takaiche.
A gaskiya yakamata musan chewa muna chikin wani yanayi ne Wanda ya kamata mu mayar da ayyukanmu muna yinsu ne domin Allah da ikhlasi ( taqawa).
Tabbas duk wani aeki da zakayi muddin Dan wani kake yinsa Tofa akwae qalubale akan makomar aikin Nan naka .
Babban abunma shine idan kanada maqiyi karka shagaltu da bibiyar batanchin da yake maka
saboda shi maqiyi ala kulli hanin Yana Neman hanyar chi bayan kane ba hanyar chi gabanka ba,Kae Kuma da kake addini Koma ba'a bangaren addini ba a bangaren rayuwanka ma biyewa zantukan mutane da tsayawa maeda martani zae hanaka gudanar da wasu
ayyukan Wanda suma zae iya yiyuwa masu muhimmanchi ne.
Babu abunda yake da zafi irin shi maqiyi din yaga yayi Abu ka share idan na jini tofa yaga kamarma ba ka jiba idan Kuma na kallo ne ka nunawa wannan maqiyi chewa Kae fa baka ma kalla ba .
Wannan wani sirrine na wulakanta maqiyi ta hanyar daya kamata.
Muzama masu miqa kukanmu ga Allah ta'ala mu zama masu nema a wurin Allah,
Sannan duk Wanda yayi Mana ba dai-dai ba to mu miqa qaransa gurin Allah ta'ala kamar yanda maulana sayyid zakxaky ya koyar damu.
Allah ka shige mana gaba, ka futo Mana dasu hasken idanunmu, sayyid zakxaky da ummush-shuhada.
Kura-kuren danayi achiki Allah ta'ala ya yafemin Kuma wanda nayi Ina neman afuwarku.
Wasallahu Ala Muhammad wa Ali Muhammad