Ma'asumah nigeria news update.
Ummu Radiyya ce...✍🏻
Amfani da man kwakwa da man amla: Da farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man amla, sannan ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sai ki zuba man a kwalba ko wani mazubin da bazai zube ba. Kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati, zakisha mamaki.
Amfani da lemon tsami: Ki samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti talatin, sannan ki wanke da ruwan dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau biyu a wata.
Amfani da aloe vera: Ki samu ruwan Aloe bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti ashirin sai ki wanke da ruwan dumi.
Amfani da man zaitun: Man zaitun na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.
Ku kasance damu a shafin mu na www.ma'asumah.ng.com