Zanga–Zangar Rushe SARS Ya Isa Mai Hankali Ya Gane Gaskiya.


Ma'asumah Nigeria News Update tare da Shana Islam.


Wani Abunda Al'ummar kasar nan ya dace su fahimta, konace su gane idan can baya basu gano ba, duk da ina da tabbacin wasu sun dade da ganewa kawai dai bushewar Zuciyace yasa sukayi shiru da bakunan su.


A'bunda nace Al'Umma ya dace su gane shi ne, yanada kyau Ko nace yazama dole a wannan lokacin al'ummar kasar nan su gane cewa Lallai Malam Zakzaky (H) da Al'majiransa ba "Yan tashin hankali bane zaman lafiya suke son kasar nan da Shi.


Mai karatu idan baka manta ba wannan malamin Malam Zakzaky shi ne wanda Sojojin Nigeria suka kashewa Al'amajirai sama da Dubu daya a ciki harda "ya yan sa Uku a Shekarar 2015 a Zaria, suka halbe shi da matarsa bayan hakan suka Kama shi,


Tun bayan Kama shi da Gwamantin Nigeria tayi Al'amajiran sa ke Fitowa zanga zangar lumana a duk garutuwan dake cikin Fadin kasarnan ba dare ba Rana, Yau Shekara Biyar kenan suna zanga zangar lumana a cikin kasar nan domin Kiran Asaki malamin amma Gwamnati tayi shiru.


Tou wani a'bun dubi shi ne duk shekarun da Al'amajiran na Malam Zakzkay (H) sukayi suna wannan zanga zangar basu taba zuwa shagon wani ko gidan wani da sunan yimasa barna ba, basu taba tare jami'an tsaro da sunan ayi tashin hankali ba, sai dai ita gwamnatin ta tura jami'an tsaro su Affka masu a lokacin da suke gudanar da zanga zangar har su kashe masu mutane kuma basu tabajin zasu ramaba.


Amma sai ga shi kasar nan ta shiga cikin wani halin Kone Konen Motoci da rusa shagona sakamakon zanga zangar Rushe SARS masu zanga zanga suna kone ofsoshin "Yan sanda da motocin Al'Umma da Rushe shagonan masana'antun Al'Umma saboda kawai a karbi korafin su, Abunda masu Muzaharar Free Zakzkay basu taba yiba duk da tsawon lokacin da suka dauka sunayi na tsawon Shekanru 5 Amma ga shi masu zanga zangar Rushe SARS ko wata basuyi da farawa ba har sun fara tayar da hankalin "Yan kasa da ita kashinkan ta kasar.


Wannan ya ishi mai hankal gane cewa lalali Malam Zakzkay da Al'majiransa Sune cikankun masu son zaman lafiya a kasar nan  kawai a saki malamin zaman lafiya a Nigeria aga zaman lafiya tsantsa Amma batukar Ana tsare da malam Zakzaky wallahi hankalin kasa baima Fara tashi ba zai dai tashi.


Gwamantin Nigeria Free Sheikh Zakzkay ba tare da want sharadi ba.


@Shana islam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post